Neman Ceto 2



Dalilinsu na biyu a kan haramta neman ceto daga waliyyan Allah shi ne cewa: Dalilin da ya sanya mushirikai zamanin Manzo suka yi shirka, sun kasance suna neman ceto ne daga gumaka, ga abin da Kur’ani yake cewa dangane da hakan: “Sun kasance suna bautar abin da ba ya cutar da su kuma ba ya amfanar da su, kuma suna cewa wadannan su ne masu cetommu a wajen Allah”[9].

Saboda haka duk wani nau’i na neman ceto daga Manzo ko waliyyan Allah kamar neman ceton mushrikai ne da suke yi daga gumaka. [10]

Amsar wannan kiyasi kuwa a fili yake domin:

Na farko: tsakanin wannan neman ceton guda biyu akwai bambanci a bayyane, mushrikai suna kiran gumaka a matsayin alloli, sannan kuma suna ganin su ne suka mallaki ceto da kansu.

Amma su kau musulmai masu kadaita Allah sun dauki annabawa a matsayin bayin Allah, kuma sun yi imani da cewa sunsamu wannan izinin ceton ne daga Allah madaukaki, kuma shi ne mamallakin wannan ceto na asali. Don haka ta yaya za a dauki wannan neman ceton guda a matsayin guda daya?

Na biyu, mushrikai suna bautar gumaka ne, bayan sun bauta musu suke neman ceto daga gare su, sannan wannan aya tana nuna wadannan abubuwa guda biyu ne, (wato bauta da neman ceto) aiki na farko kuwa inda ayar take cewa”suna bautar wanin Allah”aikin na biyu kuwa”Suna cewa wadannan su ne masu ceton a wajen Allah. Alhalin su kuwa musulmai suna bauta wa Allah shi kadai, bayan bautar Allah makadaici sai su nemi ceto daga waliyyansa.

Daga wannan ne zamu fahimci cewa, kwatanta wannan neman ceton guda biyu wani abu ne wanda sam ba shi da tushe.

3-Neman ceto daga mamaci wani abu ne wanda ba shi da wani amfani

Dalilinsu na karshe a kan hani da neman ceto, shi ne mutumin da ya mutu neman ceto daga gare shi ai wani abu ne marar fa’ida.

Amsar wanann kuwa tare da kula da bahsin da muka yi dangane da rayuwar barzahu ya wadatar mu fahimci rashin ingancinsa.

Domin kuwa yayin da ya kasance shahidi a tafarkin Allah yana raye a barzahu, annabin Allah shi ya fi cancanta ya kasance a raye, sakamkon cewa mun yi cikakken bayani dangane da wannan a cikin bahsimmu na rayuwar barzahu, don haka a nan ba zamu mai -mai ta ba.

Mu dauka cewa annabawan Allah matattu ne, ta yadda ba su jin maganarmu, a nan zai zamana neman ceton da muke yi a wajensu ba shi da amfani, ba wai ya haramta ba.

Wanda ya fada a cikin rijiya, idan ya nemi taimako daga masu wucewa, aikinsa ya dace da hankali, amma idan ya nemi tamako daga duwatsun da suke gefen rijiya, to lallai ya yi aikin banza marar amfani, amma bai aikata haram ba, kuma bai shigar da shirka ba a cikin bauta.

Hafiz Muhammad Sa'id - hfazah@yahoo.com – www.hikima.org

Haidar Center for Islamic Propagation (HAIDARCIP)

Facebook: Haidar Center - December, 2012





back 1 2 3 4 5