Hakkin Ji



 

 

 

 

 

Ji yana da cikin ni'imomin da Allah madaukaki ya yi mana a matsayin bayinsa, ya sanya shi kofa ce ta kaiwa zuwa ga cuciya, don haka ne da ji ne ake hankaltar abubuwa a fahimce su, da ji ne muke samun ilimi, sai dai da hankali ne muke tacewa. Duk wata magana zata bi ta cikin kunne, amma ba dukkan magana ba ce karbabbiya sai sahihiya, don haka ne ya hau kanmu mu yi wa dukkan wata magana tankade da rairaya, idan mun ga sahihiya ce sai mu karba, idan kuwa ba haka ba sai mu ajiye ta.

Ya wajaba a kiyaye ji daga sauraron haram da jita-jita musamman ga mai maganar da an san ba ta da tushe, da yawa mutanen da aka saurare su maganarsu ta zama bala’i ga al’umma da mai sauraron. Haka nan ana son sauraron magana mai amfani kamar ta Ilimi da sauraron karatun Kur’ani (musamman ga mai ciki), kuma mai magana da kai yana da hakkin ka saurare shi idan ya gama maganarsa sai ka yi taka.

Domin amfani da kunne amfani mai inganci sai mu yi kokarin kiyaye abin da zamu ji, sai mu himmatu da jin karatun Kur'ani da hadisan Annabi (s.a.w), wasu sukan mance da cewa akwai Kur'ani a rayuwarsu. Mu kare kanmu daga jin mummuna kamar yadda muke kare kanmu daga furta mummuna, domin jin mummuna yana shiga hankali sai ya yi masa mummunan tasiri.

Mu kiyayi satar jin maganar mutane ta bayan bango da garu, da kofofi ko taga, wannan yana daga cikin ha'inci da mummunan ladabi, kuma yana cikin leken sirrin mutane da yake haram. Idan muka ji wani yana yin zancen wani to kada mu yi tarayya da shi a cikin wannan, sai dai idan ya kasance wani abu ne na maslahar al'umma da ta kama sai an yi wannan maganar, ko kuma ya kasance laifin da shi wancan mutumin yake yi a fili yake yin sa.

Kada mutum ya kasance shi ne mabudin sharri ta hanyar dauko maganganun wasu mutane yana gaya wa wasu domin haifar da fitina da Allah ya hana ta. Sannan ba ya daga cikin ladabi mutum ya yi ihu a cikin kunnen wani, ko ya hura masa kunne, ko ya doke shi a kunne, ko ya ja masa kunne, sai dai babu laifi a huda kunnen 'yan mata domin sanya kayan ado kamar dan kunne.

Mu nisanci kade-kade da jin su, domin koda ya kasance yana yi mana amfani ta wani bangaren, amma yana sanya shagaltuwa daga tunani, da bata lokaci, da kashe karfinmu, da daidaita mana tunani, da raba mana  hankali, da karanta mana lafiya ta hanyar dukan kwakwalmu da sauti daya mai maimaici da yawa yake yi, sannan wani lokaci yana sosa mana rai ta hanyoyi daban-daban, kamar sanya sha'awa, ko sanya bakin ciki, da sauransu.

Mu gode wa Allah kowace rana a kan ni'imar ji da ta gani da ya yi mana ita, wannan ni'ima ce wacce ba don ita ba da ba mu san komai ba a rayuwarmu ta duniya, da ba mu amfana daga jin makomarmu da abin da zai amfane mu a cikinta ba. Allah madaukaki yana cewa: "… Allah ne ya fito da ku daga cikin uwayenku alhalin ba ku san komai ba. Kuma ya sanya muku ji da gani da zuciya ko kwa gode".

Don haka kunne ni'imar Allah ce mai daraja, don haka ya hau kanmu kada mu yi amfani da shi wurin saba masa, sai mu yi amfani da shi wurin ji da sauraron zancen Allah mai hikima, da hadisan annabinsa masu daraja, maimakon mu rika sauraron zancen masu giba, da yana annamimanci, da hana yin alheri. Mu yi amfani da shi wurin samun ilimi, da aiki da shi, sanin duk wani abu da muka jahilta, sai sauraron wadannan abubuwan ya zama bautar Allah.

Hafiz Muhammad Sa'id

hfazah@yahoo.com

www.hikima.org

Saturday, May 14, 2011



back 1 2