Jagoranci



"Kuma babu wata al'umma face mai gargadi Ya zamanto a cikinta." Surar Fatir: 24.

Ismar Imamai

Mun yi Imani da cewa Imami ma tamkar Annabi wajibi ne Ya zama katangagge daga duka munanan ayyuka da alfasha, na zahiri da na badini, daga yarinta har zuwa mutuwa, da mantuwa ko da ganganci, haka nan wajibi ne ya zama katangagge daga kuskure da mantuwa da rafkanuwa domin Imamai masu kare shari'a, masu tsayuwa a kanta, halinsu tamkar halin Annabi ne. Dalilin kuwa da ya hukunta mana imani da ismar Annabawa haka nan shi ne dalilin da ya hukunta mana imani da ismar Imami ba tare da wani bambanci ba, kuma ba gagararre ba ne ga Allah (S.W.T) Ya tare talikai duk cikin abu daya duk jimillah (wannan yana nufin ba abinda ya gagari Allah ) 

Siffofin Imami

Mun yi imani cewa imami tamkar Annabi shi ma ya wajaba ya zamanto mafificin mutane a siffofin kamala, kamarsu jaruntaka, da karimci, da kame kai, da gaskiya, da adalci, da tafi da al'amura, da hikima da kuma kyawun hali, dalilinmu na wannan siffofi da Annabi ya siffantu da su shi ne dalilanmu game da Imami a game siffantuwarsa da su.

Dangane da Iliminsa, kuwa, shi yana samun saninsa da hukunce-hukuncen Ubangiji da dukan masaniyar sa ne ta gurin Annabi ko kuma Imamin da ya gabace shi, Idan kuwa aka sami wani sabon abu to babu makawa ya san shi ta hanyar ilhami daga karfin kwakwalwa da Allah Ya cusa masa, idan ya mai da hankalinsa a kan wani al'amari yana so ya san hakikaninsa to ba ya kuskure kuma ba ya rikirkicewa kuma ba ya bukatar hujjoji na hankali a kan haka kuma ba ya bukatar fahintarwar Malamai koda yake ilimin nasa na iya karuwa ya kara inganta, wannan shi ne abinda ya sa Annabi (S.A.W) a addu'arsa yake cewa:

 "Ubangiji ka kara mini ilimi."

Kamar yadda yake a fadar Ubangiji "Ka ce Ya Ubangiji Ka kara mini ilimi." Surar Taha: 114.

Na ce: Ya tabbata a ilimin sanin halayyar dan Adam cewa kowa yana da wata sa'a ayyananniya ko ma awowi da yakan san wani abu shi da kansa ta hanyar kaifin fahinta wanda shi a kan kansa reshe ne na ilhami, saboda abinda Allah  Ya sanya masa na karfin yin haka, wannan kudurar ta sha bamban wajen tsanani da raunana, da karuwa da kuma raguwa a dan Adam gwargwadon sabanin daidaikunsu, sai tunanin mutum ya kai ga sani a wancan lokacin ba tare da bukatar ya tsaya ya yi tunani ko kuma tsara mukaddima da hujjoji ba ko kuma koyawar malamai ba, kuma sau da yawa mutum kan sami irin haka sau da yawa a kan kansa a rayuwa, Idan kuwa al'amarin haka yake to ya halatta ga mutum ya kai ga madaukakan darajojin kamala a karfin tunaninsa na sanin ilhami. Wannan kuwa abu ne da masana falsafa na da da na yanzu suka tabbatar da shi.

Don haka muke cewa: Shi a kan kansa Karfin ilhami a gurin Imami da ake kira "kuwwa kudsiyya" Ya kai ga mafi kololuwar darajar kamala, don haka yana da tsarkakar ruhi da ke daidai da karbar sannai a kowane kokaci ta kowane hali, don haka duk lokacin da ya mai da hankali ga wani abu daga abubuwa yana bukatar ya san shi sai ya san shi da wannan kudurar ta "Kuwwa Kudsiya" ta Ilhami ba tare da jinkirtawa ba ko shirya wasu mukaddimomi ko kuma koyo daga bakin malami, haka abinda yake son sanin zai bayyana gare shi kamar yadda abubuwa ke bayyana a tsafta tacce madubi, babu wani dindimi ko rikitarwa game da abinda ya so saninsa.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next