Kabilancin Shi'anci



3- Mustashriki Polhuzan ya ce:

Amma batun cewa ra’ayin Iraniyawa sun yi daidai da na Shi'a wani abu ne da babu kokwanto a cikinsa, amma kasancewar wadannan ra’ayoyin na Shi'a sun zo ne daga Iraniyawan to wannan wani abu ne wanda babu wani dalili da yake iya tabbatar da shi, kai ruwayoyin tarihi ma suna tabbatar da akasin hakan yayin da suke cewa sai da Shi’anci ya kafu tun farko a kasashen Larabawa sannan sai daga baya ya cirata zuwa ga Mawali.

4- Mustashriki Adam Mitz ya ce:

Manzhabar Shi'a ba kamar yadda wasu suka yi imani ba ne cewa wani abu ne na daukar fansa daga Iraniyawa domin saba wa musulunci, Jazirar Larabawa ta kasance Shi'a ce dukkaninta banda manyan birane kamar Makka da Tahama da San’a’a. Kuma Shi'a sun yi galaba a wasu garuruwan kamar Amman da Hajar da Sa’ada da kuma wasu birane na Khuzistan wacce take karkashin Iraki ta yadda rabin mutanenta sun kasance Shi'a ne, amma Iran ta kasance Sunna ce banda Kum kawai, kuma mutanen Ispahan sun kasacne sun yi shisshigi wajen son Mu’awiya har ma wasu suka yi imani da cewa shi annabi ne mursali.

5- Mustashriki Jolad Tasiher ya ce:

Yana daga cikin kuskure a ce asalin Shi’anci da yaduwarsa ta kasance sakamakon tunanin Iraniyawa ne game da musulunci bayan sun rike shi kuma sun mika wuya ga jagorancinsa ta hanyar yaki ne. Wannan ra’ayi mummuna ya faru ne sakamkon abubuwan tarihi da aka yi musu mummunar fahimta, motsin nan na harkar alawiyyawa ya fara ne a kasar Larabawa tsantsa.

6- Mustashriki Noladkeh ya ce:

Kasashen Farisa sun kasance wani yanki ne mai girma da suke bin mazhabar sunnanci, kuma wannan ya ci gaba har zuwa shekara ta 1500 miladiyya yayin da aka shelanta mazhabin Shi’anci a matsayin mazhaba ta kasa da tsayuwar kafuwar daular safawiyya.

Bayan duk wannan maganganu da muka cirato daga marubuta wadanda suke tabbatar da larabcin Shi’anci a gaba dayansa, kuma a lokacin da wannan ba ya kore kasancewarsa ya samu karbuwa wajen wasu al’ummum, sauran al’ummu suna da kima da girma, kuma mu ba mu kasance muna da wani take a musulunci ba sai a fadin nan nasa madaukaki: "Ya ku mutane hakika mu mun halicce ku daga namiji da mace kuma muka sanya ku jama’u da kabilu don ku san juna, hakika mafi girmanku a wajen Allah shi ne mafi tsoronku (gareshi). Hujurat: 13.

Amma sai ga shi muna fuskantar wasu maganganu da suka shaharantar da mazhabin Shi’anci suna masu jingina shi da Farisanci, daga karshen magana muna iya gabatar da wani bayani game da mutanen da mazhabin Shi’anci ya tsayu kan alkalumansu da matsayinsu, bayan nan sai mu sanya kuma wasu bayanai da suke nuni ga kasancewarsa asalinsa Larabci ne da kuma bayanin asalin wasu mazhabobin daban.

Daga Littafin Sheikh Wa'ili Na HAKIKANIN SHI'ANCI

Tarjamar: Hafiz Muhammad Sa'id da Munir Muhammad Sa'id



back 1 2 3 4