Iyali Da Yalwa



Karin bayani kan hakan muna iya ganin wannan ruwayar tana nuna mana abin da muka kawo a fili a fadinsa ma’aiki (s.a.w): manzon Allah (s.a.w) yana cewa: “Babu wani abu da ya fi soyuwa wurin Allah madaukaki a musulunci fiye da gidan da ake raya shi da aure, kuma babu wani abu da ya fi kiyuwa gun Allah madaukaki a musulunci fiye da gidan da yake rushewa saboda saki” (Kafi: j 5/ babin Hassi alan nikah/ 328/ h 1).

Sannan wanda yake ganin cewa; bari in yi ta sako ‘ya’ya in watsar da su, ba tare da ya yi kokarin ganin kawo adadin da yake jin zasu dace da yanayinsa ba, ya yi kuskure mai girma. Domin musulunci bai bar wani abu ba sai da ya yi bayaninsa, sannan Imam Ali (a.s) wanda da takobinsa ne musulunci ya tsayu, kuma shi ne kofar birnin ilimin Annabi (s.a.w) ya yi nuni da sabanin hakan yayin da yake cewa: "Karancin Iyali dayan Yalwa ne guda biyu, Soyayyar (mutane) rabin hankali ne, Bakin ciki rabin tsufa ne". Nahajul Balaga: Hikima: 135.

A nan a fili yake cewa Imam (a.s) yana nuni da cewa wanda ya fi karancin iyali nauyin da yake kansa zai fi raguwa, kuma wannan yana nufin zai fi samun yalwar iya tattalinsu da kula da su fiye da wanda ya tara su birjik. Sai dai mu gane cewa wannan lamari yana da alaka da yanayin mutane da bambancinsu ta fuskacin iko da yalawa, ta yadda wani yana iya kula da 2, wani kuwa 5, wani kuwa 12, da makamantansu. Don haka zamu iya fahimtar cewa Allah madaukaki ya dora lamurran wannan duniyar bisa sabubba ne, ba ya yin wani abu bisa wasa, ba ya wani aiki babu hikima, Allah Ka girmama mai hikima!.

 

Cibiyar Al’adun Musulunci

www.hikima.org

Hafiz Muhammad Sa’id

hfazah@yahoo.com

Wednesday, April 07, 2010



back 1 2 3 4