Gadir Khum



Gadir Khum a Sabon Tufafinsa na Zamani

Da Sunansa Madaukaki

Wannan bayani kan Gadir an rubuta shi sakamakon gasa da aka yi ta rubutun makala kan Gadir a makarantar Imam Khomain da take Bajak-Kum, ta kasar Iran, a shekarar1423 H. Kuma mutane 128 ne daga kasashen sama da 50 na duniya da suka hada da latin Amurka, da Amurka da Asia, da Turai, da Afrika ne suka yi rubutu kan Gadir a wannan gasar, Godiya ta tabbata ga Allah ni marubuci Hafiz Muhammad Sa’id daga Nijeriya na samu wanda ya cinye a matsayin na farko. Kuma dan Afrika na biyu abokina Abdullahi Doso dan Ivory Cost ya samu na hudu a gasar.

Bayanin duk da na rubuta shi da larabci ne kuma ya fi dadi da larabcin amma na fassara shi zuwa harshen Hausa kamar haka:

Lokacin da na karbi littafin hudubar Manzon Allah (s.a.w)  a yau litinin 22 ga watan zalhijji 1423 bayan na duba sai na ga cewa dukkan matsalar dan Adam ta duniya da kuma dukkan kamalar dan Adam yake nema ta lahira da dukkan abubuwan da suka faru ko suke faruwa ko zasu faru a tarihin rayuwar dan Adam duk sun damfaru da wannan huduba kuma warwararsu ta ta’allaka da fahimtar wannan huduba da abin da ya gudan a wannan rana mai girma ta Gadir

Ina iya cewa har a cikin zuciyata na yi imani cewa har da matasalarmu ta kashin kanmu wato ba kawai matsalar al’umma ba, warwararta tana dogara bisa imani da abin da yake kunshe cikin wannnan sako na Ubangiji da ya aiko fiyayyen mazajen Allah kuma bayinsa na gari da shi.

Da na kalli hudubar da kyau  sai na ga gabatarwarta ita ce ainihin karshenta, wato; farkonta da tsakiyarta wadanda su ne madarar sakon da ke kunshe cikinta, da kuma karshenta duka abu guda ne, domin dukkan su sun hadu domin fitar da hikimar samuwar mutum a bayan kasa, da hadafin halittarsa, da kuma abubuwan da zai kudurce a zuciyarsa domin samun tunani sahihi. Wadannan abubuwa ne da idan suka gyaru suka zama su ne suke motsa mutum a tunani da ayyukansa sai a gan shi yana motsawa zuwa ga neman kamala a aikace, sai ka ga ayyukansa sun zama irin na mutum kamili wanda shi ne darasin da waccan hudubar take dauke kuma take kunshe da shi .

Mu duba sosai da mai ganin mai basira zamu ga abin ta kunsa bayanai ne da suke su ne cikakken musabbabi na kamalar dan Adam, wannan kuwa domin suna kunshe da abin da masu Ilimin Usul suke cewa da "Almuktadhi" wato samun yiwuwar abu. Sannan da karin kuma cewa babu wani abu da zai zo ya hana samun kamala sakamakon riko da su, kai sun fi haka ma girmama da daukaka domin su bayanai ne da suke cikakkun sabubba na samun kamalar mutum kai abin ya shafi dukkan sa’adar talikai ba ma dan Adam ba kawai duk suna cikin wannan darasi mai girma na wannan huduba. Domin da an fahimci wannan huduba, aka yi imani da ita, aka kuma yi aiki da ita, da rabauta ta mamaye kowa, da ta kuma game dukkan halittu, rabautar kamalar da daya daga cikin mutane ne ya same ta a kowane zamaninsa, domin shi ne a wancan lokacin aka yi wa wahayi, don haka ake jingina kamalar rabauta gareshi, akwai kuma aljanu da sauran mutane.

Ya kaicon dan Adam! sai ga 'yan fashi a kan hanyar rabautar dan Adam sun kankame ko'ina suna masu hana sautin kira da wilaya ya isa ga dukkan kunnuwa masu sauraro! sai ga dokokin Allah sun cancanza! sai ga 'ya'yan Annabinsa ana karkashewa! sai ga waliyyi Jagoran Muminai an kawar da shi daga fagen lamurran al'umma! sai ga rukunai da bangaye na addini suna rushewa! sai ga dan'adamtaka da mutuntaka ta tafi! rashin mutunci da jahilci sun mamaye! Kimar wahayi ta fadi warwas!.

Sai ga fadin gaskiya ya zama hukuncinsa shi ne cire wuyan mafadinta da halatta dukiyarsa! kuma a kawar da dukkan wata kariya daga gareshi! Sai ga ci gaban Musulunci ya tsaya cik! sai ga shi a yamma an yi gunkin wane ana shi masa albarka cewa yana daga cikin mutanen  da suka hana Ali (a.s) sakat, in ba haka ba, da yanzu Jamus da ire-irenta ana shelanta kalmar "Ash'hadu anna muhammadar rasulullah!".

Duba ku gani daga randa Ma'aikin Allah (s.a.w) ya shelanta cewa "Duk wanda nake shugabansa to Ali  shugabansa ne". Wannan kuwa kusan shekaru  dubu da dari hudu ke nan, sai ga shi kiran wilaya ba a ji shi ba sai shekara goma sha tara da suka wuce zuwa ishirin da daya ko sama da haka, kai ko kasa da haka ma, wannan kuwa domin wasu abokai na ba su san Shi'a ko Gadir ba sai shekara biyar zuwa bakwai da suka wuce.

Alhamdulillahi! katangun da 'yan fashi suka gina a kan titi don farautar masu son wucewa zuwa Gadir da wilayar Jagoran muminai Ali (a.s) mun koyi yadda ake haura su, don ni na hango wata 'yar hanya da ta nan na wuce na kuma nuna wa wasu 'yan dubunnan mutane su ma suka haura katangar ta nan, wannan ya sanya wasu 'yan karnukan 'yan fashin da aka tarbiyyantar a kan farauta suka rika yi mun haushi har suka so kona gidajenmu, suka kwashe mana dukiya kusan shikaru shida baya da suka wuce zuwa bakwai ke nan. Amma sai muka yi musu gwalo da isgili muka ce mun dai riga mun fahimci Gadir kuma mun haura katangar, kuma koda an kashe mu to farkon digon jinina zai diga ne a matakalar minbarin manzon rahama (s.a.w) kuma dai dai kasan tafin Imam Ali (a.s)



1 2 next