Matsayin Budaddiyar Zuciya



b)- Alakokin da suke haifar da tuhuma ta kaucewa ta akida, tunani ko kuma siyasa, kamar abokantaka da ma’abuta bidi’a da bata ko kuma zama da su, ko kuma karatu a wajensu, saboda an yi hani ga hakan.

An ruwaito Abi Abdillah (a.s) na cewa: “Kada ku yi abokantaka da ma’abuta bidi’a, kada ku zauna tare da su don za ku kasance tamkarsu a idon jama’a. Manzon Allah (s.a.w.a) na cewa: Mutum yana kan tafarki (addinin) aboki da na kusa da shi ne[12]”.

Nesantar Muggan Abokai

Na Biyu: Batattun mutane masu muggan dabi’u da ake kira da ‘muggan abokai’, saboda mutum zai cutar da kansa da tasirantuwa da su sakamakon zama da su, don kuwa a dabi’ance mutum ya kan tasirantu da wanda yake zaune da shi.

An ruwaito daga Amirul Muminina (a.s) cewa Manzon Allah (s.a.w.a) ya ce: “Ku kula da wanda kuke magana da shi, don kuwa babu wanda mutuwa za ta zo masa face sai an misalta masa abokansa wajen Allah, idan ma’abuta alheri, to (zai ga) alheri, idan kuwa ma’abuta sharri ne, to (zai ga) sharri, babu wanda zai mutu face sai an misalta masa yayin mutuwa[13]”.

An ruwaito daga Abil Hasan (a.s) yana cewa: “Isa (a.s) ya ce: Hakika ashararin aboki ya kan juya baya, mugun aboki ya kan fadi, don haka ku yi dubi kan wannan za ku yi aboki da shi[14]”.

Na’am babu laifi idan har abokantakar ta kasance ne saboda manufa mai kyau kamar shiryar da shi, ko kuma saboda wata halaltacciyar maslaha ta addini ko ta duniya.

Muggan abokan da aka ambaci siffofi da sunayensu cikin ruwayoyi su ne:

1- Wadanda suke da muggan dabi’un da suka saba wa shari’a, misali, fajiri, makaryaci, mai yanke zumunta, marowaci, matsoraci (rago) ko kuma wawa.

An ruwaito Abi Abdillah (a.s) yana cewa: “Amirul Muminina (a.s) ya kasance idan ya hau mimbari yana cewa: Yana da kyau ga musulmi da ya nesanci abokantaka da mutane uku: maras kunya fajiri, wawa da makaryaci. Don shi maras kunya fajiri, zai kawata maka ayyukansa, zai so ka zamanto kamarsa, ba zai taimake ka kan al’amurran da suka shafi addininka ba, makomarka (ranar kiyama), babu abin da za ka samu wajen zama da shi face bushewar zuciya, shiga da fitansa ba za su kasance komai gare ka ba face zubar da mutumci. Shi kuwa wawa ba zai nufe ka da alheri ba, ba kuma zai so kawar da wata cutarwa daga gare ka ba ko da kuwa ya yi kokari, mai yiyuwa ya so amfanar da kai sai ya cutar da kai, mutuwarsa ita tafi alheri daga rayuwarsa, shirunsa shi ya fi daga maganarsa, nesantarsa ita tafi alheri da kusancinsa. Shi kuwa makaryaci, rayuwa da shi ba za ta kasance abin farin ciki ba, zai yada maganganunka sannan kuma zai zo maka da maganganu. A duk lokacin da wani labari ya gushe zai kirkiro wani na daban, ta yadda ko da ya fadi gaskiya babu wanda zai gaskata shi, ya kan raba kan mutane da sanya gaba da kiyayya cikin zukata. Don haka ku ji tsoron Allah, ku yi dubi don kanku[15]”.

2- Jahilai, kaskantattu a idon al’umma, ko kuma wadanda aka barsu a baya wajen hankali da wayewa kamar mahaukata, dolaye, kaskantattu da ‘ya’yan zina.

Ammar bn Musa na cewa: Abu Abdullah (a.s) ya ce: “Ya Ammar! Idan kana son ni’ima ta zo maka, sannan ka samu cikan mutumci kuma rayuwa ta yi maka kyau, to kada ka sanya bayi da kaskantattun mutane cikin lamurranka, don kuwa idan ka amince musu za su ha’ince ka, idan suka maka zance za su maka karya, idan wani bala'i ya fada maka za su guje ka, idan kuwa suka maka alkawari za su saba maka”, ya ce: na ji Aba Abdillah (a.s) yana cewa: “Kaunar mutanen kirki ga mutanen kirki sakamako ne ga mutanen kirki, kaunar fajirai ga mutanen kirki falala ce ga mutanen kirki, kiyayyar fajirai ga mutanen kirki kawa ce ga mutanen kirki, kiyayyar mutanen kirki ga fajirai wulakanci ne ga fajirai[16]”.



back 1 2 3 4 5 6 next