Yara a Cikin Shari'a



Da Sunan Allah Mai Raham Mai Jin Kai

Tsira da amincin Allah su tabbata ga manzon Allah (s.a.w) da alayensa tsarkaka (a.s)

Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: “Yaro a shekara bakwai na farko shugaba ne kuma sarki, a shekara bakwai kuma bawa ne ribataccen yaki, a shekara bakwai kuma dan’uwa ne kuma waziri”[1]. Wannan Hadisi yana nuna mana shekara ishirin da daya da zaka yi tare da yaro, da irin mu’amalar da zaka yi da shi a kowacce daga shekaru bakwai. Kuma zamu yi kokarin ganin mun gina wannan littafin bisa wannan asasi mai muhimmanci.

Magana kan yara wani abu ne da babu abin da ya kai shi muhimmanci a tarihin rayuwar dan Adam Saboda su ne manya a gobe, kuma idan ba a tarbiyyatar da su yadda ya kamata ba to wannan yana nufin rushewar al’adun al’umma na gari, da shafe kufan abin da ta gada kaka da kakanni. Shi ya sa ma a tarihin juyin juya halin al’ummu zamu ga yana faruwa ta hannun Yara da Samari ne, idan mun duba tarihin Annabawa (a.s) da Manzon Rahama (s.a.w) da ma juyin da ya faru a bayansu, zamu ga ya faru ne ta hannun samari.

Duba ka gani yadda mushirikan Makka suke cewa: Manzo ya zo ya bata tunanin samarinsu sabaoda samari su suke karbar canji, amma tsohon jini da ya kafu a bisa wata Akida da ta kafu a tunaninsa da ra'ayinsa, yana da wahala ya canja da sauri ko ya samu sauyi, don haka ne ma Musulunci ya bayar da muhimmaci a kan shekarun samartaka.

Malaman tarbiyya suna ganin cewa; Yana da wahala ga mutum ya canja da wuri bayan ya yi shekaru arba’in kan wani ra’ayi: Misali idan mutum ya kai shekara arba’in ba ya sallar dare to yana da wahala ya iya jurewa ya dage a kai, Shi ya sa idan saurayi ya dore a kan hanya ta gari to yana da wahala ya canja.

Amma ba mu kore cewa mutum yana iya samun canji kan abin da ya rayu ba, misali mutum yana iya rayuwa kan wani abu na gari wanda yake nuni da cewa; shi na gari ne a zahirinsa, amma idan ya zama yana da dauda a zuciya kamar hassada, ko mugun kulli kan bayin Allah, to duk wannan yana iya tasiri wajan lalacewarsa koda yana ayyuka ta bangaren ibada, a nan ba mamaki ba ne karshensa ya ki kyau. Bil’am dan Ba’ur malami ne, amma saboda ya yi wa Annabi Musa (a.s) hassada sai ya lalace, haka ma Iblis yana daga mala’iku masu ilimi na koli, amma sai ya yi hassada, shi ke nan sai ya kaskanta, darajarsa ta yi kasa.

Don haka ne ya zo a wata ruwaya cewa: "Kada ku duba yawan sallarsu, da azuminsu, da yawan hajji, da kyawawa, da kuma sautinsu da dare, ku duba gaskiyar magana da rikon amana"[2]. Wato; kada a duba yawan salla, da ruku’u, ko sujadar mutum, ta yiwu wata al’ada ce da ya saba da ita, idan ya bari sai ya ji babu dadi, amma a duba ayyukansa da mu’amalarsa, irin wadannan mutane suna sallar jam’i ko ta dare, da azumin nafila, amma ba sa tasiri a ayyukansu sakamakon lalacewar zukatansu.

Don haka; Idan yaro ya saba da wani abu haka zai taso da shi a matsayin saurayi, idan da ya saba da karatu sai ya zama saurayi to ba zai iya bari ba kuma haka zai manyanta ya tsufa matukar wani yanayi na tilas da lalura bai fado ba. Amma yaron da ya taso yana bin bata gari, yaya zai taso? Don haka ne tarbiyyar yara, da samari, da ilmantar da su domin a samu al’umma ta gari take bukatar hukuma, da iyaye, da ‘yanuwa, da makwabta, da malamai, su sanya hannu.

Manzon Allah (s.a.w) yana cewa: “Yaro a shekara bakwai na farko shugaba ne kuma sarki, a shekara bakwai kuma bawa ne ribataccen yaki, a shekara bakwai kuma dan’uwa ne kuma waziri”[3]. Wannan Hadisi yana nuna mana shekara ishirin da daya da zaka yi tare da yaro, da irin mu’amalar da zaka yi da shi a kowacce daga shekaru bakwai. Kuma zamu yi kokarin ganin mun gina wannan littafin bisa wannan asasin mai marhaloli uku masu muhimmanci a shekarun yaro.

Kur’ani mai girma ya himmantu da tarbiyyar yaro da kula da shi, don haka ne a ayoyi masu yawa ya yi magana game da ‘ya’ya da hakkokinsu, da yadda ya kamata a kalle su, da zama da su, da zamu iya kawo su a dunkule kamar haka:



1 2 3 4 5 next