Tattaunawa Ta Takwas



Sau da yawa kana koma wa maganar mutlakat ne har yau, ina ganin kana bukatar sanin ilimin Usulul fikh kafin ka fahimci wasu bayanai, idan dai ba zaka iya ganewa ba to ka bar tattaunawa, kana magana ba ka san inda zaka sanya ta ba. Sau da yawa kana Magana kana bayar da fassara, ina ganin maganarmu ba kan Halifofi uku take ba, sai dai ban san me ya sanya ka nacewa kowane misali sai dai da halifofi uku. 

Sannan ka shahara da ayyana wa Allah wadanda yake nufi a cikin Littafinsa: Ina ganin zai zama shisshigi idan muka ayyana wadanda ake nufi ba tare da wani haske daga Littafin Allah ko hadisi sahihi ba. Manzon Allah (s.a.w) yana cewa da halifa na farko (kamar yadda ya zo a littafin muwatta'I Malik), bayan ya tambaye shi ya ki sheda masa da alheri a duniya ya tambayi Annabi (s.a.w) dalili. Annabi (s.a.w) ya amsa masa da cewa domin ban san abin da zaku yi bayana ba!

Sannan dogaronka da wannan domin kore ilimin Annabi (s.a.w) da gaibi ba a mahallinsa ba ne; kuma na ji dadi da na ga ka yi nuni da wannan ka'ida da na lurasshe ka "wa'inna au iyyakum la'ala hudan…" ina fatan ka lizimce ta, sai dai ba ka yi amfani da ita a mahallinta ba. Sannan bahasin ilimin gaibi yana da bukatar na sa zaman na musamman, don haka shigarsa yana bukatar bayanai masu yawa domin ka san mene ne muke cewa.

Sannan kana maimaita musun wilayar Imam Ali (a.s) alhalin ka kasa kawo mai musun wilayar Ali koda kuwa mutum daya ne, don haka wilayarsa hujja ce a kanka a gaban Allah a gobe kiyama. Amma amfani da mutlakat kana bukatar zama mai cikakken masaniya kan abin da nake cewa sannan sai ka yi ta kawo mutlakat. Sannan da’iman kana ayyana wa Allah madaukaki wadanda yake nufi a wadannan ayoyin ba tare da wani haske daga littafi mai daraja ba ko hadisi madaukaki.

Sannan musun da kake yi wa Umar saboda ya yi furuci da wilayar Imam Ali (a.s) wannan ya nuna cewa ka yarda da cewa kana bin inda ya yi maka dadi ne a addini, domin Umar ya fada ka karyata, amma inda ya yi maka dadi sai ka yarda, addini ba haka yake ba, addini hujja ce. Koda yake kana iya bin duk abin da ka so.

Sannan tawilin da kake yi na sanya Imam Ali (a.s) ya yi tarayya cikin wannan zaluncin saboda bai mayar mata da Fadak ba; Ba mu sani ba ko kalmar da kuke jingina wa Shi’a ta zagin sahabbai tana kanku ne. Domin wannan kiyasin da ka yi mu ba mu yarda da shi ba a cikin addini, hada da cewa mai kayan ta mutu, kuma da ya dawo da shi ga 'ya'yanta da gobe bayan mutuwarsa an kwace.

Musun kai kuka kabarin Annabi (s.a.w) da sauransu yana nunawa a fili cewa ka nisanta daga sanin addini domin addinin nan cike yake da misalan da wasu suka kai kuka ga wanin Allah. â€کYa’yan Annabi Ya’kub sun kai masa kuka, sannan Manzon Allah ya kai wa Sayyida Hadiza kuka, Da akwai misalai da ba zasu kirgu ba! Sannan wannan wani abu ne mai zaman kansa da yake bukatar lokaci na musamman.

Amma da ka yi da'awar cewa ana amfani da littafin makiyan Abubakar ne ina son ka kawo su waye makiyansa da muka yi amfani da littafinsu, Buhari ne ko Muslim in ya so sai mu san matsayinka a Sunnaci. Sannan kana magana da zafi ba tare da hujja ba,  wannan ba ya iya bayar da ma’ana, Amma ina ganin yana da kyau ka nisanci tattaunawa ta addini har sai ka san littattafan Ahlus Sunna tukun. Domin wannan maganar ta inganta gun mafi ingancin littattafan tarihinsu kamar yadda kake gani, kuma wallahi ba na tsammanin ka fi Ibn Kutaiba da Dabari son Abubakar, kai hatta da ni da ka yi wannan kagen na ina kin Abubakar ba na tsammanin zaka iya rantsuwa da Allah cewa ka fi ni sonsa.

Amma da kake mamakin sahabbai da sauran mutane suna gani aka ja Imam Ali (a.s) kuma aka doki 'yar manzon rahama (s.a.w) da sauran wulakanci da aka yi wa sayyida Zahara har kana mamakin hakan, kuma har kake kiran wannan da tatsuniya: Ina ganin ya kamata ka daina tattaunawa kan addini har sai ka san mas’alolinsa da kyau, domin wurare da yawa irin wadannan sun faru: kana ina Annabi ya bayar da umarni a hudaibiyya in banda shi da Ali babu wanda ya yi har sai da mutane suka ga kamar azaba ce zata sauko kuma ka duba rawar da wasu suka taka a gaban Annabi har ma da hana bin sa da gaya masa bakar magana, kai kun ruwaito cewa akwai wanda ya shake wuyan Annabi ya hana shi yin salla ga ibn Ubayyi. Kuma kai kana ina Annabi ya la’anci duk wanda ya tura karkashin Usama idan ba su tafi ba, amma suka yarda su dauki wannan la’anar. Kana ina manzon Allah ya nemi a ba shi abin da zai rubuta wasiyyarsa amma aka hana shi, kuma ya kori wadanda suka hana din kuma ba su sake haduwa da shi ba har ya rasu. Wannan fa duk a littattan da ka yi imani da su akwai shi, har kake mamakin don an yi wa aalayen Annabi wani abu a bayansa don wani bai taimaka musu ba. Gaya mini wanda ba kashe shi aka yi ba daga aalayen Muhammad (s.a.w).

Amma da kake nuna goyon bayanka ga wadanda suka ki biyayya ga gyaran da Imam Ali (a.s) ya so ya kawo bayan ya riki mulkin al'umma, ke nan kana nufin ka ce shi imam Ali wadannan mutanen sun fi shi ilimi ke nan, ko kuma kai ma ka yarda da ra’ayinsu na cewa sunnar Umar ta fi ta manzon Allah ke nan..



1 2 3 next