Kabilancin Shi'anci



Kuma tunda kasancewar Shi'a daga Hijaz suke to yarensu shi ne Larabci kamar yadda zamu ga shi’ar Ali (a.s) suke, kamar yadda ya bayyana daga bayanan da suka gaba ta na masu fasahar Larabawa kuma gwarazan iya bayani.

Kuma wannan fice da Shi'a suka yi wajen iya bayani sun same shi ne daga imaminsu Ali (a.s) shugaban masu bayani, har sai da suka yi fintinkau a cikin wannan kuma masu tarihi suka kirga su cikin kwararru na fasaha: Daga cikinsu akwai; Udayyi dan Hatimudda’i, da Hashimul Mirkal, da Khalid dan Sa'id Al’abshami Umawi, da Walid dan Jabiri dan Zalim Ad’da’i da wasunsu.

Kuma kasancewar yaren Larabci shi ne yaren Kur'ani mai girma to Shi'a sun kasance masu tsanantawa wajen ganin sun yi rubutu da Larabci a matsayinsa na luggar ibada kuma lugar kulla a aure, kuma ba su taba yin sakaci ba a cikin wannan, kuma babu wani yare da suka dauke shi a makwafin Larabci, a kan wannan kuma ana iya ganin wannan al’amarin ta hanyar ganin cewa a wajensu lugga ba kawai wani abu ba ne da yake ma’ana zalla kawai ba, domin da haka ne, to da wani yare ya tsaya a makwafinta, sai dai ita wani abu ne da yake da al’adunsa da dabi’unsa na asli daban wadanda suka bubbogo daga sako, don haka ne ma Kur'ani mai girma ya sauka da Larabcin.

Kuma muna iya ganin tarayyar malaman Shi'a sun tafi a kan rashin halaccin karatu a salla ko kiran salla ko kuma kabbarar harama sai da Larabci, yayin da zamu ga Abuhanifa kai tsaye ya tafi a kan cewa ya halatta a yi kiran salla ba da Larabci ba, haka nan ma Shafi'iyya da Malikiyya suna ganin ya halatta a yi kiran salla ba da Larabci ba idan mai kiran ya kasance ba’ajame, ko kuma zai yi kiran salla ga kansa ne, ko kuma zai yi wata jama’a irinsa ne.

Kuma muna iya ganin Shafi'iyya da Hanifawa da Malikiyya sun tafi a kan halaccin yin kabbarar harama ba da Larabci ba, idan ya kasance ba zai iya yin Larabci ba, kuma mai Fikihu ala Mazahibil Arba’a ya kawo wannan a babin sharuddan kabbarar harama a juzu’i na farko. Ban dai samu wasu madogara ba da kaina game da wannan wanda yake cewa suna da sharadi a kan yin kulla aure da Larabci yayin da Shi'a suka tafi a kan cewa ba zai yiwu ba sai da Larabci bisa zabi, kuma idan aka yi maganar kulla aure to Hanifawa da Malikawa da Hambalawa suna tafi a kan zai yiwu ba da Larabci ba tare da mutum yana da iko a kan hakan, kuma suna ganin ingancin wannan kullin.

3- Larabcin Halifa

Daga cikin abin da ya shafi al’amarin lugga don gane da muhimmancin Larabci a matsayin shari’a yana iya bayyana cewa Allah ya zabi wannan yare ne domin ya kasance mai dauke da tunanin musulunci, kuma Ubangiji madaukaki ya girmama wannan luga a littafinsa yayin da yake fada a aya ta biyu ta surar Yusuf: "Haka nan muka saukar da shi Kur’ani Larabci ko kwa hankalta" kuma yana fada a wata aya ta talatin da bakwai a surar Ra’adi "Haka nan muka saukar da hukunci larabaci" al’amarin da masu fassarar Kur'ani suka hadu a kan cewa Kur'ani hikima ce ta Larabci kuma muhawararsa tana tsare ne a bisa irin ta muhawarar Larabawa da usulubinsu, idan ka ga dama ka ce; ya dauki al'adar Larabawa da dukkan wata wayewa ta ci gabansu yayin da ya zabi lugarsu -yarensu- kuma amma bai kebanta da su ba domin sakon musulunci na duniya ne, sai dai Allah ya sanya yaren Larabci shi ne hanyar da yake ciratar da addini madaidaici zuwa ga mutane ta hanyarsa.

Don kiyaye wannan al’amari na sako sai da yawa daga jama’ar kungiyoyin musulmi suka tafi a kan cewa dole ne halifa ya kasance balarabe. Ba wai don wani dalili da ake iya fahimtar kabilanci daga wannan sakon na sama ba wanda ya tsarkaka daga hakan, sai dai jama’ar musulmi sun kasu gida biyu ne kan hakan: Kuma tayiwu mu ce Shi'a sun karfafi kasancewar halifa ya kasance balarabe saboda fadin nan na Annabi (s.a.w) "Jagorori (shugabanni) daga kuraishawa ne". Yayin da muka ga da yawa daga musulmi wadanda ba Shi'a ba sun tafi a kan rashin la’akari da wannan sharadin. Kuma wannan yana iya farawa tun daga kan halifa na biyu yayin da ya ce:

Da dayan mutanen nan biyu ya riske ni da na sanya al’amarin jagoranci a hannunsa: Salim maulan Abu Huzaifa, da Abu Ubaida Aljarrah, da Salim ya kasance a raye da ban sanya ta shura ba.



back 1 2 3 4 next