Neman Ceto



1-Ceto a ranar lahira yana hannun Allah madaukaki ne, wato komai zai samu tushe ne daga gare shi, wato shi ne zai tayar da mai ceto sakamakon matsayi na musamman da yake da shi zai ba shi izinin yin ceto, ta yadda Allah zai gudanar da rahamarsa da jinkansa ga bayinsa ta hanyar shi wannan bawa nasa, amma a duniya abin sabanin haka yake, domin kuwa mai laifi ne zai tayar da wanda zai shigar masa tsakani, idan da bai sanya wanda zai shigar masa ba, shi da kansa ba zai yi tunanin yin hakan ba. Idan har Kur’ani yana ba da umarni ga wadanda suka yi zunubi da su je wajen manzon Allah a nan duniya, domin ya nema musu gafarar Allah, don haka wannan ma zai samo asali ne daga shi Allah madaukaki, domin kuwa zai bai wa masu zunubi umarni da su yi wannan aiki, domin idan da bai bayar da wannan umurnin ba, to da babu yadda za a yi su je wajen Manzo (s.a.w) idan kuwa har ma sun tafi ba tare da umurnin Allah ba to da zuwansu ba zai yi wani tasiri ba.

2-A cikin ceto na gaskiya mai ceto yana karkashin inuwar rububiyya ne, amma a cikin ceton na bata, mai karfi zai tasirantu da maganar mai ceto ne, sannan shi kansa mai ceto ya tasirantu da maganar mai laifi ne.

3-A cikin ceto na duniya nuna bambanci ne kawai a cikin dokoki, ta yadda karfin mai ceto zai yi tasiri a cikin mai kafa doka ko mai tafiyar da doka ya rinjaye shi, ta yadda mai karfi kawai zai iya gudanar da dokarsa a kan raunana. Amma a ceton lahira babu wani wanda zai gwada wa Allah karfi ya rinjaye shi ko ya tilasta shi, sannan babu wanda zai iya hana a gudanar da doka. Ceton rahamar Ubangiji wanda yake mai fadi ya samo tushe ne daga shi kansa Allah madaukaki mai tausayi, yana so ne ta wannan hanyar ya tsarkake wasu daga cikin bayinsa wadanda suka cancanci hakan kuma zasu iya karbar wannan tsarkakewar.

Amma gungun da ba zasu samu ceto ba, ba ya nufin cewa ba akwai nuna bambanci a cikin dokokin Ubangiji, wannan yana nufin cewa su wadannan ba su cancanci samun wannan rahama mai fadi ba ce ta Allah ta’ala, don haka ne zasu yi saura a cikin wannan hali da suke ciki. Rahamr Ubangiji ba kamar akwatin banki ko na wani dan kasuwa bane, ta yadda zai iya karewa, rahamar Allah ba ta karewa sai dai ya zamana wanda za a ba bai cancanci ya karbi wannan falalar ba, balantana ya samu wannan rahama.

Idan Allah yana cewa: “Allah ba ya gafarta wa Mushrikaiâ€‌[1], wannan ya samo asali sakamakon cewa zuciyar mushrikai kamar wani jarka ce a rufe, idan da za a saka shi a cikin kogi guda bakwai ruwa ba zai taba shiga a cikinsa, ko kuma kamar kasar da ba ta yin noma mai gishiri, duk yadda aka yi ruwa babu wani abu wanda zai faru sai dai ta jike ko kaya ta fito daga gareta.

Idan Kur’ani yana Maimaita cewa, ceto a ranar kiyama zai kasance daga wadanda Allah ya amince wa, kamar yadda yake cewa: “Babu wanda zai yi ceto sai dai wanda muka yardar mawaâ€‌[2]. Wannan ya faru ne sakamakon ya san cewa wane ne daga cikin bayinsa ya cancanci baiwar Allah madaukaki da wanda bai cancanci wannan baiwar ba. Ba wai kawai mushirikai ba zasu rahamar Allah da ceton waliyyan Allah ba, har da wadanda saboda tsananin zunubinsu ba zasu cancanci samun wannan gafarar ubangijin ba, don haka ceton bayin Allah ma ba zai kai zuwa garesu ba.

Dalilai Daga Kur’ani Dang­ane Da Ceto

Ayoyin da suka zo dangane da ceto manyan bayin Allah sun fi gaban mu kawo dukkansu a cikin wannan bahasi, don haka zamu kawo wasu daga cikinsu ne, domin mai karatu ya samu cikakkiyar masaniya dangane da batun ceto da sharuddan da suke tattare da yin hakan, wanda muhimmi daga cikinsu shi ne izinin Allah madaukaki. Saboda haka za a ambaci wani asali tabbatacce duka da yake ba za a kawo sunayen masu ceto ba, amma za a kawo siffofinsu das sharuddansu wannan ya wadatar, kamar haka:

A nan zamu ambaci ayoyi guda biyar idan muka kula da kayu zasu tabbatar mana da wasu abubuwa guda biyu kamar haka:

A-Ceto a ranar kiyama ya samo tushe ne daga Kur’ani.



back 1 2 3 4 5 6 7 next