Matsayin Budaddiyar Zuciya



Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Mutane biyar ko ta yaya a kaurace musu: kuturu, mahaukaci, dan zina da balaraben kauye (bakauye)[17]”.

Nesantar Ma’abuta Sana’oi Na Haramun

Na Uku: Su ne ma’abuta ayyuka da sana’oi na haramun, ko kuma masu sana’oin da ke taimakawa wajen yada fasadi, da masu wargi da hukumce-hukumcen shari’a da ladubban Musulunci, kamar wadanda suka zo cikin wannan hadisi:

Daga Ja’afar bn Muhammad daga Iyayensa (a.s) yana cewa: “Mutane shida ba a musu sallama: Bayahude da Banasare,, mutumin da ke cikin bayan gida, ko wanda ke kan teburin (shan) giya, da mawakin da ke kazafi wa kamammun mataye da masu zagin iyayensu mata[18]’.

A fili abin da ake nufi da sallama ita ce sananniyar gaisuwar nan da ake yi wato ‘Assalamu Alaikum’, amma babu matsala cikin sauran nau’oi na gaisuwa kamar barka da asuba, barka da yamma.

Daga Asbagh bn Nabata, daga Ali (a.s) yana cewa: “Mutane shida bai kamata a yi musu sallama ba: yahuda da nasara, masu lido da dara, mashaya giya da masu goge da gurmi, masu wargi wajen zagin iyayensu mata da mawaka[19]”.

Abu ne a fili cewa abin nufi da mawaki shi ne mawakin da ke kazafi wa kamammun mata ko kuma me wuce haddin shari’a, kamar wasu waka wa azzaluman shugabanni ko kuma masu wakokin batsa kamar yadda Alkur’ani mai girma ya yi nuni da hakan cikin Allah:

﴿ وَالشُّعَرَاء يَتَّبِعُهُمُ الْغَاوُونَ ! أَلَمْ تَرَ أَنَّهُمْ فِي كُلِّ وَادٍ يَهِيمُونَ ! وَأَنَّهُمْ يَقُولُونَ مَا لاَ يَفْعَلُونَ! إِلاَّ الَّذِينَ آمَنُوا وَعَمِلُوا الصَّالِحَاتِ وَذَكَرُوا اللَّهَ كَثِيراً وَانتَصَرُوا مِن بَعْدِ مَا ظُلِمُوا وَسَيَعْلَمُ الَّذِينَ ظَلَمُوا أَيَّ مُنقَلَبٍ يَنقَلِبُونَ ﴾

“Kuma mawaka halakakku ne ke binsu. Shin, ba ku ga cewa, lalle ne su, a cikin kowane rango suna yin dimuwa (su ketare haddi) ba? Face wadanda suka yi imani suka aikata ayyukan kwarai, kuma suka ambaci Allah da yawa, kuma suka rama zalunci, daga bayan an zalunce su. Kuma wadanda suka yi zalunci, za su sani a wace majuya suke juyawa[20]”.

NesantarCakuduwa da Ma’abuta Cututtukan Da Suka Shafi Ciki

Na Hudu: Cakuduwa da ma’abuta cututtukan da suka shafi ciki da masu bazuwa kamar yadda muka gani cikin wasu ruwayoyin da muka kawo a baya. Daga ciki har da ruwayar da aka ruwaito daga Imam Sadik (a.s) daga Iyayensa inda yake cewa: “An karhanta mutum ya yi magana da kuturu sai a tsakaninsu akwai tsawon zira'i”. Sannan yana cewa: “Ka gudu (nesanci) wa kuturu tamkar gudunka daga zaki[21]”.


[1] . Wasa’il al-Shi’a 8:438, Abwab Ahkam al-Ashra’, babi na 34, hadisi na 1.



back 1 2 3 4 5 6 next