Hadisan manzo (SAW)



Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Mafificin mutane wanda mutane suka amfana dashi.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنَّ أبخَلَ النَّاسِ مَـن بَخَلَ بـِالسَّـلامِ .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Hakika mafi rowarmutane shi ne wanda yayi rowa dasallama.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: لينوا لِمَن تُعَلِّمون َولِمـَن تَتَعَلـَّمـونَ مِـنـهُ .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Ku tausasawa wanda kukekoyarwa da kuma wanda kukekoya daga gare shi.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: أحسِن إلى مَن أساءَ إلَيكَ .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Ka kyautata wa wandaya munana maka.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: المُسلِمُ مَن سَلِمَ المُسلِمونَ مِن لِسانِهِ ويَدِهِ .

Manzon Allah (S.A.W) ya ce : Musulmi shi ne wanda musulmi suka kubuta dagaharshensa da hannunsa.

قال رسول الله صلّى الله عليه و آله: إنّي أمزَحُ ولا أقولُ إلّا حَقاً .



back 1 2 3 4 next