Saukar Wahayi



Wahayi

Wahayi a ma’anarsa ta isdilahi yana nufin abin da ake yi wa annabawa da manzanni sakonsa na daga zance ko ilhami da ake kimsa musu (A.S). Kuma shi hanya ce da Allah yake sanar da mutum ubangijinsa da kansa da shiriyarsa domin ya tsara rayuwarsa da zamantakewarsa da sauran halittu, da kuma yadda zai fuskanci ubangijinsa.

Nau’o’inwahayi

1.Ta hanyar sauti da annabi yakan ji

2.Ta hanyar mala’ika da yake jiyar da shi

3.Ta hanyar jefawa ga annabi a cikin ransa

4.Ta hanyar mafarki

Wahayi GaManzon Rahama (S.A.W)

Allah madaukaki ya shirya annabinsa kuma ya tarbiyyantar da shi da tarbiyya mai kyau, ba domin komai ba sai domin saninsa da nauyin da zai dora masa na shiryar da dan Adam da tseratar da shi zuwa ga tafarki madaidaici, ya kasance farkon nau’in wahayin da ya fara ga manzon rahama shi ne ta hanyar mafarki na gari[1].

Daga cikin hanyoyin tarbiyyantarwa ga annabi da ubangijinsa ya shirya masa sun hada da;

a.Ilhama damafarkin gaske da yake nuna masa zahirin abin da yake faruwa a gaske

b.Soyantarmasa da halwa da kebewa domin ya yi nazari cikin samuwar ubangiji da duniyoyin da ya samar da kuma fuskanta zuwa ga Allah madaukaki

SaukarWahayi

A shekara ta 610 miladiyya ne Allah madaukaki ya saukar da wahayi ga manzo a watan Ramadan mai girma ya saukar masa da farkon surar alak.



1 2 next