Tattaunawa Ta Tara



Amma da ka ce: ((5) Matsayin Fatima da Aliyu a Addinin Shi'a

Wannan ma'aurata biyu masu girma da matsayin irin nasu wanda ya kamace su cikin Addinin Musulunci, to a addinin Shi'a sunfi karfin tinaninka domin matsayinsu ya zarce na du mahaluki har shi kansa Annabi (SAW) da mabiya Addinin Shi'a suke faman yi masa Jafa'i ga ra'ayoyin malamansu tsaya kaji,Hassan Dan isuhu ya fada a littafinsa Kashaful Yakeen fi Fada'ilu Amirur Muminina shafi na 229 cewa "Allah ya yiwa Manzon Allah "SAW" Magana a daren Mi'iraji da sautin Aliyu dan Abi Dalib")).

Sai in ce maka: Matsayin Ahlul Baiti (a.s) ya wuce na mahluki gaskiya ne, amma kuma bai kai na mahallici ba domin dukkan wannan matsayin Allah mahalicci ya ba su shi. Ban sani ba ko kana cikin "am yah sudunan nasaأ¢â‚¬آ¦" da kake yi musu hassada kamar sauran masu yi musu da suka gabata.

Amma maganar Allah ga manzo (s.a.w) da muryar Ali (a.s) ya inganta, idan kun karkata ruwayar kuka ce da muryar Abubakar ne kuma wannan bai sanya kun yi wa Annabi (s.a.w) jafa'i ba, to don me idan mabiya Ahlul Baiti (a.s) sun karbo daga garesu cewa da muryar Ali (a.s) sai Banu Umayya suka jirkita shi suka ce da muryar Abubakar ne wanda kai kwakwalwarka take cike da koyarwarsu zai kasance su ba su yi jafa'i ga Annabi (s.a.w) ba!

Da wannan ne nake ganin karancin tunaninka ya yawaita, jahilcinka ya tabbata! Yaya "ba" dinka zata yi jarra amma ta Shi'a ba ta yi! Da wane jirkitaccen hankali ne ka samu wannan kiyasin batacce!!?

Da wannan ne na san cewa matsayinsu dole ya wuce tunaninka!

Sannan da kai da Shi'a waye ya yi wa Annabi (s.a.w) jafa'i a matsayinka na mai tunani game da shi kamar haka:

Jingina masa shafar shedan sadda aka haife shi: Buhari 4, 94.

Jingina wa Annabi kurakurai da Umar dan Khaddabi ke yi masa gyara sai kuwa Allah ya goyi bayansa a kan abin da ya yi wa Annabi (s.a.w).

Daukar tawassuli da ziyarar Annabi (s.a.w) shirka.



back 1 2 3 4 next