Gadir Khum



Na so a ce ni ne daya daga cikin matakalar minbarin nan da ta samu albarkar hawa kanta da fadin wannan hadisi alhali kafafuwa ba daya ba, ba biyu ba, ba uku ba, kai har kafafu hudu wacce take ta Hasken Allah na farko, da kuma na biyu mai biye masa wanda yake shi ne ainihinsa su ne a kanta.

Wane ne ya isa ya yi bayanin wannan kafafu da tsayuwar su! wane ne ya isa ya yi bayanin hadisan da sirrinsu! kai balle ya je bayanin hannaye masu tsarki da girma wadanda suke kunshe da hanke mai dimautar da mai nufin sanin wannan sirri! Wallahi kwakwale sun gajiya su san wannan sirrin! Amma da falalar Ubangijin Talikai da rahamarsa ya ba wa wadannan kwakwale fahimtar sanin ma’anar Harun (a.s) da matsayinsa gun Musa (a.s), kuma ya ba su ikon fahimtar wilitaka da Jagorancin muminai, da cewa; babu mai shar'antawa sai waliyyinsa.

Yayin da na yi duba zuwa ga wannan huduba sai na ga cewa; dukkan sakon da Manzon Allah (s.a.w) ya zo da shi yana tattare ciki, muna iya cewa duk rayuwar Manzo (s.a.w) da sauron sako share fage ne ga wannan rana! shi ya sa ma "…Idan ba ka yi ba to ba ka isar da sakonsa ba…"[1]. shi ya sa a kashi na farko zamu ga ta kunshi Kadaita Allah da nuni zuwa ga cewa shar'antawa na Allah ne, yayin da ta kunshi Kadaita Allah da dukkan nau'insa kamar Kadaitakar Hukunci, da Kadaitakar Tafiyar da lamurran bayi, da Kadaitakar Bauta ga Allah, da sauransu.

Sannan domin kada Manzo (s.a.w) ya tsaya ga isar wa mutane sai ya zama shi ne farkon wanda ya yi shaida, kuma ya yi furuci da wilayar Jagorancin Ali (a.s), bayan ya yi furuci da wilayar Ali (a.s) sai ya ci gaba da kawo sababbin bayanai na shari'a, wannan kuwa duk da cewa kafin wannan lokacin ya riga ya yi shimfidarsu kuma ya dasa su tun kafin nan a cikin kwakwalen musulmi, wato an shuka su tun kafin wannan ranar sai dai ranar Gadir ranar girbi ce.

Idan ka so ka ce wannna rana ita ce ranar tafsirin asasin da Kur'ani ya kunsa, ita ce ranar taro, kuma ranar shelanta ma'anonin addini masu kima, kamar ma'anar matsayin  Harun (a.s) gun Musa (a.s), da ma'anar Wasiyyai kuma halifofi, da ma'anar Babban alkawari mai nauyi da karaminsa, sannan sai karbar BAI'A da wasiyyar bin Ali (a.s) da yi masa bai'a suka zama rufe taro.

Wani abin da ya ba ni tsoro shi ne yaya aka samu kungiya ta mafiya ta asiri, da aka samu lokacin Manzo (s.a.w)  cikin  musulmi har Ubangiji ya hana Manzo (s.a.w) ambaton sunan su, kai har ma wahayi yake cewa: "Allah ne yake kare ka daga mutanen…"[2]. Sannan ga ishara da cewa duk siffofin Manzo (s.a.w) suna dabbakuwa a kan Imam Ali (a.s) idan ka cire annabici, kuma duk siffofin muminai to shi ne gaba, sannan shiga aljanna ya doru a kan yi masa biyayya, da riko da Jagorancinsa shi da 'ya'yansa, sannan sai ya gargadi mutane game da shugabannin bata da tsoratarwa daga bin su.

A cikin maganganun hikima ya zo cewa; Wadanda suka yi riko da wilaya da jagorancin Ali (a.s) tamkar mala'iku ne da suka yi sujada ga Adam (a.s), amma wadanda suka ki bin sa kamar iblis ne da ya ki yin sujada ga Adam (a.s).

A bangare na karshe na wannan huduba an kawo bayanin wajabcin wasu hukunce-hukunce da suka shafi Salla, Zakka, Halal, Haram, Umarni da Kyakkyawa, da Hani ga Mummuna, wadanda suka lizimci abubuwa daban-daban kamar Tattalin arziki, Zamantakewar al’umma, da makamantansu.

Amma wani abu da yake an yi nuni da shi a nan shi ne; cewar dukkansu suna a matsayin mataccen jiki ne maras rai matukar babu riko da wilaya da jagorancin Ali (a.s), kai hatta da kasawa da gajiyawa a kan riko da jagorancinsa an kira shi da kafirci, haka nan an kira wuce gona da iri kan riko da jagorancinsa da shirka. "Ma fi yawancinsu ba sa imani da Allah sai suna masu shirk"[3].

Marubuci: Hafiz Muhammad Sa'id

www.hikima.org

hfazah@yahoo.com


[1] Ma'ida: 67.

[2] Ma'ida: 67.

[3] Yusuf: 106.



back 1 2