Daurewa Rayuwar Tare



An ruwaito wani hadisi daga Abil Hasan Imam Musa al-Kazim (a.s) inda yake cewa: “Kada jin nauyi ya gushe tsakaninka da dan’uwanka; ka bar wani abu daga cikinsa, saboda gushewarta gushewar kunya ne[13]”.

Kamar yadda aka ruwaito daga Ibn Abbas, da kuma Imam Ridha (a.s) dangane da tafsirin fadin Allah Ta’ala ﴾ وَتَأْتُونَفِي نَادِيكُمُ الْمُنكَر ﴿ suna cewa sun kasance suna zama a wajajen zamansu ba tare da jin nauyi da kunya ba[14].

Kamar yadda kuma aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s) dangane da batun sakin jiki cikin yarda yana cewa: “Ka da ka yarda da dan’uwanka dukkan yarda, saboda ba a iya fadin yanayin sakin jiki[15]”.

Daga Amirul Muminina (a.s) yana cewa: “Ka so masoyinka cikin sauki, saboda mai yiyuwa ne wata rana ya zamanto makiyinki, ka ki makiyinka cikin sauki, saboda mai yiyuwa ne wata rana ya zamanto masoyinka[16]”.

A baya mun ga iyakoki da siffofin da ake bukata a wajen aboki da na kurkusa wadanda suke ma’auni wajen yarda[17].

d)– Kin Gardama da Husuma

Daga cikin wadannan abubuwa har da rashin mika kai ga shu’urin samun galaba ta ruhi yayin magana da tattaunawa, ta yadda hakan zai iya kai wa ga rikici da husuma, hakika shari’a ta yi hani da hakan.

An ruwaito Imam Sadik (a.s) cikin wani hadisi yana cewa: “Amirul Muminina (a.s) yana cewa: Ina gardadinku da gardama da husuma, saboda dukkansu biyu sukan haifar da rashin jituwa tsakanin ‘yan’uwa, da tsirar da munafuci[18]”.

e)– Kiyaye Harshe da Shiru Sai Dai Cikin Alheri

Daga cikin hakan har da rashin mika kai ga son zuciya cikin magana, da wajibcin kiyaye duk abin da zai fito daga bakin mutum da kula da hakan dukkan kulawa. Allah Madaukakin Sarki da Ahlulbaiti (a.s) sun yi gargadi da yawan gaske kan hakan, saboda masaniyyar da suke da shi na irin wannan shu’uri da ke cikin zuciyar mutum, da kuma irin gagarumar cutarwar da za a iya samu sakamakon tuntuben harshe, musamman a bangaren alaka ta zamantakewa. Akwai abin koyi cikin abin da aka ruwaito na hikima daga (Annabi) Lukman al-Hakim. Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Lukman ya ce wa dansa: Ya kai dana! Idan har kana zaton cewa kalami daga azurfa yake, to shiru kuwa daga zinare yake[19]”.

An ruwaito Abil Hasan al-Ridha (a.s) cikin wani hadisi yana cewa: “Daga cikin alamun masaniya (har da) ilmi, hakuri da shiru: shiru kofa ce daga kofofin hikima, shiru ya kan janyo kauna, shi dalili (alama) ne na dukkan alheri[20]”.

Abu Abdullah (a.s) yana cewa: “Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce wa wani mutumi da ya zo wajensa cewa: ashe ba zan sanar da kai wani abu ba wanda da shi Allah Zai shigar da kai Aljanna? Sai ya ce: Na’am Ya Manzon Allah, sai ya ce: Ka ba da abin da Allah Ya ba ka. Sai ya ce: idan kuma ina bukatuwa ga abin da aka ba ni din fa? Sai ya ce masa: ka taimaki wanda aka zalunta. Sai ya ce: Idan kuma na fi wanda zan taimakan rauni fa. Sai ya ce: to ka faranta masa rai, sai ya ce idan kuma ba zan iya yin hakan ba fa. Sai ya ce: to ka kame harshenka face sai kan alheri. Ashe ba zai faranta maka rai ba ka kasance kana da guda daga cikin wadannan siffofi ba da zai kai ka zuwa Aljanna[21]?”.



back 1 2 3 4 5 6 7 next