Hankali da Jahilci



Hankali da Jahilci

Hankali da Jahilci wasu rundunoyi biyu masu harin juna da gaba mai tsanani tsakaninsu, domin duk sa'adda aka samu wani abu to babu mai yarda wani ya dauka shi kadai, kuma babu mai yarda a raba, kowanne yana son ya mallaka shi kadai ne. Don haka ne idan mutum ya samu kansa a karkashin harin wadannan abubuwa biyu babu makawa ne ya zabi daya domin ba sa haduwa wuri daya, kuma filin yaki da dauki-ba-daninsu shi ne jikin mutum, kowannen daga cikin yana son ba shi umarni ne sabanin dayan.

Da dayan zai ce dauki haram dayan zai hana, haka nan kallon haram, ko taba haram, ko jin haram, ko cin haram, ko karbar haram, duk suna karkashin umarnin rundunar jahilci ne da hanin rundunar hankali, kamar yadda jin halal, da aikata halal, da karbar halal, da ganin halal suke karkashin hanin rundunar jahilci da umarnin rundunar hankali.

Amma kafin mu ga yadda za a warware wannan rigimar ta yadda za a samu rundunar hankali su yi galaba kan rundunar jahilci cikin sauki ba tare da daga jijiyar wuya ba, zamu so kawo wasu daga cikin misalan wadannan rundunoni biyu domin mu san su tukun.

Zamu yi kokarin kawo misalai game da wannan mummunar runduna mai karya garkuwar tsaron rayukan mutane, mai jan su zuwa ga azabar Allah da fushinsa. Ita wannan rundunar tana da bangarori biyu, na farko ya shafi hukuncin shari'a, na biyu kuwa ya shafi kyawawan halaye.

 Sannan zamu fara kawo Rundunar Jahilci sannan Rundunar Hankali ne domin sai an yi wanka an wanke dauda an shafa mai, sannan sai a yi ado da kaya masu kyau a sanya musu turare. Haka nan ne yake game da wadannan lamurran biyu, sai an cire munanan halaye an cizge su daga zuciya da ayyukan jiki, sannan ne idan aka yi kyawawa sai su zauna daram cikin ado. Amma mutumin da yake warin dauda, ya yi bududu da kura, fuskarsa ta dusashe, ga gumi ya jike jikinsa warin dauda yana tashi, sai kuma ya sanya tufafi masu kyau a kan wannan daudar, to haka ne misalin wanda yake yin kyawawan ayyuka amma kuma bai bar munana ba, don haka muka fara kawo su kafin mu kawo kyawawan ayyuka.

Allah madaukaki yana cewa: "Ka ce ku zo in karanta muku abin da Ubangijinku ya haramta muku"[1]. Kamar yadda ya lizimci musulmi ya nemi sanin wajibai haka nan ya lizimta masa neman sanin haram da kuma nisantar su, kuma mu a nan zamu kawo galibin abubuwan da aka haramta a fikihu ne musamman wadanda ana iya cin karo da su kamar haka:

