Hakkin Ji



Hakkin Ji

Imam Zainul-abidin (a.s) yana cewa: "Amma hakkin ji shi ne a tsarkake shi daga giba -yi da wani-, da jin abin da bai halatta a ji ba, da tsarkake shi daga sanya shi hanyar zuwa ga zuciya, sai dai idan wata magana ce mai kima da zata farar da wani alheri a cikin zuciyarka, ko kuma zaka samu wata dabi'a mai daraja da girma da ita, domin shi ji shi ne kofar magana zuwa ga zuciya wanda yake kaiwa ga fahimtar abubuwa daban-daban na alheri da na sharri. Babu kuma karfi sai da Allah".

Mariskai su ne mafi muhimmancin hanyoyin da mutum yake samun alaka da wajensa, kuma da su ne yake iya fahimtar da waninsa abin da ya kudurce ko kuma ya san abin da waninsa ya kudurce, don haka idan aka toshe su daga mutum wannan yana nufin an toshe masa hanyoyin samuwar ilimi. Sai dai duk da haka da wannan muhimmancin da suke da shi, zamu iya ganin suna da shugaba wanda suke rusana masa gaba daya, wanda idan babu shi to zasu rasa kimarsu, wanna kuwa shi ne hankali da Allah madaukaki ya ba wa mutum.

 Imam Sadik (a.s) ya yi nuni da wannan lamarin mai muhimmanci yayin da Disani (shi wani mutum ne da bai yi imani da samuwar Ubangiji ba) ya ce masa: Nuna mini abin bautata? Sai imam Sadik (a.s) ya riki wani kwai, sai ya ce: Wannan wata katanga ce rufaffiya tana da fata mai kauri, kuma a karshita akwai wata fata siririya, kuma akwai wani ruwan azurfa karkashi siririyar fatar, da kuwa wani ruwan zinariya, sannan wannan ruwan zinariyar ba ya cakuda da ruwan azurfar, kuma waccan ba ta cakuda da wannan, wani abu bai shiga cikinta ba, kuwa babu wani abu da ya fita daga cikinta, ba a sani ba cewa namiji aka halitta ko mace, sannan sai ta tsage  ga –tsuntsu- kamar Dawisu, shin kana ganin akwai wanda ya shirya hakan?

Sai Disani ya ce: Mu ba ma imani sai da abin da muka riska da idonmu, ko ji, ko shaka, ko dandano, ko tabawa. Sai imam Sadik (a.s) ya ce masa: Ka ambaci mariskai, su kuwa ba sa amfanar komai sai  da hankali. (Sharhin Risalatul Hukuk: s; 35).

Da wannan lamarin muna iya fahimtar kimar hankali ga wadannan mariskai, domin idan sun yi kuskure sukan koma wa hankali domin su tantance, idan kuwa babu hankali to ba su da kima sai riskar abubuwa, don haka dan Adam zai kasance a cikin toshewar ilimi da rashin sanin gaskiya, da kuma kasa tantancewa.

Wannan yana iya tuna mana yadda Amru dan Ubaid ya kasance tare da Hisham, yayin da Hisham dalibin imam Sadik (a.s) ya yi masa kakat game da cewa wadannan gabobin da muke da su ba su da kima sai da hankali. Asalin wannan tattaunawar ta kasance ne yayin da Amru dan Ubaid ya yi musun wajabcin jagora ga al'umma, shi kuwa Hisham ya kawo tilascin samar da jagora ga al'umma daga Allah wanda zai daidaita al'umma idan ta karkace.

Hisham ya ce da Amru: Ina da tambaya. Sai ya ce: Kawo ta. Sai na ce: Kana da idanu? Ya ce: I. Na ce: Me kake gani da shi? Sai ya ce: Launuka da mutane. Sai na ce: Kana da hanci? Ya ce: I. Na ce: Me kake da shi? Ya ce: Ina shaka da shi. Sai ya ce: Kana da baki? Ya ce: I. Sai na ce: Me kake da shi? Sai ya ce: Ina dandana abinci. Sai ya ce: Kana da zuciya? Sai ya ce: I. Sai na ce: Me kake da ita? Sai ya ce: Ina tantance dukkan abin da ya zo wa gabobi ne don sanin gaskiya da shi. Sai na ce: Shin ba sa wadatuwa daga zuciya? Sai ya ce: I. Sai na ce: Yaya haka bayan lafiyarsu lau? Sai ya ce: Ya kai dana! Gabobi -mariskai- idan suka yi kokwanto cikin wani abu da suka shaka, ko suka gani, ko suka dandana, sai su mayar da shi zuwa ga zuciya, sai su samu yakini, sai kokwanto ya lalace. Sai ya ce: Ke nan Allah ya sanya zuciya ne domin –maganin- kokwanton gabobi? Sai ya ce: I. sai na ce: Ke nan dole ne a samu zuciya domin idan ba  haka ba gabobi ba zasu samu yakini ba? Ya ce: I.

Sai na ce: Ya kai Marwan Allah bai bar wata gaba ba sai da ya sanya mata jagora da zai gyara mai kyau, ya kore shakkun da take da shi, sannan sai ya bar halitta dukkansu cikin dimuwa, da kokwantonsu, da sabaninsu, bai sanya musu wani Imami jagora ba da zasu koma masa yayin shakkunnsu dimuwarsu, amma sai ya sanya wa gabobinka Imami makoma jagora da zasu koma masa yayin dimuwarka da kokwantonka!. (Nahajul Iman: Ibn Jubair, s 161. Amali: Saduk, s 472. Ihtijaj: Dabarasi, s 367).

Muhimmancin ji ba karamin abu ba ne, hatta da 'yan wuta suna cewa: "… da mun kasance muna ji, ko muna hankaltuwa da ba mu kasnace daga cikin 'yan Sa'ira ba". (Mulk: ). Sai suka yi furuci da cewa rashin kiyaye ji shi ne ya kai su wuta, domin sun mika jin su ga dukkan shirme da sabon Allah, sai suka mika shi ga masu bautar wani Allah, suka cika musu kwakwalensu da shirka da bautar waninsa.

Da sun saurari manzanni da annabawan Allah madaukaki, da ba su fada cikin wannan halakar ba, amma sai suka ki, suka toshe kunnuwansu, suka ki saurara. Wannan lamarin kamar yadda ya faru a lokacin da Annabi (s.a.w) yake kira, da can kafinsa ya faru ga mutanen Annabi Nuhu (a.s) yayin da yake kiran su zuwa ga Allah (s.w.t), amma sai su sanya tufafinsu su rufe kunnuwansu, su yi girman kai ga barin jin sa.



1 2 next