Muhammad dan Abdullahi



Hijirarsa :ya yi hijira daga Makka zuwa Madina a farkon watan rabiul auwal bayan shekara 13 daga aikensa, wannan ya faru ne sakamakon cutarwa daga kafirai gare shi da kuma ga sahabbansa.

Yakokinsa :Allah ya yi wa manzo izinin yakar mushirikai da kafirai da munafukai, sai ya yi dauki ba dadi da su a wurare da yawa da mafi girmansu sune :Badar- Uhud- Al-khandak(ahzab)- Khaibar- Hunaini.

Matansa:Khadija â€کyar khuwailid  ita ce matarsa ta farko, amma sauran sune :Saudatu â€کyar Zami’a da Aisha â€کyar Abubakar da Gaziyya â€کyar Dudan (Ummu sharik) da Hafsa yarUmar da Ramla â€کyar Abu sufyan (ummu habibia) da Ummu Salama â€کyar Abu Umayya da Zainab â€کyar Jahash da Zainab â€کyar Huzaima da Maimuna “yar Al-haris da Juwairiyya â€کyar Al-haris da Safiyya â€کyar Huyayyi dan Akhdabl.

â€کya’yansa :su ne 1- Abdullah 2-Al-kasim 3-Ibrahim     4-Fadima (AS) a wani kaulin da Zainab da Rukayya da Ummu Kulsum.

Ammominsa :su tara ne su ne â€کya’yanAbdulmudallib :Al-haris da Zubair da Abu Dalib da Hamza da Al-Gaidak da Dirar Al-mukawwam da Abulahab da Abbas.

Ammominsa mata :su shida ne daga iyaye mata daban daban su ne :Amima da Ummu hakima da Barra da Atika da Safiyya da Arwa.

Wasiyyansa goma sha biyu ne su ne:Amirulmuminina Ali  (AS)  da Al-hasan dan Ali  da Al-husaini dan Ali  da Aliyyu  dan Husaini  da Muhammad  dan Ali  da Ja’afar dan Muhammad  da Musa dan Ja’afar da Ali dan musa da Muhammad dan Ali da Ali dan Muhammad da alhasan dan Ali da Hujjat dan Al-hasan Al-mahadi (Allah  ya gaggauta bayyanarsa).

Mai tsaron kofarsa :Anas dan Malik

Mawakansa:Hassan  dansabita da Abdullahi dan Rawahata da ka’abu dan malik.

Mai kiran sallarsa:Bilal al-habashi da Dan ibn ummu maktum da sa’ad al-kirdi

Hatimin zobensa:(Muhammadur rasulullah).

Tsayin rayuwarsa :shekaru 63.

Tsayin lokacin annabtarsa :shekaru 23.

 

Tarihin wafatinsa:28 safar11 H.

Wajan da ya yi wafati:madina.

Inda aka binne shi:madina a masallaci madaukaki mai alfarma.

Domin karin bayani duba Biharul anwar juz’i na 15 da 16 na sayet dinmu.

 



back 1 2