Taimakawa ga yin sabo, Taimakon azzalumi, Nutsuwa da fushin Allah, Musun mu'ujiza, Musun ranar sakamako da tayar da jikin mutane ko wani daga asasin addini ko na mazhaba, Musun larurin addini, Kawar da kai daga ambaton Allah, Izgili ga muminai, Yin Barna, Dagewa kan kananan sabo, Sanya zoben zinare ga namiji, Jawo mani kamar da hannunsa ko da na wani amma idan ta hannun matarsa ne to ba komai, Cutar da muminai, Kauce wa hukuncin shari'a, Amfani da kwanon zinare da azurfa koda don ado ne, Wulakanta musulmi, Yada sirrin wanda bai yarda a yada ba, Yada sirrin juna tsakanin miji da mata, Rashin biyayyar mace ga mijinta cikin abin da yake wajibi ne ta bi shi, Rashin biyyar 'ya'ya ga iyayensu, Wasa da kayan caca tare da sanya kudi, Bayyana sabo, Yada alfahasha, Ci a Ramadan ko ranar azumin wajibi ba tare da wani uzuri na shari'a ba, Boye kaya, Rashin nisantar bawali da najasosi, Rashin yarda da Allah a cikin kaddararsa, Umarni da mummuna, Cutar da makwabta, Karbar lada a kan wajibi ayyananne, Karkata zuwa ga azzalumai, Jefa kai cikin halaka, Jingina yaro ga wanda ba babansa ba, Fitar mace ba tare da izinin mijinta ba, Sumbuntar namiji ko mace ga bare, Sumbuntar mutum waninsa don sha'awa sai dai miji da matarsa kawai ko baiwarsa, Bidi'a cikin addini, Mutum ya auri 'yarsa ko duk matar da take haramun gareshi, Mummunan zato da gini kansa, Yin Kage, Bayan gida tare da ba wa alkibla baya ko gaba, Girman kai ga barin bautar Allah, Adon namiji da zinare, Duban taurari, Girman kai, Barin salla wajiba, Barin kowane irin wajibi, Jinkirta hajji daga shekarar da ya samu iko, Karyata wani abu na Kur'ani ko hukuncin shari'a, Yin Barna, Jinkirta salla har lokacinta ya fita, Kai hukunci gun azzalumi ba larura, Halartar wajen shaye-shaye, Mace ta yi ado ga namiji bare, Hore mala'ika ko rohani ko aljani da sauransu, Sanya bacci na maganadisu, Boye aibin kaya da algus, Jinkirta rama Ramadan har wani Ramadan din, Barin umarni da kyakkyawa da hani da mummuna, Barin ladabtar da yara da zai kai ga fasadi, Haramta halal, Halatta haram, Leken aibobin mutane, Tsoratar da mumini, Barin takiyya wajen da yake dole, Kamantuwa da kafirai, Ji wa wani ciwo ko dukansa ko zaginsa ko yanke masa wata gaba, Rashin amsa sallama, Hukunci ba da abin da Allah ya saukar ba, Tsare hakkin Allah, Tsare hakkokin mutane, Tsare wani babu wani hakki, Sanya tufafin alhariri ga namiji babu wani uzuri na shari'a, Hassada da kuma aiki da ita, Tozarta hakkin mutane, Kiyaye littattafan bata da jaridu ko mujallu na bata da sayar da su da sayansu da koyar da su da koyonsu da yada su, Cin dukiyar maraya, Shan abu mai sanya maye, Cin mushe, Cin naman alade, Cin naman dabbar da aka haramta, Cin naman dabbar da ba a ambaci sunan Allah ba wajen yanka ta ko ta rasa wani sharadi na yanka, Cin tabo ko sauran abubuwan da aka haramta, Yin Ha'inci, Kayan kide-kide da muzik, kamar sayar da su da sayen su da kuma ajiye su da amfani da su, Yin Yaudara, Neman auren mace mai miji ko kuma mai idda, Cin maniyyin tumaki, Cin sauran abubuwan da aka haramta a jikin dabba, Sayar da karen kwararo ko alade da sayansu, Yakar shugaba adali, Cin najasa ko abu mai najasa da shan su, Karya ga Allah da manzonsa da Imamai (a.s), Buga ganga ko garaya da molo da ihu tare da maganganun banza da suka saba wa shari'a, Yin Sata, Yada barna, Kashe gaskiya.

Sannan akwai wasu abubuwan da aka haramta su a matsayin halaye munana da suka zo a ilimin fikihu da zamu kawo wasu daga ciki kamar haka:

