Ayyuka da Sakamako 2



Ayyuka Da Kyakkyawan Sakamako 2

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Nazarin Malaman AhlusSunna

Domin mu karasa kammala bahsin, a nan zamu cika da maganganun wasu daga cikin manyan malaman Sunna guda biyu kamar haka:

1-Khalidi a cikin litttafinsa (Sulhul Ikhwan) yana rubuta cewa: Yin bakance yana bisa ma’aunin niyyar da masu bakancen suka yi, domin kuwa “dukkan ayyuka suna tare da niyya” wato abin da mai bakance ya yi nufi. Idan ya zamana don neman kusanci ne ga mamacin to babu shakka wannan bai halatta ba. Amma idan mutum yana nufin neman kusanci ne zuwa ga Allah, amma da nufin ladar ta je wa wani mamaci wanda ya nufa da hakan, ba wai kawai ya halatta ba idan mutum ya yi alkwari zai yi hakan wajibi ne ya cika wannan alkawarin.[1]

2-Izami a cikin littafin (furkanul Kur’ani) ya kawo cewa: Idan mutum ya yi bincike dangane da alwakrin yanka da suke yi domin annabawa da salihan bayi, zai samu sakamakon cewa, ba su da wata manufa wacce ta wuce yin hakan amatsayin sadakarwa ko kyautar ladar wannan aiki zuwa ga ruhinsu. Sannan malaman AhlusSunna sun hadu a kan cewa yin sadaka zuwa ga ruhin wadanda suka riga mu daga wadanda suke raye, wani abu ne mai yi musu amfani kuma ladar zata isa zuwa garesu. Sannan ruwayoyin da suka zo dangane da hakan ingantattu ne kuma mashahurai ne.[2]

Abu Dawud tare da dangane zuwa ga Mai muna ya ruwaito cewa: Babana ya tamabayi Manzo (s.a.w) yana cewa ya manzon Allah! Na yi bakance (alkawari) cewa idan Allah ya ba ni da namiji, zan yanaka raguna a (Bawana) sunan wani wuri ne, sai yake cewa ban fahimta ba da kyau, amma mai muna yana magana ne a kan raguna guda 50.



1 2 3 4 5 6 next