Ayyuka da Sakamako 2



2-Malaman Hanafiyya suna cewa: Idan mutum bai yi wasiyya ba sai ya rasu, sai wani daga cikin magadansa ya yi masa hajji, aikinsa zai karbu da izinin Allah.

3-Shafi’iyya suna cewa: Duk lokacin da mutum ya kasa gabatar da aikin hajji, bayan mutuwarsa wani yana iya yi masa a madadinsa. [5]

Idan muna so mu kawo ra’ayoyin dukkan malaman fikihu na AhlusSunna dangane da wannan al’amari ne zamu tsawaita magana ne a kansa, don haka zamu wadatu da abin da muka ambata a sama, abin da kawai ya yi saura a nan shi ne mu yi bayani a kan wasu kalubale da wasu suka kawo dangane da hakan.

 

Kalubale Na Farko

Masu kalu balantar wannan al’amari suna cewa Kur’ani mai girma yana nuna cewa mutum kawai zai iya amfana da abin da ya aikata ne, kamar inda yake cewa: “Mutum ba shi da wani abu sai abin da ya aikata”[6].

Saboda haka ta yaya zai zamana ayyukan da wasu zasu yi don mamaci ya amfana da su, alhalin babu wani kokari da ya yi wajen aiwatar da hakan.

 

Amsa

Amsar wannan kalubale kuwa a fili yake, da sharadin cewa mu fahimci ma’anar wannan aya da kyau:



back 1 2 3 4 5 6 next