Imamanci



 Don haka ya wajaba mika wuya gare su da biyayya ga umarninsu da riko da maganganunsu, Saboda haka Mu mun yi imani cewa hukunce-hukuncen Shari'ar Ubangiji ba sa samun shayarwa sai dai daga ruwansu, kuma bai halatta a karbe ta sai dai daga gurinsu, kuma nauyin da aka dora wa baligi ba ya sauka daga kansa ta hanyar komawa ga waninsu. Kuma mukallafi ba ya samun kwanciyar hankalin cewa ya ba da wajibin da aka dora masa face ta hanyarsu, Su kamar jirgin ruwan Annabi Nuhu (A.S.) suke duk wanda ya hau ya tsira wanda kuwa ya jinkirta ya bar su ya dulmuye a cikin wannan ambaliyar da ke makale da igiyoyin ruwan rikitarwa da bata da da'awowi da rikice-rikice.

A wannan zamanin bayanin tabbatar da lmamai (A.S.) a matsayin cewa su ne halifofin gaskiya a shar'ance kuma shugabanni zabin Ubangiji domin wannan al'amari ne da ya riga ya shude a tarihi kuma tabbatar da hakan ba zai sake dewo mana da zamanin da ya wuce na tarihi ba, ko kuma ya dawo musu da hakkinsu da aka kwace na tafi da hukuncin Allah na shari'a ba, da kuma samar da abinda Manzon Allah (S.A.W) kamar yadda ya zo da shi din ba.

Sai dai kuma karban hukunce-hukunce daga masu ruwaya da kuma Mujtahidan da ba sa sha daga daddadan ruwan mashayarsu to nesanta ne daga tafarkin sawaba a Addini, kuma baligi ba ya taba samun kwanciyar hankalin cewa ya saukar da abinda aka kallafa masa daga Allah, domin tare da kaddara cewa akwai sabanin ra'ayoyi a tsakanin jama'ar musulmi dangane da hukunce-hukuncen shari'a, sabani irin wanda babu mai sa ran yin daidai a kansa to kuwa babu wani abu da ya saura ga mukallafi face ya juya ga mazhabar da ya so da kuma ra'a yin da ya zaba, kai babu makawa gare shi face ya yi bincike har ya kai ga hujja tabbatacciya tsakaninsa da Allah (S.W.T) wajen ayyana mazhaba kebantacciya wadda ya hakikance cewa da ita ne zai isa ga hukunce-hukuncen Allah, kuma cewa da ita ne zai sauke wa kansa nauyi da aka farlanta, domin abinda ake da yakinin wajibcinsa babu makawa yana bukatar a samu yakinin saukar da shi.

Dalili tabbatacce da ke nuna wajabcin komawa ga Ahlul Bait (A.S) da kuma cewa su ne ainihin wadanda za a koma gare su a kan hukunce-hukunce bayan Annabi (S.A.W) akalla shi ne maganar Manzon Allah (S.A.W) "Hakika Ni na bar muku abinda idan har kuka yi riko da shi ba za ku taba bata ba har abada bayana, shi ne abubuwa biyu masu nauyi, dayansu ya fi daya girma, wato Littafin Allah igiya mikakkiya daga sama zuwa kasa da kuma Zuriyata Mutanen Gidana ku ji ku sani cewa su ba masu rabuwa da juna ba ne har su riske ni a tabki."

Wannan hadisin masu ruwaya a tafarkin Sunna da Shi'a sun hadu a kansa, don haka ka kyautata nazarin wannan hadisin da kyau za ka iske abinda zai gamsar da kai ya kuma ba ka mamaki a ma'anarsa da abinda ya kunsa, duba manufar maganar Manzo “matukar kun yi riko da shi ba kwa taba bacewa bayana har abada” tana da zurfi, kuma abinda ya bari a tsakaninmu masu nauyi guda biyu ne a tare, domin ya sanya su ne kamar abu guda daya bai wadatu da a yi riko da guda daya ba kawai daga cikinsu, saboda haka ta riko da su tare ne kawai ba za mu taba bacewa ba har abada.

