Sakon Ali a.s ga Malik Ashtar



Sharuddan abokai na musamman ga shugaba
Kuma ka damfaru da masu tsantseni (gudun haram), da gaskiya, sannan sai ka yi musu kashedi kan cewa kada su sake su zuga ka da kambama ka (da yabon da zasu kai ka inda ba ka kai ba), kuma kada su kuranta ka da wata barna da ba ka yi ta ba, domin yawaita kambamawa tana haifar da kwalisa, kuma tana nisantarwa daga izzar (daukaka).

Siyasar karfafa masu kwarewa a hidimar al'umma
(Binciken wazirai (mataimaka))
Kuma kada mai kyautatawa da mai munanawa su kasance daya a gunka, domin wannan zai sanya tauyewa ga ma'abota kyautatawa a kyautatawarsu, da kuma ingiza masu munanawa a kan munanawarsu, sai dai ka dora wa kowannensu abin da ya dora wa kansa (mai kyautatawa ya ga sakamako mai kyau, mai munanawa ya ga munanawa).

Saukake nauyin da yake kan mutane da kyautata musu zato
(Siyasar bayan da 'yanci ga mutanen kasa da kyautata musu zato)
Ka sani cewa babu wani abu da ya fi ye wa wani shugaba ga al'ummarsa fiye da kyautata zato (garesu), da saukakewarsa garesu nauyin da yake kansu na rayuwa, da barin tilastawarsa garesu kan abin da ba daga garesu yake ba, to ya kasance kana da wani lamari kan haka da zai kasance kana da kyakkyawan zato ga al'ummarka da shi, domin kyautata zato yana yanke maka surkukiya mai nisa, kuma wanda ya fi cancanta ka kyautata masa zato shi ne wanda jarabawarka ta kyautata gunsa (wanda ka jarraba shi ka ga yana da amana), kuma wanda ya fi cancanta da munana zato shi ne wanda jarabawarka ta munana gunsa (wanda ka jarraba shi ka ga yana da ha'inci).

Matsayin jagora ga al'adun al'umma
(Girmama al'adun zamantakewar al'umma da kyautata su)
Kuma kada ka rushe wata al'ada mai kyau da farkon al'umma suka yi aiki da ita, al'umma ta saba da ita, jama'a su samu gyaruwa saboda ita.
Kuma kada ka farar da wata al'ada da zata cutar da wani abu da ya gabata na al'adun farko, sai ya kasance ladan yana ga wanda ya farar da ita, zunubi yana kanka saboda ka rusa ta.

Duba al'amura tare da kwararru da masana
(Masu bayar da shawarwari a al'amura masu muhimmanci)
Ka yawaita tuntubar ilimin malamai, da zaman (tattaunawar) masu hikima domin tabbatar da abin da zai gyara lamarin kasarka, da tsayar da abin da ya tsayar da (gyaran) al'umma kafin zuwanka.

Yanayin al'umma dabakoki ne daban-daban
Ka sani jama'a hawa-hawa ne, ba yadda za a yi wasu su samu gyaruwa sai da wasunsu, kuma ba yadda za a yi wasu su wadatu daga wasunsu.

Jama'un al'umma kala bakwai
Daga cikinsu akwai rundunar Allah (jami'an tsaro), daga cikinsu akwai dabakar kasa (na mutane) da dabakar sama (na mutane), daga ciki akwai alkalan adalci (kotu), daga ciki kawai ma'aikatan adalci da tausayi da jin kai (masu kula da walwalar jama'a), daga ciki akwai ma'abota jiziya da haraji daga mutanen amana (wadanda ba musulmi ba) da musulmin mutane. Daga ciki akwai 'yan kasuwa da masu sana'o'i, daga cikin akwai dabakar kasa daga masu bukatu da miskinanci, kuma kowanne Allah ya fadi rabosa, ya sanya masa wani rabo nasa a littafinsa da sunnar annabinsa, wannan wani alkawari (sani da amana) ne da aka kiyaye shi a gun mu.

Sojoji da 'Yan sanda
Runduna ('yan sanda) da izinin Allah su ne kariyar al'umma, adon jagorori, daukakar addini, hanyoyin samun aminci, kuma ba yadda za a yi al'umma ta daidaitu sai da su.
Kudin shigar kasa na haraji
Sannan su kuma rundunoni (sojoji) ba yadda za a yi su samu tsayuwa sai da abin da Allah ya fitar musu na daga harajin (dukiyar kasa), da zasu karfafu da shi a kan yakar makiyansu, su dogara kansa cikin abin da zai gyara su, kuma ya dauke musu bukatunsu.

Ma'aikatar Kotuna
Sannan su kuma wadannan nau'i biyu ('yan sanda da sojoji) ba yadda za a yi su daidaitu sai da wani nau'i na uku na alkalai da ma'aikata da sakatarori, da (su alkalai) zasu yi hukunci da shi na al'amuran da suka shafi kulla (kasuwancinsu da yarjejeniyoyi), da abin da (su ma'aikata) zasu tara na amfani, da dogaro da za a yi da su (sakatarori) kan abubawan da suke kebantattu da na gaba dayan jama'a.

'Yan kasuwa da masu sana'o'i
Su kuwa duka wadannan ba yadda za a yi lamarinsu ya daidaitu sai da masu sana'o'i na abin da suke taruwa kansa na kayan ciniki, da abin da suke kasuwanci a kasuwanninsu, kuma su dauke wa (sauran al'umma kamar ma'aikata da runduna) nauyin yin kasuwanci da kansu, da kasuwancin waninsu (wadanda ba 'yan kasuwa ba) ba zai kai nasu ba.



back 1 2 3 4 next