Muhammad dan Abdullahi



Tarihin manzo Allah Muhammad danAbdullahi  (SAW)

Sunansa da nasabarsa :Muhammad dan Abdullahi dan Abdulmudallibi dan Hashimi dan Abdu manafi dan kusayyi dan kilabi, nasabarsa madaukakiya tana tukewa zuwa ga annabi Ibrahim (AS).

Mahaifiyarsa :ita ce Aminatu â€کyar wahabi dan Abdu Manafi dan Zuhrata dan kilabi.

Alkunyarsa :Abul kasim, Abu ibrahim.

Lakabinsa :Almusdafa , yana da sunaye da suka zo a cikin  alkur’ani mai girma kamar:khataman nabiyyin, Al’ummi , Almuzammil , Almudassir , Annazir , Almubin , Alkarim , Annur , Anni’ima , Arrahma , Al’bdu , Arrauf , Arrahim , Asshahid , Almubasshir ,Annazir , Add’ai da sauransu.

Tarihin haihuwarsa:17 Rabiul auwal shekarar giwa(571m)bisa mashhurin zance gun shi’a, an ce 12 ga watan da aka ambata.

Wurin haihuwarsa:Makka.

Aikoshi :an aiko shi a Makka 27 rajab yana dan shekara arbain.

Koyarwarsa :ya zo da daidaito tsakanin dukkan hAlitta da â€کyanuwantaka da rangwame na gaba daya ga wanda ya shiga musulunci, sannan ya kafa shari’a madaukakiya da dokoki na adalci da ya karbo daga wajan Allah su kuma musulmi suka karba daga gare shi.

Mu’ujizozinsa :mu’ujizarsa madauwamiya ita ce alkur’ani amma wadanda suka faru a farkon musulunci suna da yawa ba sa kuma kirguwa.

Kiransa :ya kira mutane zuwa ga tauhidi a makka a boye shekara uku ya kuma kira su a bayyane shekara goma.



1 2 next