Tattaunawa Ta Tara



Amma da kake cewa: ((Matsayin Annabi Muhd SAW a Addinin Shi'a, Wannan Annabi da suke karyar so da yadda suke yaudarar wawaye da son yayan gidansa, zaka ga abinda suke fada a kansa. Majlisi Zinkidi yana fada a littafinsa Biharur Anwar shafi na 43 cewa "Annabi `SAW' baya iya bacci har sai ya sunbaci Fatima a tsakanin nonuwanta" to kaga wannan babbar alama ce da ta nuna kuna kaunar Annabi yan Shi'a, sai yasa Jaza'iri ya fada a Anwarunnu'umaniyyah Mujalladi na daya shafi na 17 "Aliyu yafi Annabi Muhd Jarumta koda yace shi Annabi Muhd dama can ba jarumi bane tun asali" to don haka karku ga na kafe akan ra'ayi na na cewa Shi'a ba Musulunci bace addini ce mai zaman kansa ku zarje ni ina da hujja)).

Sai in ce maka: Allah wadaran irin wannan tunani naka, kaiconka sakamakon karancin dirayarka da jahilcinka! Shi'a sun ruwaito maganar sumbuntar kai da fuska da kumatun sayyida Zahara (a.s) masu tsarki, da kuma sanya fuskarsa mai fuskantar tsakanin kirjinta, ka sani ire-irenka masu tunanin duniyanci da shedanci su ne suke kawo wani abu a irin wannan misali, ka sani sanya fuska alkibla ba ya nufin dora fuska, mu sanya ma haka ne to wannan yana komawa zuwa ga kallonka na shedanci ne da ba zai taba fahimtar motsi da ayyuka na ma'asumi ba.

Kai tir da tunanin da ya zo maka a kwakwalwarka, kaicon shedaninka da ya sawwala maka wani abu daban da abin da yake shi ne manufar hadisin!

Ina ganin idan akwai abin suka to yana koma wa zuwa ga kallonku ga Annabi (s.a.w) da yake dora matarsa a kafadu ko kumatu a kan kumatu a gaban mutane suna kallon rawar matan Afrika a masallacinsa. Wal'iyazu bil-Lah!

Sannan idan ka koma hukuncin shari'a Annabi (s.a.w) ma'asumi ne, kuma sumbuntar 'ya saboda kauna ga kowane mahaluki bai haramta ba, wannan jawabi a matakinka ke nan na marasa fahimtar matsayin imamanci da wilayar annabawa da wasiyyansu (a.s).

Da kake cewa: ((4) Matsayin Alkur'ani a Addinin Shi'a. To shi Alkur'ani sakon da Allah ya aiko Annabi Muhd (SAW) ne dashi izuwa dukkan alamina, mu Musulmi munyi imani dashi a matsayin tsiranmu na duniya da lahira, suma a addinin Shi'a nasu Allan ya aiko nasu Annabin da nasu Kur'anin, saurara kaji daga bakin mai ita. Kulaini Zindiki ya fada a littafinsa Usul Kafi mujalladi na daya shafi na 239 cewa "Akwai wani kwafi na Kur'ani da muke kiransa Mus'hafi Fadima misalinsa yakai ninki uku na Kur'anin "Musulmai" "maganar Kur'anin Shi'a daya sha ban_ban dana musulmi ta kai haddin tawa tiri cikin addinin Shi'a duba littafin Fuslul Kitab Fi Taharifi kitabu rabbil Arbabba na Nurul Dabarisi)).

Sai in ce maka: Ka ci amanar nakaltowa: Ruwaya ba ta ce Kur'ani ba, tana maganar "Mus'hafin Fadima" ne, wanda ba Kur'ani ba ne, kamar yadda tana maganar "ilmu makana wamayakun". Kur'ani wani abu ne wanda yake guda daya duk duniya gun Sunna da Shi'a gaba daya, kokarin da kake yi na cewa wasu suna da shi kuma ya saba da wanda yake hannun mutane kana musu ayar Allah ne da take nuna cewa ba za a iya yin waninsa ba!.

Sannan abin mamaki nisantar Ahlul Baiti (a.s) ya sanya ku ganin kowa ya cancanci ya kasance yana da littafi amma ban da su da ilimi yake gangarowa daga gidajensu. Wannan yana nuna mummunar niyya game da wannan gida mai daraja mai tsarki da kake da shi.

A yanzu kai kana da bakin magana! Amsa mana wadannan tambayoyin?

Ina ayoyin nan na "Asshaihu wasshaihatuأ¢â‚¬آ¦", idan surar Ahzaba ta fi bakara yawa ina sauran ta wanda ya fi kashi biyu cikin uku nata yawa? kamar yadda kuka ce daga Umar kuka karbo. Ina kuma sauran Kur'ani kamar yadda kuka karbo da Umar cewa miliyoyin haruffa ne wanda yanzu bai wuce dubu dari uku ba kamar yadda ya zo a Ausat na Dabarani. Ina kuma surar Hifdi wal Khul'i" da kuka ce Umar yana yin salla da su?!! A yanzu kai har kana da bakin magana ka soki wasu!



1 2 3 4 next