Neman Ceto



Ceto Ko Yaye Zunubbai

 

Mawallafi: Ayatullahi Ja’afar Subhani

Mai Fassara: Yunus Muhammad Sani

Gyara da Tsarawa: Hafiz Muhammad Sa'id

Ceto wani asali ne wanda Kur’ani da sunnar Ma’aiki suke tabbatar da shi, sannan dukkan kungiyoyin musulmai sun amince da shi ba tare da wani shakku ko kokwanto ba. Hakikanin ceton waliyyan Allah kuwa shi ne, sakamakon matsayin da suke da shi a wajen Allah, a cikin wani yanayi na musamman sai su roki Allah ya gafarta wa wasu daga cikin bayinsa laifukan da suka yi a kan takaitawarsu.

Waliyyan Allah ba kowane mutum mai sabo ne zasu ceta ba, zasu ceci mutumin da kawai ya kasance alakar imaninsa da Ubangiji ba ta yanke ba, haka nan alakarsa da wadannan waliyyan Allah ba ta yanke ba. Da wata ma’ana shi ne idan ya kasance bai nisanta ba daga halayen kwarai na ruhi, ta yadda mutum zai kai wani matsayin da ba zai yiwu ya sake komawa mutumin kirki ba.

Batun ceto kasantuwar yadda yake abu tabbatacce a tsakanin musulmai ta yadda duk wani malami ko masani na musulunci ka tambaya zai ba ka amsa da cewa ai ceto yana daya daga cikin akidun musulunci. Sannan kodayaushe a cikin addu’’o’i nuni ga wadannan masu ceto na hakika. Mafi yawancin mutune suna cewa: Ya Allah ka sanya Manzo a matsayin mai cetommu, kuma ka sanya cetonsa a gare mu karbabbe ne!

Gudanar falalar Ubangiji ta hanyar ceton masu ceto

Duniyar halitta ta kafu ne a kan tsari na dalili da sanadi (wato duk abin da zai faru yana da dalili da na sanadi a kan faruwarsa) Sannan bukatocin danAdam na duniya suna samuwa ne ta hanyar wasu daga cikin bayin Allah tare da izinin Ubangiji. Falala da ni’imar ruhi ma ba ta fita ba daga cikin wannan tsari, Shiryarwa da gafarta zunubbai duk suna daga cikin kwarar ni’imar Ubangiji, kuma suna karkashin wannan tsari.



1 2 3 4 5 6 7 next