Iyali Da Yalwa



 Da sunan Allah madaukaki

Sau da yawa mutanen kasashenmu sukan yi amfani da tunaninsu da fahimtarsu wurin bayani ko fassara ma’anar wata aya ko wasu ruwayoyi da suka zo musu a tunani, sai su ba su fahimtar da suka ga dama.

Dalilin da ya sanya na kawo wannan maganar kuwa ina son yin magana kan wani hadisi da yawancin mutane suke dogaro da shi wurin ganin a yi ta auratayya ana hayayyafa, ta yadda kowane mutum yana iya kawo maka wannan magana cikin sauki kuma ya nuna abin da take nufi kai tsaye.

Wannan hadisin shi ne: “Ku yi auratayya kwa hayayyafa, hakika ni ina yi wa al’umma alfahari da ku ranar kiyama (Maslakul Afham: Shahidus Sani / j 7/ s 12). A wata ruwayar da ta zo da karin “hatta da bari” -ina yi wa al’ummu alfahari da shi, kamar yadda wasu ruwayoyin sun kawo cewa; bari ma yana da amfani domin yana tsayawa a kofar aljanna ya ki shiga sai iyayensa sun shiga-.

 Da farko dai yawancin wannan hadisin ana kawo shi ne yayin da ake maganar matsalar rayuwa da karancin abin da za a dauki nauyin iyali na tufatarwa da ilmantarwa da ciyarwa. Sai kawai ka ji an jawo wannan hadisin ba tare da sanya fahimta ba, musamman da yake akidar kaddara da ma’anar komai daga Allah ne kuma dan Adam ba shi da wani hannu a kan rayuwarsa ta yi kanta da kamari a cikin al’ummarmu, wanda yake akida ce batacciya.

Da yake bayanin kan kaddara mun riga mun yi rubutu a kansa don haka ba zamu dauki wani sabon lokaci ba a nan domin yin magana a kansa, sai dai muna iya nuni da cewa: Ubangiji madaukaki yana cewa: “Hakika Allah ba ya canja wa mutane abin da yake garesu, har sai dai sun canja abin da yake garesu...” (Anfal: ). Wannan ayar kawai ta isa ta nuna mana cewa waccan maganar ta cewa Allah na nan shi zai yi komai ba tare da shi bawa ya dauki wani mataki ba, babu wani asasi da take da shi!.

Da farko dai muna son a fahimci cewa sau da yawa hukuncin shari’a yana da nasa lokacin da yake la’akari da shi da wuri, da yanayi, don haka wannan hadisin yana kuma daya daga cikinsu musamman idan muka yi la’akari da cewa maslahar bayi ita ce gaba wurin sanya hukuncin shari’a kamar yadda masu ilimin Usulul Fikhi suka tabbatar.

Don haka ne idan muka koma wa wannan hadisin zamu ga yana magana a wani lokaci da yawan musulmi ya yi karanci matuka, kuma da bukatar su hayayyafa. Sai dai wani zai ce ba zai kasance haka ba saboda karshen hadisin yana nuni da cewa; manzon rahama yana son ya yi wa sauran al’ummu alfaharin yawan al’ummarsa ne.

Sai dai wannan maganar tana iya zama karbabbiya ne idan da babu wasu ruwayoyin da suke nuni da cewa babu wani alheri ga ‘ya’ya ashararai. Hada da ayoyi masu yawa da suke sukan bin sha’awar duniya ta tara ‘ya’ya da mata, da dukiyoyi, da so irin na sha’awa da kwanciya, ba tare da la’akari da tarbiyyarsu bisa tafarki nagari ba (Masalikul Afkari ya yi nuni a j 7, s 12).

Wannan lamarin a fili yake cewa yana nuni da irin nau’in al’ummar da manzon rahama (s.a.w) yake son al’ummarsa ta tara masa, ba yuyar da ba ta da wani amfani ba!.



1 2 3 4 next