Musulmin Duniya



Malamai su bar neman duniya da hassada ga juna, su shagaltu da neman mafita ga wannan al’umma. Shugabanni su farka daga gafalarsu, su nisanci kyamar al’umma da barnar dukiyarta, su tausaya wa al’umma da idanun rahama. Mutane kuwa su so gaskiya su kawar da jahilcinsu, su nisanci kiraye-kirayen gaba da juna, da rikicin jahilci, su zauna da juna da kyawawan halaye. Idan muka kiyaye zamu samu rahamar Manzon Allah (s.a.w), in kuwa ba haka ba, duk abin da muka gani mu zargi kawukanmu.

Amincin Allah (s.w.t) ya tabbata ga wadanda suka bi shiriya!

Hafiz Muhammad

hfazah@yahoo.com

Thursday, March 11, 2010

 

 

 

 



back 1 2 3 4 5