Farisancin Shi'anci



Buhari ya karbo daga ummul muminin A’isha cewa Annabi (s.a.w) ya zauna kwanaki kaza yana ganin kamar ya zo wa iyalansa amma bai zo musu ba, har dai ya ce: Ya ke A’isha Allah ya yi mini bayanin wani abu da nake tambayarsa da wasu mutane suka zo min daya ya zauna gun kaina dayan kuma gun kafafuna, sai wanda yake gun kafafuna ya ce da dayan, me ya samu mutumin ne? sai ya ce; an yi masa sihiri, sai ya ce: Waye ya yi masa? Sai ya ce; Lubaid dan A’asam… har dai sammun da aka yi masa ya tafi bayan tsawon lokaci.

Wato; wannan ruwaya tana nuna cewa Annabi ya rasa hankalinsa ba ya iya gane lokacin da ake yi masa wahayi har tsawon lokaci, idan kuwa ya halatta Annabi ya samu irin wannan rashin lafiyar to yaya kuwa za a aminta da wahayi, kuma ko yaya dai wannan nauyi yana kan mai ruwaya da Buhari, kuma littafin Buhari yana kunshe da irin wannan nau’i na akidun isra'iliyanci kamar dai na abin da ya ambata a babin neman izini, a babin yin farawa da sallama, ya ce:

Da sanadinsa daga Abuhuraira daga Annabi (s.a.w) Allah ya halicci Adam (a.s) a bisa kamarsa ne, tsayinsa zira’i sittin yayin da ya halicce shi sai ya ce masa tafi ka yi wa wadancan jama’ar na mala’iku da suke zaune ka ji yaya zasu gasihe da kai domin ita ce gaisuwarka da kai da zuriyarka, sai ya ce: Asslamu alaikum. Sai suka ce: Assalamu alaika wa rahmatul-Lah, sai suka kara wa rahmatul-Lah. Don haka dukkan wanda zai shiga aljanna yana kasancewa kamar girman Annabi Adam (a.s) ne, kuma halittu ba su gushe ba suna raguwa har yanzu.

Da sauran dai ruwayoyi irin wadannan wadanda suke da yanayi na nisanta daga musulunci saboda jingina wa Allah jiki, amma duk da haka ba mu samu mai jifan wadannan tunani da cewa fita ne daga musulunci ba ko kuma yahudanci ne, duk da cirato wannan da suka yi daga isra’iliyanci zuwa musulunci, amma da mutum zai yi Shi’anci nan da nan sai a ga shi’ancinsa yahudanci ne ko nasaranci, kuma duk wani mummuna da shara sai a watsa ta kansa tare da cewa duk wani laifi da wani ya yi yana kansa ne, kuma mun riga mun nuna cewa duk wani abu da ya kore musulunci to Shi’anci yana kin sa gaba daya.

Idan ma mun kaddara cewa akwai wasu fikirori da farisawan da suka zama Shi'a suka cirato suka taho da su tare da su, kamar fadin cewa akwai hakkin Allah kamar yadda Farisawa suke fada wa game da sarakunansu kuma Shi'a suka fadinsa ga imamansu duk da kuwa akwai bambanci tsakanin wadannan abubuwan biyu, to duk wannan ba zai zama aibi ba ga akida matukar ta samu asasi da asalinta ne da ta dogare da shi daga musulunci kuma wannan la’amari ne da yake sananne gun Shi'a da suke kiyaye su, ta yadda idan dai ka ga sun yi riko da wani abu to musulunci ne.

Kuma mu muna sane da cewa dukkan asasai da suke iyakance musuluncin musulmi to su ne dai abin da Annabi (s.a.w) da kansa ya iyakanta su da kansa kamar yadda ya zo a sahihul Buhari daga Anas cewa manzon Allah (s.a.w) ya ce: Duk wanda ya yi sallarmu, ya fuskanci alkiblarmu, kuma ya ci yankanmu, to wannan shi ne muslumi, kuma alkawarin Allah da manzonsa sun hau kansa, don haka kada ku keta wa Allah alkawarinsa.

Kamar yadda Buhari ya fitar da wannan daga Ali (a.s) cewa ya tambayi Annabi (s.a.w) ranar yakin Haibar cewa a kan me zan yaki mutane? Sai manzon Allah (s.a.w) ya ce: Ka yake su har sai sun shaida babu wani abin bauta sai Allah kuma hakika Muhammad manzon Allah ne, idan suka yi haka to sun kare jininksu daga gareka.

Imam Ja’afar Sadik dan Muhammad (a.s) yana cewa: Musulunci shi ne shaidawa babu wani abin bauta sai Allah da gaskatawa da manzon Allah kuma da wannan ne ake kare jini kuma a kansa ne ake yin auratayya da gado". Don haka a bisa zahirin haka ake siffantuwa da musulunci kuma wannan suna yana tabbata ga wanda ya yi kalmar shahada kuma koda bai yi imani da Imamanci da cewa nassi ne daga Allah ba, da kuma cewa hkki ne na Allah, koda kuwa yana ganin imamanci yana tabbata da shura kuma hakki ne na mutane da suke sanya shi inda suka so!

Kai ko da bai yi imani da cewa Imamanci nassi ne ba, kuma ko da ya wuce hakan malaman musulunci ba sa kafirta shi, kuma da yawa daga malamai sun tafi a kan cewa ba a kafirta ko fasikantar da musulmi saboda wani abu da ya kudurce ko ya aikata, kuma dukkan wanda ya yi ijtihadi kan wani sai ya bi abin da yake ganin gaskiya ne, to za a ba shi lada guda biyu idan ya dace, idan kuwa ya yi kuskure zai samu lada daya, kuma wannan shi ne fadin Ibn Abi-laili da Abuhanifa da Shafi'i da Sufyanus sauri da Dawud dan Ali kuma shi ne fadin da yawan sahabbai.

An ruwaito daga Ahmad dan Zahr Sarakhsi, kuma yana daga sahabban Abul Hasan al’ash’ari, kuma a gidansa ne al’ash’ari ya rasu ya ce: Ash’ari ya umarce ni da in tara masa sahabansa sai na tara su sannan sai ya ce: Ku shaida mini cewa ni ba na kafirta wani daga ma’abota alkibla don wani sabo da ya yi domin ni na ga dukkansu suna nuni ne zuwa ga abin bauta daya, kuma musulunci yana hada su yana game su.



back 1 2 3 4 5 next