Neman Ceto 2



3-Sawad Bn Azib da neman ceto

Sawad ya kasance daya daga cikin sahabban Manzo kuma ya yi wa Manzo waka yana neman ceto daga gare shi ga abin da yake cewa: Ya manzon Allah ka kasance mai cetona ranar kiyama, ranar da ceton wasu ba ya da dai-da- da fatan dabino ba ya amfanar da Sawad. [4]

4-Imam Ali (a.s) da neman ceto daga Manzon Allah (s.a.w)

Lokacin da Imam Ali ya gama yi wa Manzo wanka, sai ya bude fuskarsa ya ce masa: “Uwa da ubana fansa gareka, Ka kasance a raye ko ba a raye ba ka tuna mu a wajen ubangijnka”.[5]

Larabawa sukan yi amfani da wannan jumlar “ka tuna ni a wajen ubangijinka” da ma’anar ceto, kamar yadda annabi Yusuf yake cewa wanda suka zauna kurkuku tare yayin da aka fito da shi daga kurkuku, yake ce masa “ka tuna da ni wajen ubangijinka”[6].

Daga karshe zamu yi tunatarwa a kan cewa ayoyi da hadisan da suka zo dangane da kamun kafa da annabawa, dukkansu suna bayar da ma’anar ceto ne, don haka babu bukatar maimaita su a nan.

 

Dalilan Masu Haramta Neman Ceto

Masu haramta neman ceto suna kafa hujja da wasu dalilai wadanda zamu kawo wa masu karatu kamar haka:

1-Neman ceto shirka ne



back 1 2 3 4 5 next