Zuciya da Tunani



A nan muna son yin nuni da ma'anar wasu kalmomi da ake amfani da su, don amsar tambayar malam Sa'adu Sulaiman. Sai dai bayanai ne a taqaice saboda rashin samun damar tsawaita bayanansu:

1. (i). Zuciya; (mind) Larabawa suna cewa: al-Kalb ط§ظ„ظ‚ظ„ط¨

Zuciya: Wani bangare ne na samuwar mutum idan an yi la'akari da yadda yake yin ayyukansa, kamar gaskiya ko karya, kuma shi ne bangaren da masu Ilimin Irfani suke nufin narkewa cikin zatin Allah madaukaki da ma'anarta mai zurfi. (Wannan ma'anar babu mai gane ta sai wanda ya sha ma'anonin Irfani). Shi ne mahallin da yake shi ne dakin Allah kuma mazaunarsa da aka fi sani zuciyar bayi da ita kadai ce ta yalwaci Allah yayin da sama da kasa ba su yalwace shi, sai dai shi ne ya yalwace su. (Mataki ne da ba nan ne mahallin bahasinsa ba don yana da tsayi da wuyar bayani).

Kuma Zuciya shi ne bangaren da Ilimin Kyawawan halaye suke maganarsa idan suka ce a tsarkake kai daga daudar miyagun halaye, a siffantu da kyawawan halaye. Shi wani bangare ne da yake riska kuma yake fahimtar mai kyau da mummuna ta fuskacin tunani ko hankalin da ya shafi riskar ayyukan mutane. Don haka ne mafi girman abu a wannan bangaren zamu ga ya shafi tsarkake kai daga daudar laifin abin ya shafi mutane a daidaikunsu kamar yin karya, da siffantuwa da adon rai kamar yin gaskiya. Ko kuma abin da ya shafi mutane kamar kyawun adalci da yin kyauta da siffantuwa da su, da munin zalunci da yin rowa da nisantarsu.

Zuciya a nan ta fita daga ma'anar da likita yake nufi da zuciya, domin shi yana nufin wannan zuciya mai buga jini wacce take da alaka da jiki, amma maganar mu a nan tana shafar bangaren rai ne ba jiki ba. Domin duk abin da jiki yake da shi, to rai tana da shi, kuma suna da alaka tsakanin na rai da na jikin. Wannan duk a takaice ke nan.

 (ii). Kwakwalwa; (Brain) Larabawa suna cewa: ط§ظ„ط°ظ‡ظ†

Kwakwalwa: Shi ne bangaren samuwar mutum da ya shafi inda (wuri) yadda yake suranta abu, da inda yake hada wadannan surorin, da inda yake fitar da sakamakon abin da ya samu na tunani. Kamar dai ya suranta (riskar ko fahimtar) ma'anar daya, da kuma ma'anar uku, da hada su, da samun natija. (1+3=4).

Ilimin Mantik (logic & mathematic), su ne uwa uba (masu amfani da wannan mahallin da ake kira kwakwalwa) a wannan bahasin, don haka ne wanda ya fi kowa saurin ganewa shi ne mutane suke cewa da shi yana da kwakwalwa, ko hazaka ko kaifin fahimta, ko saurin fahimta, da sauran kalmomi da ake amfani da su, ga wanda ya fi kowa kyakkyawan amfanuwa daga wannan mahallin da muke kira kwakwalwa.

A nan ma kwakwalwa ta saba da wacce likita yake nufi, domin shi yana nufin ta jiki ce, ba ta rai (ruhi) ba, mu kuma muna magana game da ta ruhi ce, sai dai tana da wata alka da ta jiki (da nan ba mahallin wannan bahasi mai fadi ban e). Kwakwalwa a nan ba ta bahasin likitanci ba ce.



1 2 3 next