Kira A Boye



Sai mutanen suka rika dariya, suna cewa da Abu Talib: ya umarce ka ka ji daga danka ka bi. Sai Abu Talib (A.S) ya ce: Wallahi zamu taimaka masa, sannan zamu karfafe shi, ya dan dan’uwana idan kana son ka yi kira zuwa ga ubangijinka ka sanar da mu domin mu fito tare da kai da makamanmuâ€‌[2].

Bayan wannan ne labari ya yadu tsakanin kuraishawa da cewa Muhammad yana da’awar ana yi masa magana daga sama, sai wasu suka fara isgili, wasu suka fara tuhuma, sai Allah ya umarce shi da ya bayyanar da kira ga dukkan mutane da fadinsa: “Ka cigaba da abin da aka umarce ka, ka kawar da kai daga mushrikai, mu mun isar maka masu isgiliâ€‌. Duba zuwa ga wannan aya, ina ganin zamu iya kiran wannan marhala a matsayin ta uku a kiran manzo (S.A.W), wato muna iya jera su kamar haka:

A.Marhalar boyewa

B.Marhalar bayyanarwa ga dangi

C.Marhalar bayyanarwa ga mutane

 

Marubuci: Hafiz Muhammad Sa'id

www.hikima.org

hfazah@yahoo.com


[1] Siratul musdapha: 1/158.

[2] - Mausu’atut Tarih: 1/405. Mausu’atul mustapha wal itra: 1/108.



back 1 2