Halayen Manzon Allah (s.a.w)



Wadannan wasu bayanai ne muhimmai game da halayen manzon Allah Muhammad dan Abdullah (a.s) da rayuwarsa. Manzon Allah (s.a.w) da iyalan gidansa wadanda ya bar mana su a matsayin makoma da idan mun yi riko da su ba zamu taba bata ba har abada su ne ya dace ga dukkan musulmi ya rike su alkibla makoma da zai dogara da ita har abada, kuma su ne jirgin annabi Nuhu (a.s), kofar tuba, haskakan shiriya.

Domin samun tsira dole ne mutum ya kasance yana da akida sahihiya, da biyayya ga umarnin Allah da manzonsa da suke kunshe cikin littafin Allah da sunnar manzonsa, da kuma bibiyar kyawawan halaye manzon rahama Muhamamd dan Abdullah (s.a.w) da wasiyyansa tsarkaka da suka kama tun daga Imam Ali har zuwa Imam Mahadi (a.s). Don haka babu wani wanda ya fi dacewa a yi nuni da halayensa don a yi koyi da shi sai wannan gida da Allah bai yi kamarsa ba.

Ya zo a babin ci da shan manzon Allah (s.a.w) cewa: "Manzon Allah (s.a.w) ya kasance yana cin dukkan nau'o'in abinci, tare da iyalansa da masu yi masa hidima, kuma yana ci tare da wadanda ya kira su na musulmi a kasa, kuma a kan abin da suka ci da kuma daga abin da suka ci, sai dai idan bako ya zo masa to sai ya ci tare da bakonsa".

Ba mu taba samun wani mutum mai kamala a tarihi kamar manzon rahama (s.a.w) ba, irin daukakar da yake da ita wurin Allah da babu wani mahaluki da ya taka sawunsa balle ma ya hango kurarsa, amma sai ga shi ba mu samu wani wanda ya kai shi kaskan da kai ga mutane ba.

Wani abin da yake nuna mana haka a fili shi ne abubuwan da suka zo a cikin babin cinsa da shansa, akan siffanta shi da cewa yana cin dukkan nau'in abin ci ba tare da ya aibata wani daga abin ci ba, domin dukkaninsu ni'imomin Allah ne da ya bayar da su ga bayinsa domin su gode masa, wannan siffa ta gode wa ni'imomin Allah ta bayyana cikin ayyukansa da zantuttukansa hatta ga abin ci ko sha.

Sannan yana ci tare da iyalansa da masu yi masa hidima, idan muka ce mutum yana ci da iyalansa ta yiwu mutane su ga zai yiwu saboda kusancinsa da su, sai dai ba mu samu al'adun hausa suna yin haka ba, an dauka cewa mace ba ta da wani aiki sai dahuwa da kwanciya, kamar dai wata na'ura ce ta dafa abinci kawai, amma a zauna tare da ita a ci abinci wannan bai ta so ba, haka ma ba a san yin hira da ita ba.

Sai dai tayiwu a samu canji ga mutanenmu na yau sakamakon shigowar al'adu da wayewa da a yau ta fi na mutanenmu na gargajiya, da kuma wayewa da ilimi a yau da suka fi da yawa, ta yadda a yau idan ka dauki matarka kun tafi yawo babu mai ganin hakan a matsayin sabon abu.

Amma cinsa tare da masu yi masa hidima shi ne mafi girman lamarin da ya kamata mu lura da shi sosai, domin masu aikin gida kamar masu wanke-wanke, da masu cefane, da masu yi wa mutumm gadi a cikin al'ummu ba a daukar su da kima, hasali ma mutane sukan iya yi musu tsawa, wasu ma har da duka, kuma tayiwu saboda wani abu ne kankani da suka manta da shi ko suka gafala ba su yi ba.

Sai dai manzon rahama mafi kamalar dan Adam yana daukarsu a matsayin mutane kamar kowa, don haka yana cin abinci tare da su ba tare da wani kyama ba, kuma yana fifita su a kansa, domin su ji cewa su ma al'umma ce mai daraja kuma mutane ne masu kima a cikin al'umma.

Bai taba zagi ko duka ko daka tsawa ga dayansu ba, har ma ya kasance ana cewa yakan ce da su da an yi abu kaza da shi ya fi, tsira da amincin Allah su tabbata gareshi, sai Allah ya siffanta shi da cewa shi ne mafi daukakar bayi a kyawawan halaye. Tawali'unsa ya kai ga balaraben kauye yakan shigo birni sai ya zo majalisin annabi (s.a.w) amma sai ya tambaya ya ce: "Waye Muhammad a cikinku?.



1 2 3 4 5 6 7 8 9 next