Neman Ceto



Manzo Da Ba Shi Kyauta Har Ya Amince Da Ita

A wata aya ana bayanin cewa Allah madaukaki zai bai wa Manzo kauta har sai ya yarda, kamar yadda aya take cewa:

“Lallai lahira ta fi maka wannan duniya. Da sannu Allah zai ba ka kyauta har zai ka amintaâ€‌[12].

Aya ta biyu tana da rikitarwa ta fuska guda biyu kamar haka:

Na daya: Ba a bayyanar da inda Allah zai bayar da wannan kyauta ba, ta wace hanya aka san cewa ranar kiyama ne zai faru?

Na iyu: Ba a bayyanar da abin da Allah zai bayar ba, watakila abin da za a bayar wani abu ne ba ceto ba.

Amma rikitarwa ta farko ana warwareta ta hanyar kula da abin da ya gabaci wannan aya, domin kuwa Allah ya yabi lahira kuma ya fifita ta a kan duniya, sannan bayan wannan ne yake cewa: “Allah zai ba ka har sai ka yardaâ€‌. Idan muka hada wadannan ayoyi guda biyu zamu gane cewa wurin da za a bayar da wannan kyauta na wannan duniyar ba ce wata duniya ce ta daban.

Babban matsayin Manzo wanda shi rahama ne ga dukkan halitta, yana wajabta masa a wannan rana mai ban tsoro ya tuna da al’ummarsa, ta yadda sakamakon gafarta wa da yawa daga cikinsu ya yi farin ciki da haka. Tare da kula da wannan asali za a kawar da rikitarwa ta biyu a cikin wannan al’amari cewa, ceton al’umma ake nufi da wannan kyauta wanda zai sanya Manzo (s.a.w) ya amince.

Abin da kuwa yake tabbatar da wannan ma’ana shi ne ruwayoyin da suka zo a kan cewa abin da ake nufi da wannan kyauta wacce za a bai wa Manzo har sai ya yarda, shi ne ceton al’ummarsa.[13]

Zuwa nan mun fa’idantu daga Kur’ani dangane da asalin ceton, sannan hadisai da suke Maganakan ceto saboda yawansu sun fi gaban muka kawo su duka a nan, saboda haka daga wadannan ruwayoyi wadanda suke sama da dari zamu takaita ne kawai da wasu daga cikinsu.



back 1 2 3 4 5 6 7 next