Tattaunawa Ta Tara



Kun sanya shi shedan yana iya hana shi sallarsa ta dare.

Kun sanya shi yana tsere da matarsa a cikin rundunar yaki a sahara.

Kun sanya shi yana hana abu shi kuma ya yi.

Kun sanya shi yana zuwa kallon rawar 'yan matan Afurka a masallacinsa.

Kun sanya shi yana yin alwala da giyar dabino.

Kun sanya shi yana samun shagaltuwa da rafkanwa a zuciya har sai ya manta ko ya yi salla ko kuwa, ya zo matansa ko kuwa!!

Kun sanya shi ana iya yi masa tsafi ya kama shi har ya yi wata shida bai san me yake yi ba!!

Ina tambayarka don Allah da wannan munanan tubaru da ta cikinsa kake ganin Annabi (s.a.w) da kai da Shi'a waye ya yi masa jafa'in?!!.

 (Mahallin kuka) Kun sanya shi yana zo wa matansa tara a rana daya, yana zo masu suna haila, yana yin abin da bai dace ba sai ya yi bawali a tsaye, ya karbi baki yana rigingine, ya saurari waka, ya kalli rawa, ya sha Nabiz (giyar dabino)! Ya shagaltu da matarsa A'isha, ya fifita ta a kan sauran matansa, ya saurari kida da waka tare da ita, ya dora ta kan kafadarsa domin su yi kallo ta taga kumatunsa a kan nata domin kallon rawar matan Afrika, ya bar rundunarsa ta yaki ya yi tsere da ita. Kai tsarki ya tabbata ga Allah da annabinsa daga abin da suke siffantawa.

Hafiz Muhammad Sa'id

May, 1, 2009



back 1 2 3 4