Daurewa Rayuwar Tare



Kamar yadda kuma ya zo cikin wani hadisin na daban daga Imam Sadik (a.s) daga Manzon Allah (s.a.w.a) cewa tambaya kan suna da nasabar mutum na daga ciki hakkoki na wajibi da kuma gaskiyar abokantaka: “Idan wani daga cikinku yana son dan’uwansa musulmi, to ya tambaye shi kan sunan, sunan mahaifinsa, sunan kabilar da ya fito, saboda hakan na daga cikin hakkoki na wajibi da gaskiyar ‘yan’uwantaka, idan kuwa ba haka ba to sanayyar ta zama sanayyar wawaye[6].

b)– Dariya da Barkwanci

Mai yiyuwa ne mutum a rayuwarsa ta zamantakewa ya hadu da wani abin da zai sashi dariya, shin hakan ta hanyar barkwanci ko kuma ta ganin wani abin ban dariya, a nan dole ne ya yi kokari kula da wannan yanayi ta yadda ba zai kansa ga kyalkyalewa da dariya da daga sautinsa sama ba. An ruwaito Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Kyalkyalewa da dariya daga Shaidan ne[7]”.

A cikin wani hadisin kuma na daban yana cewa: “murmushi shi ne dariyar mumini[8]”.

Daga Abi Ja’afar (a.s) yana cewa: “Idan har kyalkyale da dariya, to bayan ta gama ka ce: Ya Allah! Ka da ka ki ni[9]”.

Ko kuma hadiye dariyar ta hanyar dalili, an ruwaito Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Lalle yana daga cikin jahilci, dariya ba tare da al’ajabi ba”.

Face ma dai Imaman Ahlulbaiti (a.s) sun kirayi mabiyansu wajen karancin dariya da barkwanci, saboda abin da ke cikin hakan na mummunan sakamako na zamantakewa baya ga mummunan tasirinsa ga mutum shi kansa.

Cikin wani hadisi da aka ruwait daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Ina gargadinku da barkwanci saboda yana kawar da ruwan fuska (mutumci)”, sannan yana cewa: “Yawan dariya na kashe zuciya”, sannan yana cewa: “Yawan dariya na narkar da addini kamar yadda ruwa ke narkar da gishir[10]”.

Amirul Muminina (a.s) yana cewa: “Ina gargadinku da barkwanci saboda yana jan mutum zuwa ga kiyayya da kuma gadar da shi[11]”.

Daga Imam Sadik (a.s) yana cewa: “Kada ka yi barkwanci sai a samu karfin gwuiwa a kanka[12]”.

c)– Kunya (Jin Nauyi) da Sakin Jiki Cikin Yarda

Daga cikin wadannan abubuwa har da lizimtuwa da modesty…..cikin abokantaka da rayuwa tsakanin mutane, da rashin mika kai ga atifa ta so da kauna cikin mu’amala, haka nan sakin jiki cikin yarda da mutane ko kauna da kiyayya, dole wadannan abubuwa su kasance karkashin kulawa ta hankali da kasantuwar wasu siffofin na musamman cikin abokin zama. Hakan kuwa bai saba wa kyakkyawan zato da fadaddiyar zuciya ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 next