Imamanci



Imamai (A.S.)

Ba mu yi imani game da Imamai (A.S.) irin yadda 'Yan gullatu masu wuce iyaka suka yi ba haka nan ba mu yi irin yadda 'Yan Hululiyya suka yi ba, "Kalmar da ke fita daga bakunansu ta girmama." (Surar Kahf 5).

Mu Imaninmu a kebe shi ne cewa su mutane ne kamar mu suna da abinda muke da shi kuma abinda yake kanmu yana kansu sai dai kawai su bayin Allah ne ababan girmamawa Allah ya kebance su da karamarsa kuma Ya so su da soyayyarsa, domin sun kasance a kan daraja mafi kamala mafi dacewa ga mutum na daga ilimi, da takawa, da jarumta da karimci, da kamewa, da dai dukan kyawawan dabi'u mafifita na da kyawawan sifofi, kuma babu wani dan Adam da zai yi kusa da su a kan abinda aka kebance su da shi.

Da wannan ne kuma suka cancanci su zamo Imaman shiriya da kuma duk abinda yake ya shafi bayanin shari'a da kuma abinda ya kebanci shari'a da kuma abinda ya kebanta da Alkur'ani na daga tafsiri da bayani.

Imam Sadik (A.S.) Ya ce:

"Duk abinda ya zo muku daga gare mu wanda bai halatta ya zamanto daga halittu ba kuma ba ku san shi ba ba ku fahimce shi ba to kada ku musa shi ku mayar da shi gare mu, kuma abinda ya zo muku daga abinda bai halatta ya kasance daga halittu ba ku musa shi kuma kada ku mayar da shi gare mu.

Imamanci Sai da Nassi

Mun yi imani cewa lmamanci tamkar Annabci ne ba ya kasancewa sai da nassi daga Allah (S.W.T) a harshen Manzonsa ko kuma a bisa harshen lmamin da ya kasance da nassi idan har ya so ya ba da nassi game da lmamin bayansa.

Hukuncin lmamanci a kan haka tamkar hukuncin Annabci ne ba tare da wani banbanci ba, mutane ba su da ikon wani hukunci a kan wanda Allah Ya ayyana shi mai shiryarwa da datarwa ga dan Adam baki daya kamar kuma yadda ba su da hakkin ayyana shi ko kuma kaddamar da shi ko zabensa, domin wanda yake da tsarki da kwazon daukar alkyabbar lmamanci baki daya da kuma shiryawa da illahirin dan Adama gaba daya bai dace ya san wani abu ba face da sanarwar Allah kuma bai kamata a ayyana shi ba face da ayyanawar Allah.

Mun yi imani cewa Annabi (S.A.W) Ya ba da nassi game da halifansa kuma lmamin talikai Aliyu Dan Abi Talib Amirul muminina (A.S) Amini kan wahayi, lmamin halittu, ya ayyana shi a gurare da dama kuma ya nada shi ya kuma karba masa bai'a a kan shugabancin Muminai Ranar Gadir Ya ce: ((A ji a fadaka duk wanda na kasance shugabansa ne to ga Aliyu shi ma shugabansa ne, Ya Allah ka so wanda ya so shi ka ki wanda ya ki shi, Ka taimaki wanda ya taimake shika tozarta wanda ya tozarta shi kuma Ka juya gaskiya tare da shi duk inda ya juya)) Daga cikin guraren farko dangane da nassi a kan lmamancinsa maganarsa Manzo yayin da ya kirayi danginsa makusata da 'Yanuwansa na kusa kuma Ya ce: "Wannan shi ne dan'uwana kuma wasiyyina kuma halifana ku bi shi" a yayin nan kuma shi yana yaro bai balaga ba. Kuma ya maimaita maganarsa sau da dama cewa: "Kai a gare ni matsayin Haruna ga Musa kake sai dai kawai babu Annabi ne bayana" Da sauran ruwayoyi da ayoyi masu girma da suke nuni da tabbatar shugabanci na gaba daya gare shi kamar ayar da ke cewa: ((Tabbatacce kawai shi ne cewa Allah ne majibincinku da Manzonsa da Wadanda suka yi imani wadanda suke ba da zakka su suna masu ruku'i)) Surar Ma'ida: 55.

wannan ta sauka ne game da shi yayin da ya ba sadakar zobensa yana cikin ruku"u. Bin diddigin dukan abinda ya zo na daga ruwayoyi da ayoyin Alkur'ani ba ya goyon bayan cewa wannan sakon kagagge ne, haka nan bayanin manufofinsu da suke nuni da su. Sa'an nan shi kuma kansa (A.S) Ya ba da nassi game da Imamancin Hasan da Husain (AS), shi kuma Husain ya ba da nassin Imamancin dansa Aliyu Zainul Abidin (AS) haka nan dai Imami ke ba da nassin Imami bayan Imami, wanda ya gabata ya ba da na mai zuwa har zuwa kan na karshensu kuma shi ne zababbensu kamar yadda zai zo.

Adadin Imamai

Mun yi imani da cewa Imamai wadanda suke da siffar Imamancin gaskiya su ne wadanda muke komawa gare su a hukunce-hukuncen shari'a wadanda aka ba da nassi game da Imamancinsu su goma sha biyu ne, Annabi (S.A.W) ya ba da nassi a kansu dukkaninsu da sunayansu, sa'an nan kuma duk wanda ya gabata daga cikinsu to ya ba da nassi a kan wanda ke biye da shi kamar haka:­



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next