Tattaunawa Ta Takwas



Amma kagen da ka yi na takura wa 'yan Sunna a Iran wannan karya ce da ka sharara, kuma ka sani hisabinta yana kanka in ba ka nemi yafewar Allah ba. Domin Afganinstan da su mutanenku aka hada kai aka kashe ma’aikatan embassy na Iran da ma muminai da yawa amma suka yi hakuri, sannan sai Allah ya gwara kan mutanenku da iyayen gidansu wadanda suka rene su wato; Amerikawa, kamar yadda ya yi muku a can da kuma a Iraki. A baya sun sanya mutanenku yakar Shi’a, amma yanzu Allah ya gwara kansu. Kuma yanzu haka wadanda aka sanya su kare Isra’ila na mutanenku a Labanon, su ma muna nan zaka ga babu wani abu da Amurka da Isra’ilan zata tsinana musu tun daga mutanenku larabawa har na Afghan. Wadannan mutanen suka yi amfani da mutanenku wurin karkakatar da hadin kan musulmi, idan suka ga sun gama yi musu aiki sai kuma su rusa su da kansu.

Babban misali kana iya ganin shi ga wanda kuke gwarzantawa: bayan Regan ya ba shi Nobel na shaidar wanda ya fi kowa kawo zaman lafiya a duniya, amma bayan shugaba biyu kacal sai ga Bush ya sanya shi babban dan Ta’adda!.

A nan Iran da Shi'a da Sunna duk suna wuri daya kuma suna ibadojinsu suna kaunar juna in banda wadanda makiyan musulunci suka hure wa kunnuwa bayan sun fita daga kasar su ne suke dawowa da fitina. Amma Allah yana son masu gaskiya da neman hadin kai. Waye ya kirkiro neman hadin kan musulmi a cikin wadannan shekarun 30 kuma yake ta neman ganin ya samu hadin kansu, har ma yake cewa;  duk wanda yake tayar da fitinar Shi’a Sunna shi ba Shi’a ba ne, kuma ba Sunna ba ne. Sai imam Khomain!.

  Amma batun hadisin ridda da ya zo a cikin Buhari ina jiran ka kawo da wa ake, tun da ka ce ka san su, kamar yadda ka saba ayyawa Allah wadanda ake nufi. In ganin yana da kyau ka yi wa kanka adalci, ka kawo me ake nufi, bai kamata ka kasa kawo su wa ake nufi ba, kuma ka sani addini yakan zo da dokoki ne, idan wadannan dokoki wani ya siffanta da su sai su hau kansa.

Amma batun kafa hujjar wasici ka sani na kawo maka hujja can baya sai ka duba ka koma ka sanya hankali zaka ga dalili kar! Amma abubuwan da kake fada ina ganin ciwon da kake da shi shi ne ka dauka cewa abin da ka sani ka yi imani da shi haka nan yake wurin Allah, na sauran kuma bata ne. kai ke da matsala da ka ba wa ilmini Allah fassararka ka gaya masa wadanda yake nufi kuma kake so ya kasance yadda kake fassarawa. Don haka ne ba zaka iya fahimtar abin ta mahangar ilimi ba sai dai ta mahangarka.

Amma da kake cewa sharuddan umarni da kyakkyawa shi ne; dole ne duk sadda ka ga abin da ba daidai ba in har zaka iya kokarin gyara, to dole ne ka yi: Matsalarka shi ne ba ka san mafi yawan abin da yake munkarin ba, kuma ba ka san sharuddan yin sa ba. Don haka zaka yawaita yin kurakurai da su ma kuma munkari ne!. Saboda tayiwu kai kana ganin wani abu munkari alhalin ba munkarin ba ne!.

 

Ka sani umarni da kyakkyawa yana da sharudda idan sharudda suka fadi to ya saraya inda suka fadin. Ka duba yadda ka fada kana mai dogaro da hankali cewa shi ne dole ne duk sadda ka ga abin da ba daidai ba in har zaka iya kokarin gyara, to dole ne ka yi. Wannan ya sanya na gaya maka ba ka san sharuddan ba, don wannan ba sharadin ba ne!.

Amma maganar khairu ummatin da kake maimaitawa ka sani a littattafan da ka yi imani da su: Kun ce ku ne zaku zama shaida kan mutane ba ku yi zamani da su ba, sannan kana mamakin Annabi (s.a.w) zai yi shaida kan wasiyyansa bai yi zamani da su ba. Ka ga a nan ke nan har kun dara Annabi sanin halin mutane da abin da suka yi a duniya, wal'iyazu bil-Lah! Wannan a fahimtarka ma ken an ba ku yi adalci ga ilimin Annabi (s.a.w) ba.

Balle kuma lamarin ba yadda ka fahimta ba ne, Wannan ita ce matsalarka, koda yaushe kana fassara da yadda yake a kwakwalwarka ne. Wallahi khairu ummatin su ne Alayen Annabi (s.aw) kamar yadda ya gabata (a.s).

Ina ganin ya kamata ka dakatar da tattaunawa har sai ka yadda da cewa hujja tana iya hawa kanka ko kana so ko ba ka so matukar ta futo daga abin da ka yi imani da shi cewa ingantacce ne, in ba haka ba babu wani amfani ga tattaunawa.

Kada ka damu da wani kamar yadda wani bai damu da kai ba, ina ganin kowa ya yi nasa, idan wani abu ya hada mu kamar masallaci daya sai mu yi salla, kowa ya girmama abin da dayansa ya yi imani da shi ba tare da jahiltar juna ba.

Hafiz Muhammad

Kammala gyarawa

01 /July/ 2009

 



back 1 2 3