Yara a Cikin Shari'a



11- Yi wa ‘ya’ya nasiha da wasiyya a karshen rayuwar iyaye kafin mutuwarsu: Bakara: 132[4].

12- Nuni da nauyin da aka dora wa iyaye na kare 'ya'yansu daga wuta a fadinsa madaukaki: Ya ku wadanda kuka yi imani ku kare kawukanku da iyalanku daga wuta…[5]

 13- Kamar yadda aka nuna nauyin da ya hau kan 'ya'ya game da iyayensu da abin da yake nuni da girman iyaye da nauyinsu a cikin fadinsa madaukaki: Ubangijinka ya hukunta cewa kada ku yi bauta sai gareshi, kuma ku kyautata wa iyaye…[6]

Haka nan shari'a ta yi nuni da marhalolin rayuwar yaro tun farkon fitowarsa duniya har zuwa mutuwarsa. Idan mun duba abubuwan da za a yi masa bayan haihuwarsa zamu ga an yi nuni da su kamar haka:

An yi umarnin yin kiran salla da ikama a kunnuwan yaro yayin da ya zo duniya, sai a yi kiran salla a na dama, a yi ikama a na hagu, domin yaro ya fara da jin mafi dadin kalmomi mafi tsarki wadanda su ne tushen addini kuma asasinsa da suke dauke da kadaita Allah madaukaki, kuma su ne mafi tasiri a ruhin yara wajen tarbiyya da dasa imani a zukatansu, kuma wannan shi ne mataki na farko da jagoran wannan duniya da lahira ya koyar da mabiyansa (s.a.w)[7].

Sannan kuma sai shari'a ta sake nuna yadda za horar da shi tun bayan haihuwarsa cikin wasu hikimomi da duniya ta kasa zuwa da kamarsu. Hikimomi ne daga mai gaskiyar gidan Annabi (a.s) yayin da yake nuni da wannan. Imam Sadik (a.s) ya yi nuni da cewa; shekara ta bakwai ita ce shekarar da za a fara koyawa yaro sanin tarbiyyar addini, da koyar da shi hukunce-hukuncensa, yana mai cewa: Ya zama wajibi ne a kan iyaye a shekara ta bakwai su sanar da 'ya'yansu haram.

Sannan sai aka yi nuni da matakin da yaro zai fara takawa yayin da ya fara samun tunanin abin da yake kewaye da shi na samammu, da nuni da yadda ya kamata a yi rayuwa tare da shi. Hadisin Annabi (s.a.w) mai daraja ya kawo a fadinsa: "Yaro shugaba ne a shekaru bakwai, kuma bawa ne a shekaru bakwai, kuma waziri ne a shekaru bakwai"[8].

Sai kuma shari'a ta sake nuni da cewa su wadannan yara amana ce a hannunmu, don haka Allah zai tambaye mu game da su. Wannan lamarin yana nuna mana cewa; Allah yana ganin duk abin da muke yi game da wannan ajiyar tasa, don haka zai tambaye mu shin mun kiyaye ta ko kuwa. Ma'aikin tsira da aminci (s.a.w) yana cewa: "Ku tarbiyyantar da 'ya'yanku, domin ku ababan tambaya ne game da su".

Sai dai a dukkan wannan lamarin addini ya nuna mana muhimmancin kula da 'ya mace, musulunci yana kiran ta da lada ce, domin a tarbiyyarta akwai lada mai tsananin yawa, Surar nur: 30 – 31, ta yi nuni da siffofin da ya kamata mace ta kasance a kansu na kamewa da jin kunya kamar haka: "…Su kiyaye lullubinsu da adonsu ban da abin da yake zahirinsu ne kamar fuska da tafukan hannaye, su dora abin lullubin akan wuyan su domin kada a ga kirjinsu da wuyansu, sannan kuma kada su bayyanar da adonsu sai ga mazajensu, ko kuma iyayensu, ko baban mazajensu, ko ‘ya’yansu ko ‘ya’yan mazajensu, ko ‘yan’uwansu, ko ‘ya’yan ‘yan’uwansu ko ‘ya’yan ‘yan’uwansu mata, ko kuma mata irinsu, ko bayinsu, ko kuma wawayen da ba su da bukatuwa zuwa ga mata, ko yaran da ba su san wani abu na sha’awa ba. Kuma kada su rika buga wani abu da kafafunsu wanda zai iya bayyanar da adon kafafunsu ko jawo hankulan maza zuwa garesu.

Kyautata sunan yaro yana daga cikin abubuwan da suke da muhimmanci, domin suna yana da tasiri a rayuwar mutum, kuma hakki ne kan uba ya samara masa suna mai kyau. Imam Ali (a.s) yana cewa: “Hakki ne na da a kan uba ya kyautata sunansa, ya kyautata tarbiyyarsa, ya sanar da shi Kur'ani” [9]. Wannan hadisi mai kima yana nuna mana kyautata tarbiyya da koyar da karatun Kur'ani kuma a matsayin hakkin da a kan babansa.



back 1 2 3 4 5 next