Kabarin manzo



3-Imam Sadik a.s. daga manzon tsiara s.a.w.a. yana cewa:"Duk wanda ya zo Makka don aikin hajji amma bai ziyarce ni ba,zan banzatar da shi a ranar tashin kiyama,wanda kuwa ya ziyarce ni cetona ya wajaba a garesa,duk wanda cetona ya wajaba a garesa,aljanna ta wajaba a garesa.Saduk:Ilalish shara'i'i

4-Imam Sadik a.s. yana cewa manzo .s.a.w.a.yana cewa:"Duk wanda ya ziyarce ni zan zama mai cetonsa a ranar tashin kiyama".b kulawaihi:Kamili ziyarat:12majalisi:Bihar:97,142.

Ruwayoyin da dukkan bagarori guda biyu suka ruwaito ta   fuskar ma'ana ba su da bambanci,saboda haka suna karfafa abubuwa guda biyu kamar haka:

A-Duk wanda ya je Makka bai ziyarci manzo ba to ya yi wa manzon jifa'i.

B-Duk wanda ya ziyarci manzo manzo zai cece shi a ranmar kiyama. Saboda haka don  mu takaita wadannan ruwayoyi guda takwas daga shi'a da sunna sun wadatar wanda yake son karin bayani sai ya koma zuwa ga littfan da muka ambata.

   Tattaunawar Imam Malik tare da Mansur Dawaniki:

Kadhi Iyadh ya nakalto tattaunawar Imam Malik tare da Mansur Dawaniki kamar haka:

Mansur Dawaniki wanda yake khalifa ne mashahuri  na Abbasiy, wata rana ya shiga haramin manzo yana magana da karfi.

 Malik a lokacin shine Fakih a Madina sai juya zuwa ga Mansur ya ce:ya kai shugaban Muminai,kada ka daga muryarka a cikin wannan masallaci,Allah madaukaki ya koyawa wasu muatane ladabi inda  yake cewa:"Kada ku daga muryarku saman muryar Annabi"Hujurat:2.

  Sannan ya ya bi wasu gungu daga cikin mutane ya ce:Lallai wadan da suke kasa da muryarsu a gaban manzon Allah, su  ne wadan da Allah ya jaraba zukatansu da takawa"hujurat:3



back 1 2 3 4 5 next