Jagoranci



 Son Ahlul Bait (A.S.)

Allah Ta'ala Yana cewa: "Ka ce ni bana rokon ku wani Lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai. surar Shura: 23.

Mun yi imani cewa bayan wajabcin riko ga Ahlul Bait (A.S) wajibi ne a kan kowane musulmi ya yi Addini da soyayya gare su da kaunarsu domin a wannan ayar Allah ya kayyade abinda ake rokon mutane da su yi shi da soyayya ga Dangi Makusata.

Ya zo ta hanyoyi daban daban da dama daga Ananbi (S.A.W) cewa soyayya gare su alamar imani ne kuma kiyayya gare su alamar munafunci ne, da kuma cewa wanda ya so su ya so Allah da ManzonSa wanda kuma ya ki so to ya ki Allah  da Manzonsa (S.A.W). Hasali ma soyayya gare su farilla ne da wajibin Addinin Musulunci wadda ba zai yuwu a yi jayyayya ko shakka a kai ba, dukkkan musulmi sun hadu a kai duk da sabanin da suke da shi kuwa tsakaninsu a tafarki na da ra’ayoyi, in banda wata jama’a kalilan da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah wadanda suka yi watsi da su da suna “Nawasiba” wato wadanda suka kulla gaba a kan Zuriyara Gidan Muhammadu (S.A.W), don haka  ne ma ake kidaya su a cikn masu karyata wajiban Addinin Musulunci tabbatattu mai karyata wajiban Addini a zukata ana kidaya shi ne a hukuncin wadanda suka karyata ainihin Addinin Musuluncin. kai ya karyata sakon koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada.

      Wannna shi ne abinda ya sa kiyayya ga Zuriyar Muhammad (S.A.W) ta za ma daga cikin alamun munafunci soyayya gare su kuma daga alamun imani. saboda haka ne kuma har wayau kiyayya gare su ta zama kiyayya ga Allah (S.W.T) da Manzonsa kuma babu shakka Allah (S.W.T) bai farlanta soyayya gare su ba sai don sun cancanci soyayya da biyayya ta bamgaren kusancin su ga Allah da Manzonsa da tsarkinsu da nisantar su ga sabo da shirka, ba zai taba yuwuwa ba a sunnanta cewa Ubangiji ya wajabta son wanda ke aikata sabo ko kuma wanda ba ya bin sa yadda ya kamata domin shi ba shi da wata kusantaka da abota tare da kowa. mutane a gurinsa ba kome ba ne illa bayi halitta matsayi guda suke. kawai mafifici a cikinsu a gurin Allah  shi ne mafi tsoron Allah daga cikinsu. Duk wanda ya wajabta son su a kan mutane baki daya to babu makawa ya zamanto mafificinsu a takawa kuma mafi darajarsu baki daya, idan da ba don haka ba kuwa to da waninsa ya fi cancantar haka, ko kuma da kenan Allah ya fifita wani sashe a kan wani a wajabcin soyayya da biyayya haka nan siddan sarmadan ba tare da cancanta ko karama ba.

Imamai (A.S.)

Ba mu yi imani game da Imamai (A.S.) irin yadda 'Yan gullatu masu wuce iyaka suka yi ba haka nan ba mu yi irin yadda 'Yan Hululiyya suka yi ba, "Kalmar da ke fita daga bakunansu ta girmama." (Surar Kahf 5).

Mu Imaninmu a kebe shi ne cewa su mutane ne kamar mu suna da abinda muke da shi kuma abinda yake kanmu yana kansu sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa Allah ya kebance su da karamarsa kuma Ya so su da soyayyarsa, domin sun kasance a kan daraja mafi kamala mafi dacewa ga mutum na daga ilimi, da takawa, da jarumta da karimci, da kamewa, da dai dukan kyawawan dabi'u mafifita na da kyawawan sifofi, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abinda aka kebance su da shi.

Da wannan ne kuma suka cancanci su zamo Imaman shiriya da kuma duk abinda yake ya shafi bayanin shari'a da kuma abinda ya kebanci shari'a da kuma abinda ya kebanta da Alkur'ani na daga tafsiri da bayani.

Imam Sadik (A.S.) Ya ce:



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next