Kabarin manzo



 Sannan Allah yana ce wa Wasu gungun mutane wadan da suke Hayaniya a bayan gidan Manzo suna cewa:Ya Muhammad ka yi sauri ka fito daga cikin gida,Allah yana kaico da halinsu, yan cewa:"Lallai wadan  da suke kiranka daga bayan gida mafi yawansu ba su da hankali".Hujurat:4

 Sannan ya cigaba da cewa girmama manzo a lokacin da ba shi da rai kamar lokacin da yake da ra ne babu bambanci.

  Lokacin da Mansur ya ji wannan magana sai ya zo da kansa wajen Malik ya ce:A lokacin da nake addu'a zan kalli kibla ne ko kuwa kabarin manzo?

  Sai Malik ya ba shi amsa da cewa:Me ya sa zaka juya wa manzo baya alhali kuwa shi ne tsaninka kuma tsani ga babanka Adam har zuwa ranar tashin kiyama,don haka ka kalli kabarin manzo ka nemi ceto daga gare shi Allah ya amshi cetonka.Allah yana cewa:A lokacin da suka zalunci kawunansu suka zo gare ka suna neman gafarar Allah manzon zai nema musu gafara.."Kadhi Iyadh asha1/2:fasali na 9 206.

 Ziyarar Kabari da kiyaye asali:

 A cikin wannan bahsi namu mai tsawo kawai mun yi amfani ne da ruwayoyin da suke nuni akan wannan al'amari daga ruwayoyin Ahluls Sunna.Amma muna da ruwayoyi da dama daga maruwaitammu na shi'a da suka ruwaito daga Imaman Ahlul bait as. Wadan da ba mu yi nazari akansu ba.Sdaboda haka idan aka duba littafan hadisai na shi'a za a tabbatar da wannan al'amari cewa,ziyarar manzo da Ahlul bait a.s yana daga cikin abin da yake karbabbe ga kowa a cikin wannan mazahaba ta Ahlul bait a.s. sakamakon haka ne aka rubuta littfai da dama akan hakan  wadan da a ka fi sani da suna "almazar"wato wurin ziyara, daga cikin wadan nan littfai kuwa wanda duk ya fi shahara shi ne,"Alkamil Ziyarat" wanda shehin malamin nan mai suna Ja'afar bn muhammad bn kulawaihi ya rubuta.(ya yi wafati 367H).

  Anan zamu kara da cewa ,kiyaye abubuwan da suke na  asali  yana daya daga cikin ayyukan addinin musulunci.Abin da muke nufi da asali kuwa shi ne abin da yake bayyanar da gaskiyar musulunci da cigabansa har ya isa zuwa ga dukkan zamunna.

 Addinin musulunci addini ne da yake na duniya baki daya,don haka har ya zuwa tashin kiyama zai kasance matsayin addini cikakke har karshen duniya.Saboda haka dole ne mu yi iya koarinmu muga cewa mun kiyayen asalimn wannan adini don ya isa kamar yadda ya zo zuwa ga wadan da zasu zo a nan gaba.

   Saboda haka ziyarar kabarin manzo da ahlul bait a.s. yana daya daga cikin kiyaye asalin addini,don haka barin hakan bayan wani tsawon zamani sai ya zamana an manta da wannan babban aiki mai albarka.Saboda haka dangane  da wadanda zasu zo nan gaba sai a zamana wadannan wurare na musamman na manyan bayinAllah ya koma kamar wani abin tatsunniya.

  Kasancewar Zuwan Isa a.s a yau wani abu ne wanda ba abin shakka ba ga al'ummar musulmi,amma a yammacin duniya musamman ga matasa al'amarin Annabi Isa ya zama kamar wani abin tatsunniya, wannan kuwa ya faru ne sakamakon rishin wani abu wanda yake nuna gaskiyar samuwar shi Annabi Isa a.s. a hannayen muatane.Wannan kuwa ya faru ne sakamakaon canza littafinsa da a ka yi, don haka dangane da shi kansa Masih da mahaifiyarsa da sauran manyan sahabbansa babu wani abu na  hakika wanda yake tabbas daga garesu ya ke.Don haka sakamakon tsawon zamani a  yau al'marin masihiyya ya zamana kimarsa ta rage kuma ya shiga cikin wani halin kokwanto da rishin tabbas.Kamar yadda a yau ziyarar manzo wadda take daya daga cikin abu na asali a cikin addinin musulunci kuma mai nuna hakikanin matsayi da samuwar manzo tana neman ta zama wani abu marar muhimmanci a cikin al'ummar musulmi,koma ya zamana an ajiye ta a gefe guda.Don haka sakamakon tsawon zamani akwai yiwuwar abubuwan asali na addinin musulunci da waliyyan Allah, su shiga cikin wannan hadari mai girma.

  Saboda haka al'ummar musulmi dole ne su tashi tsaye domin kare wannan hadari da ya fuskanto su,wannan kuwa yana samuwa ne ta hanyar kiyaye duk wani abu da ya shafi sakon mazanci da Imamanci, ta yadda  za a rika tuna shi a ko wane zamani.Saboda haka ziyarar wadannan manyan bayin Allah tana daya daga cikin hanyoyin kiyaye su daga bacewa da kuma yin tunani a kansu a kowane lokaci.Saboda haka sakamakon yin kahan ba za a taba watsi da matsayin wannan muhimmin al'amari ba, ta yadda za iya kulle kofar ganawa ta hanyar ruhi da wadannan manyan bayin Allah ga al'ummar musulmi.

   Saboda haka da ikon Allah a nan gaba zamu yi magana akan kiyaye wadannan wurare masu tsarki.



back 1 2 3 4 5