Kuma ma'anar fadinsa (S.A.W) cewa: "Ba za su taba rabuwa ba har su iso gare ni a tabki" a sarari take sosai, wato wanda ya raba tsakaninsu bai yi riko da su tare ba to ba ya taba samun shiriya har abada, wannan kuma shi ne abinda ya sa suka zamanto “Jirgin ruwan tsira da Amincin Allah a bayan kasa”. Kuma duk wanda ya jinkirta ya dakata ya bar su to ya nutse a cikin guguwar bata ba kuma zai amintu daga halaka ba, fassarar wannan kuwa da soyayya gare su ne kawai ba tare da riko da maganganunsu da bin hanyarsu ba guje wa gaskiya ne, babu abinda ke kaiwa ga hakki illa ra'ayin rikau da gafala daga ingantacciyar hanya a bisa fassarar bayyanannen zancen Larabci.

 Son Ahlul Bait (A.S.)

Allah Ta'ala Yana cewa: "Ka ce ni bana rokon ku wani Lada a kansa sai dai soyayyar dangi na kusa kawai. surar Shura: 23.

Mun yi imani cewa bayan wajabcin riko ga Ahlul Bait (A.S) wajibi ne a kan kowane musulmi ya yi Addini da soyayya gare su da kaunarsu domin a wannan ayar Allah ya kayyade abinda ake rokon mutane da su yi shi da soyayya ga Dangi Makusata.

Ya zo ta hanyoyi daban daban da dama daga Ananbi (S.A.W) cewa soyayya gare su alamar imani ne kuma kiyayya gare su alamar munafunci ne, da kuma cewa wanda ya so su ya so Allah da ManzonSa wanda kuma ya ki so to ya ki Allah  da Manzonsa (S.A.W). Hasali ma soyayya gare su farilla ne da wajibin Addinin Musulunci wadda ba zai yuwu a yi jayyayya ko shakka a kai ba, dukkkan musulmi sun hadu a kai duk da sabanin da suke da shi kuwa tsakaninsu a tafarki na da ra’ayoyi, in banda wata jama’a kalilan da aka dauke su a matsayin masu gaba da Zuriyar Manzon Allah wadanda suka yi watsi da su da suna “Nawasiba” wato wadanda suka kulla gaba a kan Zuriyara Gidan Muhammadu (S.A.W), don haka  ne ma ake kidaya su a cikn masu karyata wajiban Addinin Musulunci tabbatattu mai karyata wajiban Addini a zukata ana kidaya shi ne a hukuncin wadanda suka karyata ainihin Addinin Musuluncin. kai ya karyata sakon koda kuwa a zahiri ya yi furuci da kalmar shahada.

      Wannna shi ne abinda ya sa kiyayya ga Zuriyar Muhammad (S.A.W) ta za ma daga cikin alamun munafunci soyayya gare su kuma daga alamun imani. saboda haka ne kuma har wayau kiyayya gare su ta zama kiyayya ga Allah (S.W.T) da Manzonsa kuma babu shakka Allah (S.W.T) bai farlanta soyayya gare su ba sai don sun cancanci soyayya da biyayya ta bamgaren kusancin su ga Allah da Manzonsa da tsarkinsu da nisantar su ga sabo da shirka, ba zai taba yuwuwa ba a sunnanta cewa Ubangiji ya wajabta son wanda ke aikata sabo ko kuma wanda ba ya bin sa yadda ya kamata domin shi ba shi da wata kusantaka da abota tare da kowa. mutane a gurinsa ba kome ba ne illa bayi halitta matsayi guda suke. kawai mafifici a cikinsu a gurin Allah  shi ne mafi tsoron Allah daga cikinsu. Duk wanda ya wajabta son su a kan mutane baki daya to babu makawa ya zamanto mafificinsu a takawa kuma mafi darajarsu baki daya, idan da ba don haka ba kuwa to da waninsa ya fi cancantar haka, ko kuma da kenan Allah ya fifita wani sashe a kan wani a wajabcin soyayya da biyayya haka nan siddan sarmadan ba tare da cancanta ko karama ba.



back 1 2 3 4 5 6 7 8 9 10 11 12 next