Neman Tabarruki2



Urwa Bn Mas’ud Sakafi wanda ya kasance wakilin kuraishawa a sulhun Hudaibiyya, ya ga wannan al’amari yayin da ya koma ya gaya wa kuraishawa inda yake cewa: Sahabban Muhammad domin su samu ruwan alwallarsa sukan yi buge-buge, ya ci gaba da cewa ba wai kawai ruwan alwallarsa da wanka ba, har da ruwa da abincin da ya rage, ko kuwa kwanon da ya ci abinci ko rijiyar da ya sha ruwa sukan nemi tabarruki da ita. [2]

 

Neman Tabarruki Da Kabarin Manoz (s.a.w)

A- Marwan Bn Hakam ya shiga masallaci, sai ya ga wani mutum ya kafa fuskarsa bisa kabarin Manzo (s.a.w) sai Marwan ya dago kansa ya jawo shi baya ya ce masa: “Ka san abin da kake yi kuwa? Sai wannan mutum ya dago kansa, sai khalifa ya gane cewa Abu Ayyub Ansari ne wanda yake daya daga cikin manyan sahabban Manzo (s.a.w) kuma wanda ya sauki Manzo yayin da ya zo a Madina. Abu Ayyub sai bai wa Marwan amsa, ga abin da yake cewa: Ni ban zo nan ba sabo da dutse, na zo ne saboda manzon Allah, Ya kai Marwan na ji daga Manzo yana cewa: Zuwa lokacin da mutanen kirki suke jagorantar musulunci kada ku yi kuka a kan haka, amma ku yi kuka yayin da ya zamana wadanda ba su cancanta ba suke shugabancin musulunci, wato kai da gidan Amawi. Wannan bangare na tarihi, Hakim Nishaburi ya kawo shi a cikin Mustadrikul sahihaini yana nuna mana yadda ya kasance manyan sahabban Manzo suke neman tabarruki da kabarin Manzo a lokacin rayuwarsu. Sannan yana nuna mana kiyayyar wasu daga cikin wadanda ba su da soyayyar Manzo a cikin zuciyarsu kamar irinsu marwan a kan yin wannan al’amari na neman tabarruki.

B-Bilal Habashi wanda yake shi ma daya daga cikin manyan sahabban Manzo wanda bayan rasuwar Manzo ya zabi ya yi rayuwa a wani wuri daban sabanin Madina, wata rana ya yi mafarki da Manzo yana ce masa, wannan rashin kula har ina? Lokacin da ya farka daga barci, sai ya yi tunanin ya tafi domin ya ziyarci Manzo, domin kuwa tun lokacin da ya baro Madina bai sake zuwanta ba, don haka goben wannan rana sai ya tafi Madina, lokacin da ya shiga garin Madina, sai ya zauna gefen kabarin Manzo ya yi kuka mai yawa yana goga fuskarsa ga kabarin Manzo (s.a.w) lokacin da ya ga HAsan da Husain (a.s) sai ya rungume su yana sumbatarsu, sannan suka neme shi da ya je inda yake kiran salla a zamanin Manzo domin ya kira salla haka kuwa ya yi kamar yadda muka kawo a baya. [3]

C- A lokacin da Manzo ya yi wafati bayan an rufe Fadima (a.s) ‘yar Manzo (s.a.w) ta je wajen kabarinsa ta yi kuka sannan ta debo kasar kabarinsa ta shafa a fuskarta, Ga abin da take cewa a wasu baituka na waka: Me zai faru ga wanda ya shaki kasar kabarin Ahmad, Don bai shaki turare mai tsada ba a tsawon rayuwarsa. Masifa ta sauka gareni, wacce idan da rana ta saukar wa zata koma dare.

A nan zamu wadatu da wadannan misali da muka kawo daga cikin gomomin misalai da suke tabbatar da neman tabarruki daga Manzo, amma idan aka koma zuwa ga manyan Littattafan hadisi zamu ga yadda wannan al’amari na neman tabarruki ya kasance mutawatir.

Sakamakon Bahsin

Bincike a kan tarihin musulunci yana tabbatar mana da cewa batun neman tabarruki da Manzo ko wani abu wanda aka jingina shi zuwa ga Manzo wani abu wanda ya zama al’adar musulmi a duk tsawon tarihi, sannan manufarsa a kan hakan yana daga cikin dayan biyu:

1-Neman tabarruki da wadannan abubuwan da nufin cewa ni’imar Ubangiji tana biyowa ta nan ne zuwa gare su, kamar yadda ya kasance ni’imar Ubangiji zuwa ga annabi Yakub ta biyo ta hanyar rigar annabi Yusuf (a.s)



back 1 2 3 4 next