Iyali Da Yalwa



Da farko dai kalmar “Ku yi auratayya kwa hayayyafa” tana nuna mana aure ana yin sa ne tsakanin mutum biyu, ba ya kasancewa sai da yarda bangaren namiji da mace, don haka sai ya zo da kalmar tarayya da aikin da yake daga bangarori biyu a larbci تناكحوا ku yi auratayya, koda yake ana iya cewa yana nufin ku yi aure wato ku biyu kenan miji da mata.

Don haka sharadi ne sai idan mace ta yarda aure ya yi, wannan ne ya sanya zamu ga musulunci ya sanya auren tilas ba aure ba ne.

Sannan a wannan ruwayar babu wani abu da yake nuna ana nufin a auri mata da yawa, amma kakan ji wasu a gefen titi, hatta da wasu masu da’awar ilimi ya yi mata da yawa yana mai kafa hujja da wannan ruwaya.

Kamar dai yana son ya ce; ba wani abu ake nufi da wannan ruwaya ba, sai a yi ta yin auren mata da yawa ana kawo ‘ya’ya barkatai koda kuwa babu wani abu da zai iya na daukar nauyin rayuwarsu!. Sannan mun riga mun yi nuni can baya da cewa ba yadda zamu yi zaune mu yi tsammanin Allah ya kawo mana canji haka kawai ba tare da mun tabuka komai ba, da hujjar cewa Allah yana nan!.

Sannan fadinsa ma’aiki “Ku yi auratayya” yin aure a nan umarni ne na mustahabbi kamar yadda malamai suka yi nuni da shi, kuma aikatau ne shudadde a ka’idar nahawun larabci wanda a Hausa yake bayar da umarni, don haka ne a hausa muke fassara shi da umarni domin ma’anarsa kenan. Amma bangaren wannan jumala mai cewa; “kwa hayayyafa”, yana nuna mana dalilin yin auren kenan. Kamar yadda zaka ce da wani mutum ne, ka yi kasuwanci ka samu riba, ko ka yi karatu ka samu ilimi.

Wanda yake nuna sai an yi wadannan ayyukan sannan ake iya samun natija wato bangaren karshe. Don haka hadisin yana nuna mana idan muna son haihuwa da hayayyafa to sai mu yi aure, amma idan ba ma son mu hayayyafa to ba zamu yi auren ba. Sai dai ma’aiki mai daraja ya kwadaitar da yin auren domin da shi ne zai yi alfahari ga sauran al’ummu.

Domin idan hayayyafa ta kasance ta tsaya cik, ko kuma idan hayayyafa ta hanyar fasadi ne kamar zina, to babu wani abu da zai yi wa sauran al’umma alfahari da shi.

Amma fakarar da take cewa: “hakika ni ina yi wa al’umma alfahari da ku ranar kiyama”, wannan fakarar tana nuna mana dalili na biyu na yin aure wanda yake nuna cewa; idan kuka yi aure kuka hayayyafa to zan yi alfahari da ku kenan. Wannan yana nuni da cewa; idan kuwa ba ku yi aure kuka hayayyafa ba to babu wani abu da zai yi wa wasu al’umma alfahari da shi na salihan bayin al’ummata, domin samuwarku ta katse kenan.

Sannan alfahari yana yiwuwa ne idan akwai abin da za a nuna na azo-agani kamar salihan bayi da babu kamarsu a cikin wata al’umma, don haka wannan yana nuna cewa idan taci-barkatai ne wannan al’ummar take kyankyasowa take hayayyafarwa babu wani abin alheri da za a iya yin alfahari da shi!.

Sannan duk da muna da dalilai daga aya da wasu hadisai da suke nuna ‘ya’ya nagari ne ma’aikin tsira yake nufi, sai dai a wasu ruwayoyin zamu ga akwai karin da yake nuna hakan, domin fadinsa cewa: “hatta da bari -ina yi wa al’ummu alfahari da shi- domin ya zo cewa; yana tsayawa a kofar aljanna ya ki shiga sai iyayensa sun shiga. Tana nuna mana cewa zuriya ta gari ake nufi da wadanda za a yi alfahari da su, don haka sai kowa ya shirya wa kawo wadanda ya san zai iya daukar tarbiyyarsu, idan ya yi nasa sai kuma ya nemi Allah ya kama masa.



back 1 2 3 4 next