Kira A Boye



Kira a Boye

 Yana daga hikimar da kiran Manzon rahama ya doru a kanta ita ce; kawo canji a duniya gaba daya domin gyara â€کyan’adamtaka da tseratar da mutane daga zalunci, da kafirci, da barna, kuma da dogaro da darasin da kiran manzo ya dauka na tarihin abin da ya faru a tarihin annabawa (A.S) da suka gabata ta yadda kafirai suka yi wa da’awarsu kwaf daya tun kafin ta je ko’ina. Sai manzon tsira ya fara kiransa a boye[1]; farkon wanda ya yi imani da shi su ne imam Ali (A.S) da sayyida Khadiza (A.S), sannan sai Zaid Dan Harisa.

 Bayan kammalar wannan al’amari na fara kiran mutanen gidansa, sai kuma ya kira danginsa da sauran na kusa da shi da abokansa wadanda yake da aminci da su, wannan hanyar ta kira a boye da kuma dauki daidai ta taimaka wajan kafa mutane na farko masu dauke da tunani irin na kiran manzo (S.A.W) da suka dauki nauyin kare kiran da kuma yada shi, kamar yaddda karancinsu da imaninsu suka taimaka wajan tarbiyyantar da su domin tunkarar irin wannan aiki mai wahala.

 Sun kasance suna boye imaninsu suna ibada a boye, ba sa bayyanar da musuluncinsu, kuma wannan marhala ta boye kiran ta dauki tsawon shekaru uku, wanda a cikinta aka tarbiyyantar da mutane masu yawa a makarantar farko ta musulunci wato gidan Arkam Almahzumi, masu tarihin suna cewa; a wannan marhala adadin musulmi ya kai arba’in.

 

Kiran Danginsa a Bayyane

Bayan shekaru uku sun gabata, sai kiran manzo (S.A.W) ya shiga sabon fagen kiran na fili da bayyanarwa, a wannan marhalar ya fara da makusantansa ne na jini, hikimar da hakan ta kunsa ita ce;

Kadaa ce; don me bai kira makusantansa ba idan ya kansance kiran nasa alheri ne.

Bukatarkariya domin samun karfin yada da’awarsa.

Sai manzo (S.A.W) ya sanya imam Ali (A.S) da ya yi abinci ya kira dukkan makusantansa na Bani Hashim wadanda yawansu ya kai mutun arba’in da daya ko ba daya, sai suka ci abincin suka sha abin shan da yake na mutum daya ne, amma ya ishe su su duka gaba daya, amma kafin manzo (S.A.W) ya yi magana sai Abu lahab ya nuna cewa wannan ciyarwar sihiri ce, sai manzo (S.A.W) ya ki yin magana, kuma ya sanya imam Ali ya sake shirya musu wani abincin a rana ta gaba, bayan sun ci sun sha sai ya ce musu: “Ya Bani Abdulmudallib ni mai gargadi ne a gareku daga Allah (S.W.T) ni na zo muku da abin da wani daga larabawa bai zo da shi ba, idan kuka bi ne zaku shiriya ku rabauta ku tsira, wannan liyafa Allah ne ya umarce ni da ita; sai na yi muku ita kamar yadda isa dan Maryam (A.S) ya yi wa mutanensa;; wanda ya kafirce daga cikinku bayan wannan to Allah zai azabtar da shi azaba mai tsanani da bai azabtar da wani daga talikai da irinta ba, ku ji tsoron Allah ku ji abin da nake gaya muku, ku sani ya Bani Abdulmudallib: Allah bai aiko wani manzo ba sai ya sanya dan’uwa da yake waziri kuma wasiyyi kuma mai gado garshi daga ahlinsa, hakika ni ma ya sanya mini waziri kamar yadda ya sanya wa annabawan da suka gabace ni, kuma Allah ya aiko ni zuwa ga mutane gaba daya, ya saukar mini da ((Ka gargadi danginka makusanta)) da jama’arka masu tsarkake zuciya, kuma Allah ya ba ni labarinsa, kuma ya gaya mini sunansa, amma ni ina kiranku, ina kuma yi muku nasiha, ina bujuro muku; domin kada ku samu hujja bayan wannan, ku makusantana ne kuma jama’ata ta kusa, wanene daga cikinku zai yi rigo zuwa ga wannan a kan cewa ya zama dan’uwana a al’amarin ubangiji, kuma ya taimaka mini a kan wannan al’amari a kan ya kasance dan’uwana, wasiyyina kuma halifana a bayana a cikinku. Sai mutanen suka tage (jugum) gaba dayansu, sai Ali (A.S) ya ce: Ni ne ya annabin Allah zan kasance mai taimakonka a kansa. Imam Ali (A.S) yana cewa: Sai ya rike kafadata, sannan sai ya ce: Hakika wannan dan’uwana ne, wasiyyina kuma halifana a cikinku ku ji daga gareshi kuma ku bi.



1 2 next