Neman Tabarruki2



2-Soyayyar al’ummar musulmi ga Manzo shi ya sanya duk wani abu da ya shafi shi manzon suke girmama shi, don haka ne ya sanya duk kankantar wani abu da ya bari wanda ya hada daga takobi, hula, takalmi gashi, farce, da abin da ya sha ruwa a cikinsa, da abin da yake zuba ruwa a cikinsa, da rijiyar da Manzo ya sha ruwa a cikinta, duk sun kasance suna kiyaye su suna kuma girmama wadannan abubuwa, haka nan suna neman tabarruki da tufafin Manzo da makamancinsa, sanann ya kasance zoben Manzo yana zagaya a tsakanin yatsun sahabbai.

Daga karshe zamu yi tunatarwa da wasu abubuwa guda biyu kamar haka:

1-Ahmad Bn ham Hambal shugaban mazhabar Hambaliyya wanda yake da girma a tsakanin ‘yan Sunna, ya ksance yana da ra’ayoyi masu yawa dangane da abin da ya shafi neman tabarruki, a nan zamu kawo wasu daga cikin maganganunsa a matsayin misali:

A-Dan Abdullah yana cewa: Na tambayi babana a kan cewa na ga wani mutum yana dora hannunsa a kan mimbarin Manzo da nufin ya neman tabrruki kuma yana sumbatarsa, sannan ya yi hakan ne ga kabarin Manzo da nufin neman lada, sai babansa ya amsa masa da cewa: babu laifi. [4]

Ahmad Bn Muhammad makarri Maliki (ya rasu 1041) a cikin littafinsa mai suna fathul muta’al yana ruwaitowa daga waliyyuddin Iraki yana cewa, Ustaz Abu Sa’id ya ruwaito daga wani littafi dadadde wanda Ibn Nasir ya rubuta ga abin da yake cewa: Na tambayi Imam Ahmad dangane da sumbatar kabari, sai ya amsa mini da cewa babu laifi.

Ibn Nasir ya kara da cewa, na nuna wa Ibn Taimiyya wannan littafi, sai ya kasance ya yi tsananin mamaki daga maganar Imam Ahmad, sai na ce masa ai babu mamaki a cikin wannan magana, Imam Ahmad shi ne wanda ya kasance ya sha ruwan da aka wanke rigar Shafi’i da shi[5]. Idan har Ahmad dangane da malamansa yana yin haka to ina ga wadanda suke samansu har zuwa abin da yake daga manzon Allah (s.a.w)[6].

Abu na biyu kuwa shi ne a shekarun baya an rubuta wasu litattafai guda biyu a kan neman tabarruki wanda daya daga ciki malamin sunni ya rubuta daya kuwa malamin Shi’a ya rubuta shi, sannan dukkan su biyun sun yi bayani da kyau kamar yadda ya dace. A nan zamu gabatar da wadannan litattafai guda biyu ga masu karatu kamar haka:

1-Ta barrukus sahaba bi asararir rasul (s.a.w) wanda babban malamin nan kuma masanin tarihi wato Allama Muhammad Tahir Bn Abdulkadir Bn Mahmud Maliki ya rubuta, kuma an rubuta wannan littafi a shekara ta 1385 a Alkahira a madaba’a ta madni.

2-Attabarruk: Wanda muhakkik Ayatullahi Ali Ahmadi Miyanji ya rubuta (1385-1421) wanda ya koma ga rahamar Allaha shakarun da suka gabata, a cikin wannan littafi na sa ya yi bincike da kyau dangane da wannan magana ta hanyar hadisai da tarihi, ta yadda ya tabbatar da tarihin musulmi a kan hakan. Ta yadda babu sauran shakku dangane da wannan al’amari.

Daga karshe zamu iya daukar sakamako cewa abin da yake faruwa a yau kuma muke gani a kabarin Manzo ta yadda wasu gungu a karkashin “yan amru bil ma’aruf da hani da mummuna, suke daukar duk wani nau’i na nuna kauna da soyayyar Manzo a matsayin bidi’a da shirka, wani zunubi ne wanda ba za a yafe shi ba, wanda ya samo asali da rashin fahimtar hakikanin addinin musulunci, idan da wadannan masu wannan aiki zasu amince da shirya tarukan karawa juna ilimi, da gaskiya ta bayyana daga cikin duhu, ta yadda kafirtawa ko fasikanta al’ummar musulmi yakau, ta yadda soyayyar muslunci ta maye gurbin gaba da kiyayya.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012





back 1 2 3 4