Daudanci da hada zina tsakanin mutum biyu, Yin Karya, Shiga kungiyoyin bata, Shiga addinan bata, Kiyayya da mumini, Son makiya addini, Zagi musamman ga Allah da Annabi da Imami da addini da Kur’ani da mazhaba da sauran abubuwa masu tsarki, Taba littafin Kur'ani babu tsarki, Mai baki biyu; ya yabi mutum idan ba ya nan kuma ya zage shi, Karbar rashawa da cin hanci domin boye gaskiya da bayyanar da karya, Karbar rashawa da bayar da ita cikin al'amuran hukunci sai da larura, Karbar riba da bayar da ita da rubuta sheda a kanta da zama tsakatsaki a kai, Zama kasar da mutum ba zai iya kare addininsa ba ko gusar da alamomin musulunci, Zuwa kasar da zata cutar da addinin mutum, Yin Fashi, Aske gemun wani ba da yardarsa ba, Yin Rawa musamman mace gaban mazaje ajnabiyyai, Shiga cikin cacar ful, Tafiya makarantun da zai kai ga fasadi, Tafiya bandaki da wurin wanka na iyo da makarantu da wuraren da ake cakudar da ba ta dace ba tsakanin maza da mata, Raddi ga Allah da manzonsa da imamai da marja'ai da suke kan tafarkinsu cikin hukuncin shari'a, Yarda da sabo, Jifan wani da zina, Yin Annamimanci, Sauraron annamimanci, Zuwa sinimar da ake nuna fasadi da barna, Kokarin rusa masallatai, Taimako ga azzalumai koda dan aike ne, Amfani da kayan kida da caca da kuros da sauransu, Waka da fadin karya a ciki, Toshe titi da hanyar musulmi, Aibata mumini da wulakanta shi da zarginsa, Karanta girman zunubi da zai kai ga jinkirta tuba, Fitar mata ba tsari da kuma cire lullubi, Shirka da Allah mai girma, Yada alfasha, Saba wa karya, Warware alkawri, Yin Shedar zur, Sharadi da sanya kudi na tsere sai dai abin da aka fada a littafin fikihu a babin tsere da harbi, Yin Rufa ido, Yin Munafunci, Ba wa azzalumi da 'yan bidi'a uzuri da kaunarsu, Tozarta wanda ake ciyarwa, Wasa da tattabaru da tsuntsaye da sauransu na daga abubuwan da sukan kai ga haram kamar sanya kudi, Zalunci da ta'addanci, Yin Zihari, Saba wa iyaye, Aikin tsafi da kuma abin da zai raba miji da mata ko kuma abin da yake sanya son wani ba tare da sonsa ba, Cin dukiyoyin mutane da barna, Jiji da kai a ibada, Yin Algus, Wakar bata da sauraronta, Canja wasiyya, Fushi da yakan kai ga haramun, Giba wato rada da sauraronta, Fasadi a bayan kasa, Yin Fitina, Fasikanci da fajirci, Sayar da littafi madaukaki, Sayar da makami ga kafirin yaki, Kiyafa wato danganta mutane da iyayensu ta hanyar kallon kafafunsu ko jikinsu da canke, Caca da kayan shadaranji idan an sanya kudi, Yanke salla wajiba, Rantsuwa bisa karya, Tone kabari, Yanke zumunci, Jingina 'ya'ya ga Allah, Yin Bokanci, Bayar da fatawa ba da ilimi ba, Fada da tafarkin Allah, Kisa ba da hakki ba, Auren mace da aka haramta da nasaba ko shayarwa ko surukuta, Aurar namiji da aka haramta aurarsa, Kin zuwa jihadi domin kare kai da addini yayin da aka kawo masa hari, Gudu daga filin daga, Yin Kafirci, Kasuwanci da abin da aka haramta sayarwa, Tauye mudu da awo, Boye sheda, Boye gaskiya, Wake da siffanta mace mai kamewa ko yaro a ciki, Zambon mumini a waka, Bude al'aura ga wanda ya haramta ya gani, Yin Luwadi, Wasannin banza na holewa, Taba jikin ajnabi ko ajnabiyya (mace ko namiji bare), Taba mace ko namiji da sha'awa ba ta hanyar halal ba, Amfani da kayan maye kamar sha, da saye, da sayarwa, da dasa su ko shuka su, da aikinsu, da cin kudinsu, da kai wa wani, da kuma hayar kanti ko abin hawa ko wani abu daban don sayarwa, da kuma sauran amfani kamar yin magani da su idan ba da larura ba, Saba wa bakance, Aikata abubuwan da aka haramta wa mai harama da aikin hajji, Zuwa wajen bokaye da 'yan bori da 'yan camfi da masu halarto da rauhanai da aljanu da sauransu, Mata su shafi juna da sha'awa, Maza su shafi juna da sha'awa, Hana zakka ko humusi ko sauran hakkoki na wajibi, Jinkirta hakkoki, Yin Hannu da ajnabiyya babu kyalle a tsakanin hannayensu, Jayayya da Allah da manzonsa da Imami bisa shisshigi, Saba wa Allah da manzonsa da imamai (a.s), Keta umarnin Annabi (s.a.w), Shisshigi da wuce gona da iri musamman ga Allah, Leken gidajen makwabta, Zama a kan teburin da ake shan giya, Hana aikata kyakkyawa, Shiga ayyukan azzalumai, Keta alfarmar Ka'aba da wurare masu tsarki, Yanke kauna daga rahamar Allah, Ruku'u da sujada ga wanin Allah, Rantsuwa da barranta daga Allah da manzonsa ko Imami ko addinin musulunci, Kai wa zuwa ga mulki ba ta hanyar shari'a ba, Azabtar da mutane don su fadi wani abu da ake bincike.

Muna iya ganin wasu abubuwan da muka fada kafirci ne yin su wasu kuma shirka ne, wasu kuma manyan zunubai ne, wasu kuma akwai kaffara a kansu wasu kuwa akwai haddi ga yinsu kamar yadda aka yi bayani dalla-dalla a littattafai.



1 2 next