Kimar Mutum



Duba abin da ya zo a littafin Risalatul Hukuk na Imam Zainul’abidin (a.s) (s; 7) yayin da wata baiwarsa take zuba masa ruwa yana yin alwala da buta, sai butar ta subuce ta fada fuskarsa ta ji masa ciwo, sai ya daga fuskarsa ya kalle ta. Sai ta ce masa: Allah madaukaki yana cewa: “Da masu hadiye fushi”, sai ya ce: Na hadiye fushina. Sai ta ce: “Da masu yin afuwa”. Sai ya ce: “Allah ya yi miki afuwa”. Sai ta ce: “Allah yana son masu kyautatawa”. Sai ya ce: Ke ‘ya ce saboda Allah!  (ya ‘yanta ta).

Duba yadda wannan baiwa tasa ta rotse masa fuska amma sakamakon fasa wannan fuska mai daraja shi ne ma’abocin wannan fuska madaukakiya ya ‘yanta wannan baiwa. Ina ne mutum zai iya samun irin wannan mu’amala, da wannan dabi’a mai tsananin yalwa da girmama in ba a irin wadannan cikakkun mutane masu daraja ba!.

Kamar yadda Ali bn Yusuf al-Hilli ya kawo a cikin littafin nan “Al’adadul Kawiyya/ s 155” game da wata ruwaya ta Sufyanus Sauri cewa ya shiga wurin Imam Sadik (a.s) sai ya gan shi duk launinsa ya canja, sai ya tambaye shi game da hakan, sai ya ce: “Na kasance na hana mutanen gidana hawa saman daki ne, na shiga gida sai ga wata baiwata wacce take renon wasu yarana ta hau saman tsani ga yaro tare da ita, da ta gan ni, sai ta tsorata ta dimauce, sai yaron ya fado kasa ya mutu. Sam launina bai canja ba saboda mutuwar yaron, sai dai launina ya canja ne saboda firgicin da ta samu saboda ta gan ni, sannan sai ya ce mata: Ke ‘ya ce saboda Allah, babu komai kan ki -ya fada mata haka har sau biyu-.

Idan ka duba wadannan masu daraja da yadda suka san ubangijinsu sai wannan ya sanya su sanin dan Adam da sauran halittu, sai suka kasance babu wani abu na cutarwa da yake iya faruwa daga garesu zuwa ga wani halitta, maimakon haka sai dai ma su samu cutuwa kuma su yafe.

Don haka sai suka kasance rahama ga dukkan talikai, fitilar haskakawa domin gane gaskiya daga bata, tudun tsira. Kuma manzon rahama (s.a.w) ya siffanta su da cewa su ne tudun tsira yayin da yake kamanta su da jirgin Annabi Nuhu (a.s), da kofar tubar Banu Isra’il.

A yanzu ne zamu gane cewa; domin kowane mutum ya kasance rahama ga talikai dole ne ya kasance ya san ubangijinsa, ya kiyaye kansa, da wannan ne zai kasance haske mai haskakawa duniya, fitilar da take kona kanta domin wasu su samu haske.

Yanzu zaka kwatanta wadannan masana Allah (s.w.t) da kaskantattun bayinsa wadanda ba su san komai ba sai kawukansu, ba su san Allah ba. Sannan ga cututtukan rayi sun cika su, idan kana neman mai girman kai da jiji-dakai ka same su, to ka kai magaryar tukewa. Su suna dagawa saboda kawai sun ga sun isa “Lallai mutum yana dagawa, saboda kawai yana ganin kansa ya wadatu”(Alaki: ).

Wasu mutanen babu wanda ya tsira daga sharrinsu, sannan na kasa da su yana gigicewa saboda halayensu, sannan mafi yawan al’amuran al’umma suna hannun irinsu a cikin kasashe. Akwai misalin wani ambasadan Nijeriya a wata kasa (a 2003-2007) wanda kamar yadda bai san kimar kasarsa da al’ummarsa ba. Rashin mutuncinsa ya mamaye hatta da gidansa ta yadda matarsa ta yi mummunan abin da zai ba ka mamaki ta kori mai yi mata hidimar shara da wanke-wanke domin kawai ta fasa mata tangaran, alhalin santsinsa ne ya sanya kubucewarsa daga hannunta.

Duba nisan da yake tsakanin irin wadannan mutane biyu, tsakanin kamilin mutum masanin Allah cikakken sani wanda yake jin zafin tsoratar da baiwarsa ta yi alhalin ta kashe masa da, amma ba wannan ne tunanin da yake damusa ba, sai tunanin tsoron da ya same ta sakamakon laifin da ta yi, kuma wannan ya sanya shi ‘yanta ta. Da kuma mutumin da ya dulmiye cikin kogin son duniya da tsananin jahiltar Allah madaukaki, da kallon bayi a matsayin abin biyan bukatarsa kawai ta yadda wannan kungurmin jahilin mutum wanda ya narke kan son duniya da ganin girmanta, da jahiltar Ubangijinsa da kuma rashin sanin kansa, ya dauki tangaran dinsa ya fi dan Adam kima, ta yadda duk wani wulakanci yana iya yi masa saboda tangaran dinsa!.

Wani abin da ya fi wannan rashin imani shi ne na wani mutum maras mutunci da ya taba kade wani yaro ya mutu sai iyayen yaron suka yafe, shi wannan mutumin ba ma dan Nijeriya ba ne. Amma da yake mutumin ba shi da kimar mutuntaka da dan adamtaka tare da shi ko kwarzane, sai ya rika yi musu dariya bayan ya tafi da shi da abokansa ‘yan kasarsa, yana mai cewa; ya dauka zai biya diyya ne, ashe wadannan mutanen wawaye ne, yanzu sun bar masa diyyar kyauta kenan!.



back 1 2 3 4 next