Zuciya da Tunani



2. A ina zuciya take a jikin dan Adam;

Idan dai kana nufin irin wacce ilimin likitanci yake bincike kanta kai ma ka sani tana a kirji bangaren da ya fi karkata da hagu, wanda na san ba wannan ne kake nufi ba.

Amma idan kana maganar wacce ilimin sani, ko ilimin tsarkake ruhi da halaye, ko kuma ilimin irfani da Falsafa da sauransu suke magana ne kanta. Ko kuma yayin da mutane suke cewa wane zuciyarsa tana da kyau ko ba ta da kyau, ko yana da zuciya, da makamantan wannan. To kowane ilimi da akwai abin da yake nufi da ita.

A irfani wani mataki ne na kamalar samuwar dan Adam, a ilimin halaye ita ce samuwar mutum ta fuskanci hankalinsa mai riskar ayyukan mutum, (sai dai duk da ba jiki ba ne, amma yana da alaka da wannan zuciya ta jiki, wato tasarrufin wancan bangaren na ruhin mutum ta fuskacin abin da ake kira zuciya, kai tsaye yana tasarrufi da jiki ta fuskacin zuciyarsa ne ta jikinsa). Amma a Falsafa ita samuwar mutum ce ta fuskancin hankalinsa mai riskar tunaninsa, kuma ba kasafai suke amfani da wannan kalma ta zuciya ba.

Mutane kuwa idan suka ce yana da zuciya, suna nuni ne da daya daga halayensa na ruhinsa ta fuskacin ayyukansa kamar yadda yake a ilimin halayen dan Adam na tunani ko hankali wanda yake iya riskar ayyukan mutane da siffoffin ayyukan ta fuskancin kyau ko muni. Don haka sai su kira mai fushi yana da zuciya, ko mai dogaro da kansa ba ya wulakanta ta da cewa yana da zuciyar nema. Sai dai a nan zuciya da ma'ana ta farko wani bangare ne na samuwar ruhin mutum, amma da ma'ana ta biyu siffa ce ta ayyukan mutane.

A irin wadannan wurare duka kalmar zuciya ba ta da mahalli, domin ba jiki ba ce a irin wadannan wuraren.

 Amma tambayar cewa:

3. Mece ce alakar wadannan abubuwa da muka fada a sama

Wadannan abubuwa suna da alaka da juna, sai dai a yi mini uzurin rashin lokacin da zamu iya bayaninsu a kowane ilimi, domin su bangarori ne a ilimin kyawawan halaye. Amma a ilimin Falsafa ko Irfani abu guda ne da sunaye iri-iri, wanda ya danganta da ta wace fuska ce aka kale shi.

Amma zan amsa ne kawai ta mahangar Ilimin Irfani da na kyawawana halaye; Don haka ne idan mun kalli samuwar mutum ta ruhinsa ba ta jikinsa ba, ta fuskacin tsarkakar ruhi da cewa bangare ne mai riskar ayyuka da siffofinsu, kuma yake juya ilahirin tasarrufin ayyukan mutum sai a kira shi da kalmar Zuciya; (mind): ط§ظ„ظ‚ظ„ط¨. Kuma yana da bangarori biyu masu muhimmanci matuka da ake kira bangaren sha'awa da na fushi. Amma sha'awa a nan da fushi ba da ma'anar da bahaushe yake nufi ba don a gane, don karin bayani a koma wa makalar da muka yi nuni da ita.

Amma idan aka duba wannan samuwar ta ruhin dan Adam ta fuskacin inda yake suranta abu a kwakwalwarsa, wato mahallin da yake amfani da shi yana sawwala abubuwa daban-daban, yana hada su yana fitar da sakamako, sai a kira shi da: Kwakwalwa; (Brain): ط§ظ„ط°ظ‡ظ†.

Idan kuma aka duba bangaren ruhin mutum wanda ya fi kowanne muhimmanci, wanda hatta da zuciyarsa idan ba ta yi biyayya gareshi ba zata halaka sai a kira shi da Hankali;  (Sense): ط§ظ„ط¹ظ‚ظ„. Wato shi ne jagora gaba daya wanda yake saman 1.tunani kan ayyukan mutum, da kuma 2.tunani na warwara (analysis) kan abubuwan da yake fuskanta na ilimi. Duk wadannan bangarori biyu masu muhimmanci suna koma wa gareshi ne. Idan na farko bai bi shi ba, to mutum zai halaka da son rai, da sabo, da fadawa ayyukan nadama, idan kuma na biyu bai bi shi ba, to mutum zai halaka a akida ne, da rasa ilimi, da samun jahilci, da sauransu.

Don haka ne wanda ya bi shi a na farko sai ya zama yana da kyawawan halaye amma jahili ne tun da bai bi shi a bangare na biyu ba, kamar yawancin mutanen duniya da suke jahiltar mafi yawan tunani sahihi amma suna da kokarin kiyaye halayensu don su zama na gari. Wanda kuwa ya bi shi a bangare na biyu amma bai bi shi a bangare na farko ba, sai ya zama yana da ilimi sai dai yana da munanan halaye, kamar shedan ne da mafi yawan masana da malamai da suka kauce wa hanya ne.

Amma idan muka kalli wannan ruhin mutum ta fuskacin cewa akwai abubuwan da ake sawwalawa a tunani, kuma ana hada su a jimla domin samar da natijoji, wadannan abubuwan sawwalawa a kwakwalwa da surorinsu sai a kira su da; Tunani; ط§ظ„ظپع©ط±.

Hafiz Muhammad

hfazah@yahoo.com

www.hikima.org

Nobember 2010



back 1 2 3