Farisancin Shi'anci



Rufewa

a- Idan wannan ne ake nufi da Farisancin Shi’anci to sai wannan ya shafi dukkan musulunci ne domin kuwa dukkan mafi yawan wadanda suka yi rubutu game da musulunci musamman a zamanin farko na musulmi wanda suka kunshi abin da a yau ake ganinsa akidarsa wanda ya faru sakamakon shigowar al’ummu zuwa ga musulunci wadanda suke dauke da tunani da akidu mabanbanta jama’a-jama’a kuma ba su yarda wannan akidun nasu ba da al’adunsu mafi yawa wadanda suka hada da Rumawa da Farisawa da mutanen kasar Sin, da Ibrawa, kai har da ma wasu jama’a daga Yahudawa da wadanda dukkaninsu sun bayar da gudummuwa mai tasiri cikin ci gaban al’adun musulunci a fagage daban-daban. Kuma wannan ya faru ne ta hanyar tafsirin addini da kissoshin addini, domin su ma ma’abota Littafi ne, kuma a cikinsu akwai malamai masu dauke da hukuncin Attaura da kissoshin al’ummu da suka kiyaye na Ibrawa da labaru da kissoshi, kuma a wancan lokacin yankin Larabawa ya kasance yana kishirwar tunanin addini da abin da ya kunsa wanda al'adar Yahudawa ta taka babbar rawa a cikinsa domin cike wasu gurabu musamman a sunnanci wanda yake neman cire wannan riga domin ya yafa wa Shi'a ita, ta hannun tatsuniyar da aka kirkiro ta Abdullah dan Saba, sai dai bincike ya nuna abin da suka yafa wa Shi’anci su ne suke da shi.

Ra’ayoyin Yahudawa sun shigo musulunci ne ta hanya Ka’abul Ahbar da Wahabu dan Munabbah, da Abdullah dan Salam, da wasunsu, kuma suka samu wajen zama a littattafan tafsirai da hadisai da tarihi, kuma ta bar kufanta a cikin hukuncin shari’a. Kuma duk mai bincike yana iya bincikawa zai ga wannan da yawa a littattafai kamar "Tarihin Dabari", da tafsirinsa "Jami’ul Bayan", da littafin "Buhari" da sauran littattafai kamar yadda zamu kawo nan gaba, kuma zaka samu wannan dalla-dalla kamar yaki da gabar mutum da macijiya da Dabari ya kawo a tafsirinsa da sanadinsa daga Wahab dan Munabbah, da kuma tafsirin nan na aya ta talatin da shida a surar Bakara a fadinsa madaukaki: "Muka ce ku sauka daga gareta sashenku makiya ne ga sashe…". Tabari yana cewa: Ina ganin wannan ne ya sanya yaki tsakaninmu da macizai, asalinsa kamar yadda malamanmu suka ambata a ruwayarmu daga garesu na shigar da Iblis aljanna ne da macijiya ta yi. Ya ci gaba da kawo wannan labari mai ban mamaki yana cewa a tafsirinsa game da bayanin ragon da aka yanka fansa da Ibrahim ya yi ga dansa Isma’il da umarnin Allah (s.a.w) da cewa ragon nan da Ibrahim ya yanka shi ne wanda dan Annabi Adam (a.s) ya gabatar ba a karba daga gareshi ba.

Yana kawo labaru masu mamaki a tarihinsa mai nuna cewa akwai yahudanci ciki, kamar yadda ya kawo yana mai cewa: Ishak (a.s) ya auri wata mata sai ta samu cikin yara biyu a cikin daya, lokacin da ta so ta haife su, sai yaran suka yi gaba, sai Yakub (a.s) ya so ya fita kafin Isu, sai Isu ya ce: Wallahi idan ka fita gabanina, to sai na fasa cikin mahaifiyarmu na fita kuma sai na kashe ta, to sai Yakub (a.s) ya yi baya Isu kuma ya fita kafinsa, sannan sai Yakub (a.s) ya fita. Don haka sai aka kira Isu da sunansa da yake nufin wanda ya saba, shi kuma Yakub (a.s) da sunansa da yake nufin wanda ya jinkirta, domin ya jinkirta bayan Isu. Sai yaran suka girma, kuma Isu ya fi soyuwa wajen babansu, shi kuma Yakub (a.s) ya fi soyuwa wajen babarsu, kuma Isu yana yin farauta ne. yayin da Ishak ya makance sai ya ce da Isu ka ciyar da ni naman farautarka ka kuma kusance ni domin in yi maka addu’a, Isu ya kasance yana da yawan gashi, Yakub (a.s) kuma ba shi da yawan gashi. Sai Isu ya fita yin farauta, sai mahaifiyar Yakub (a.s) ta ce da shi ka yanka rago ka gasa sannan ka sanya rigarsa ka kawo wa babanka domin ya yi maka addu’a, da ya zo sai babansu ya shafa shi sai ya ce: Waye? Sai ya ce: Isu. Sai ya ce: Jiki irin na Isu amma gashi irin na Yakub (a.s), sai babarsa ta ce: Shi ne danka Isu, sai ka yi masa addu’a… har zuwa karshen kissa.

Ban sani ba, yaya Ishak (a.s) ya kasance bai san muryar â€کya’yansa ba! Kuma yaya babarsa zata nemi albarka daga addu’ar Ishak tana mai yin karya, yaya kuma â€کya’yanta zasu yi karya, kuma wane Annabi ne wannan da gidansa yake irin wannan gidan, sannan kuma wane irin bayar da ma’anar sunaye ne aka yi wa wadannan â€کya’ya da aka cirato daga asalin wadannan kalmomin.

Amma a littafin Buhari kana iya ganin isra’iliyanci a wasu ruwayoyinsa, duba ka ga wasu misalai daga wadannan ruwayoyi domin ka gani a fili:

Buhari da sanadinsa daga Abuhuraira yana cewa: Babu wani Annabi sai shedan ya shfe shi lokacin da za a haife shi sai ya fado yana mai kuka banda Maryam da danta. Ban sani ba idan wannan falala ce, to don me aka hana annabinmu alhalin shi ne; shugaban annabawa, kuma idan ba matsayi ba ne to mene ne amfanin kawo shi, kuma mene ne laifin sauran annabawa da shedan zai shafe su.

Buhari ya kawo da sandinsa zuwa ga A’isha uwar muminai cewa an yi wa Annabi (s.a.w) sihiri har sai da ya kasance yana ganin kamar ya yi wani abu, amma bai yi shi ba.

Kuma Buhari ya ruwaito a kissar Musa (a.s) yayin da mala’ikan mutuwa ya zo domin ya karbi ransa sai ya mare shi a kan idanuwansa sai ya cire daya… har sai da Allah ya ce da mala’ikan mutuwa koma zuwa gareshi ka ce masa ya dora hannunsa a kan fatarsa, yana da yawan shekarun da tafinsa ya rufe na adadin yawan gashi.

A bisa hakika wannan al’amarin yana da mamaki, domin gashin da hannun tafinsa zai rufe zai iya kaiwa zuwa dubu biyar, kuma shekarun annabin Allah Musa sanannu ne, imma dai wanan ruwaya ta kasance karya, imma kuma mu karyata tarihi.



back 1 2 3 4 5 next